Friday, 15 February 2019
Yanzu-yanzu: Da yiwuwan a daga zaben gobe, INEC ta shiga ganawar gaggawa da masu ruwa da tsaki
Hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC tana cikin ganawar gaggawa da jami'an tsaro, masu lura da zabe da wasu masu ruwa da tsaki kan zaben da za'a gudanar. Game da wata majiya daga cikin ganawar, da yiwuwan abubuwa su canza bayan ganawar.
Ko sama ko kasa: An nemi kuri'un kananan hukumomi 2 an rasa a Neja
A yau, Juma'a ne Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta INEC a jihar Neja ta ce akwai
yiwuwar ba za a gudanar da zabukkan sanata a mazabun Neja ta Arewa da Neja ta Kudu ba a ranar Asabar saboda kuri'un zabe da aka tanadar domin mazabun sun bace. Bataren zabe na jihar, Farfesa Samuel Egwu ne ya bayyana hakan yayin da ya ke jawabi ga manema labarai a garin Minna.
Ko sama ko kasa: An nemi kuri'un kananan hukumomi 2 an rasa a Neja
A yau, Juma'a ne Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta INEC a jihar Neja ta ce akwai
yiwuwar ba za a gudanar da zabukkan sanata a mazabun Neja ta Arewa da Neja ta Kudu ba a ranar Asabar saboda kuri'un zabe da aka tanadar domin mazabun sun bace. Bataren zabe na jihar, Farfesa Samuel Egwu ne ya bayyana hakan yayin da ya ke jawabi ga manema labarai a garin Minna.
Thursday, 14 February 2019
Malamai In da zasu tsine min sau 10000, sai Allah ya karamin daukaka – Kwankwaso
Tsohon gwamnan jihar Kano, Engr Rabi’u Musa Kwankwaso, yayi karin haske akan maganarshi da yayi akan malamai da yace yakamata su dena amfani da mambarinsu domin zagi ko kushe su.
A ziyarar da wasu malamai suka kai masa a ranar Alhamis, Kwankwason yace kowa yayi zagi a kasuwa yasan da wanda yake, yace su malaman da yake magana akansu suma sunsan dasu yake.
Kwankwaso yace “Irin wadannan malamai ko zasu tsine min sau dubu sai Allah ya kara daukaka ni. Daya daga cikin abinda ya kawo wannnan muhawara shine rashin fadar sunaye ne, in anyi maganar masu shiga iri kaza, na ware da sauran banda ban fada ba. Kowa yasan a garin nan idan mukayi zagi a kasuwa munsan da wadanda muke.” a cewar Kwankwaso
A kwanakin nan dai Sanatan yayi maganar da ta ja hankalin mutanen jihar Kano dama kasa baki daya akan shigar malamai siyasa suna sukarsu. Lamarin da yaja malamai da yawa yi masa raddi na cewa ya taba sunnar Annabi (S.A.W) Saidai wasu na ganin malaman suna sukar Kwankwason ne saboda bambantar ra’ayi, saboda wasu na cewa kar a zabi duka yan takarkarun da yake goyon baya.
Muna nan daram a kan niyyar mu ta bawa Buhari kuri’u miliyan 19 – ‘One 2 Tell 10
Shugaban kungiyar “One 2 To 10” mai yiwa shugaba Buhari yakin neman zabe reshen jihar Katsina, Dakta Mannir El-Yakubu, y ace babu gudu, babu ja-da-baya a kan kudirin kungiyar na samar wa da shugaba Buhari kuri’u miliyan 19 a zaben shugaban
kasa na ranar Asabar. Da yake Magana a wurin taron yakin neman zaben shugaba Buhari a jihar Katsina, El-Yakubu, y ace kungiyar su za ta tabbatar da cewar shugaba Buhari ya samu kuri’a miliyan daya daga kowacce jiha daga jihohi 19 da ke fadin arewacin Najeriya.
Ya kara da cewa dandazon jama’ar da su ka halarci taron kamfen din Buhari a jihar Katsina shaida ce da ke nuna cewar mutanen jihar na tare dan su tare da bayyana cewar shugaban kasa
Buhari na da daraja a duk in da ya shiga a duniya. Kazalika, ya bayyana cewar shugaban kungiyar sun a kasa, Dakta Baffa Bichi, bait aba nuna gajiya wa ba a rangadin da kungiyar ta yi na dukkan mazabun da ke jihohin arewa 19 domin nema wa Buhari jama’a.
An kama samfurin takardun zabe buhu 7 a Jigawa
Rahotanni daga jihar Kano dake a shiyyar Arewa maso yammacin Najeriya na nuni ne da cewa jami'an 'yan sanda sun kama wasu takardun kada kuri'a na gwaji da ke kama da ta gaskiya ta hukumar INEC da aka nufi yin amfani da su a jihar Jigawa.
Labarin batun dai yana cigaba da janyo takaddama tsakanin mabiyan jam'iyyun PDP da na APC kan abinda ake shirin yi da takardun tun bayan da ya fallasa a kafafen sadarwar zamani.
Hotunan kafin aure na Rahama Sadau da Sadiq Sani Sadiq sun tayar da kura
Fitattun jaruman finafinan Hausa wato Sadik Sani Sadik da Rahma Sadau da alamun bayyanar soyayya a tartare da su biyo bayan hotunansu dake nuna alamun akwai soyayya mai tsananin karfi a tsakaninsu
. Jarumi Sadik Sani ya baiyana cewa soyayya tana da dadi koda a ce kana da mata za ka iya karawa. Da alamu akwai yiyuwar aure a tsakanin jaruman
yan sanda sun kama Buhuna 17 makare da kuri'u da aka dangwalewa APC a
An kama Buhuna 17 makare da kuri'u da aka dangwalewa APC a
Kano Jami'an 'yan sanda sun kama buhuna 17 cike da takardun zabe da aka dan gwale a jihar Kano,
rahotanni sun bayyana cewa an tafi da buhunan ofishin 'yansandan jihar dan gudanar da cikakken bincike. Jaridar Daily Nigerian ta bayyana cewa wata majiya daga jami'an tsaron ta tabbatar mata cewa jam'iyyar APC ce aka dangwalewa kuri'un.
Buhari da Atiku sun bayyana jihohin da za su rufe taron su na yakin zabe a yau Alhamis
Mu-hadu-a-2023: Buhari ne zai lashe zaben 2019 da gagarumin rinjaye - Hon Abdulmumini Jibrin
Damajalisar tarayyar nan mai wakiltar mazabar kananan hukumomin Bebeji da Kiru daga Kano da yanzu haka yake a matsayin korarre daga majalisar Alhaji Abdulmumin Jibrin ya bayyana cewa yanzu kam ta tabbata shugaba Buhari zai lashe zaben 2019 da gagarumin rinjaye. Dan majalisar da ya bayyana hakan a shafin sa na sada zumuntar Tuwita ya Kuma bayyana nasarorin da shugaban Kasar ya samu tare kuma da jam'iyyar adawa marar karfi a matsayin wasu dalilan da za su sa shugaban ya sake Lashe zaben cikin ruwan sanyi |
Yariman Saudiyya Mai Jiran Gado ya hau rufin dakin Ka'aba (karanta)
Yariman Saudiyya Mai Jiran Gado ya hau rufin dakin Ka'aba
Yariman Saudiyya Mai Jiran Gado Muhammad bin Salman ya hau doron dakin Ka'aba a lokacin da ya ziyarci garin Makka Mai Girma. Rahotanni sun ce, Yariman ya ziyarci garin na Makka domin duba sabbin aiyukan da ake gudanarwa a Dakin Allah Mai Tsarki. Yariman da ya halarci wanke Dakin Ka'aba da aka saba yi tare da jami'an tsaro 600 dake kare shi ya fara sumbatar Hajarul Aswad inda daga nan kuma ya hau matattakalar tare da shiga cikin dakin Ka'aba.
Yarima bin Salman ya yi Sallah a cikin Ka'aba inda ya dauki wani tsumma tare da yin goge- goge, sannan kuma sai ya hau saman rufin Dakin Mai Tsarki wanda abu ne da ba a saba gani ba. Hawan Yariman saman Dakin Ka'aba ya janyo ka ce na ce a shafukan sada zumunta na yanar gizo. An samu tarihin cewar daga cikin Halifofin Daular Abbasiyya Abu Ja'afar Al-Mansur ya taba hawa rufin Dakin. A yanzu dai ma'aikata na hawa saman Dakin don tsaftace shi a lokacin da aka yi ruwan sama ko kuma za a sauya rigarsa. TRThausa.
Shin ko Rahama Sadau da Sadiq Sani Sadiq zasu yi aurene? Kalli hotunan dake nuna hakan
Wadannan hotunan taurarin fina-finan Hausane, Rahama Sadau da abokin aikinta, Sadik Sani Sadik da ke nuna alamar soyayya a tsakaninsu, wasu daga cikin abokan aikinsu sun saka wadannan hotunan a shafukansu na sada
zumunta inda suke musu fatan samun rayuwar aure me kyau. A farkon makonnanne Sadik ya saki wani sako ta shafinshi na Twitter dake cewa so ne kesa mutum ya kara aure koda kuwa yana zaune da iyalinshi lafiya, sakon ya dauki hankulan mutane
sosai. Saidai duk da haka ba za'a cire tsammanin cewa wadannan hotunan na yin wani sabon fim ne ba da ake son fara salonshi da haka dan ya samu karbuwa gurin jama'a ba kamar yanda a kwanakin baya ya faru tsakanin Maryam Booth da Sadik Zazzabi. Koma dai menene lokaci be bariba.
zabe:: Kalli wani mutum da ya koma da kwana rumfar zabe dan ya zama na farko da zai sakawa Buhari kuri'a
Ya Tare A Rumfar Zabe Tun Kwana Uku Kafin
Zabe Domin Ya Zama Mutum Na Farko Da Ya Jefawa Buhari Kuri'a Abubakar Shatima, wani masoyin Buhari kenan wanda ya yi hijira daga garinsa na Jos izuwa wurin Zaɓe , tun a jiya 13/02/2019. domin zama farkon wanda ya zaɓi Buhari. Rariya.
Kalli abinda ya faru yayinda hadimin shugaba Buhari ya hadu da 'ya'yan Atiku
Kalli abinda ya faru yayinda hadimin shugaba Buhari ya hadu da 'ya'yan Atiku
Hadimin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad kenan a wadannan hotunan da yake tare da 'ya'yan dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Aliyu da Mustafa Atiku Abubakar.
Bashir ya bayyana cewa sun hadune a kan hanyarsu ta zuwa wajan yakin neman zabe yayin da Atiku yayi Adamawa su kuma sun yi Katsina. Sun dauki hoto tare wanda kowannensu yayi inkiyar gwaninshi.
Wednesday, 13 February 2019
Fitaccen jarumin fina-finan Hausa ya gargadi ‘yan Najeriya A kan zabe
Fitaccen jarumin masana’antr shirya fina- finan Hausa (Kannywood), Abba El- Mustapha, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su san cewar akwai rayuwa bayan zabe, don haka kar su bari siyasa ta raba kan su. El-Mustapha, wanda aka fi sani da
Abba Ruda’ ya yi wannan jan hankali ne a wani rubutaccen sako da ya fitar a shafin sa na sada zumunta (Instagram) yayin hutun krshen mako. Kada ka bari siyasa ta had aka rigima da kowa. Ka yi siyasa cikin mutunci da girmama wa don akwai rayuwa bayan zabe,” a cewar jarumin. Jarumin ya kara yin kira ga ‘yan Najeriya a kan su daina dage wa a kan Lallai sai an bi ra’ayin sun a siyasa.domin kowa da nasa ra’ayin
Ina ma! ina ma! ina ma da Kwankwaso zan gwabza a takarar Sanata - Shekarau
Tsohon gwamnan jahar Kano, kuma dan Takarar Sanatan mazaban Kano ta tsakiya a karkashin inuwar jam’iyyar APC, Malam Ibrahim Shekarau ya bayyana cewa ko kadan baya shakkar fuskantar dan takarar Kwankwaso, Sani Aliyu Madakin Gini a takarar da suke yi. Shekarau ya bayyana haka ne a ranar laraba, 13 ga watan Feburairu yayin da yake zantawa da manema labaru a garin Kano game da zaben dake karatowa, inda yace jama’a ne zasu tabbatar da mai nasara a tsakaninsa da dan takarar Kwankwaso, Madakin Ginii
Mun Dade Muna Zagin Malamai (karanta) sheikh dahiru bauci
A lokacin da Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya yi kira ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ya bude Boda saboda Talakawa suna shan wahala ya zagu iya zaguwa. A lokacin da Dakta Ahmad Ibrahim BUK yayi magana akan a sassautawa
Talakawa haka shima a wannan dandali aka rika zaginsa A lokacin da Dakta Ahmad Gumi ya ce baya Buhari haka zagin safe daban da na rana Lokacin da Sheikh Bala Lau ya nemi yan kungiyar Izala su zabi Buhari ya samu nasa kason zagin A dalilin bambancin akida ko fahimta mu kan takarkare mu zagi Malamin da ba tafiyar mu daya ba, wani lokacin har da kafirta juna. A wannan dandali na ga wadanda suka rika zagin Marigayi Sheikh Ja’afar Mahmoud Adam da Albanin Zariya
(Allah Ya Jikansu). Har hoton wani ya rungumi wata ake cire kan a sa na Ja’afar a la’ance shi Malam Lawan na Masallacin Triumph ba irin zagin da bai sha ba saboda yana Kawo gyara a mulkin Buhari. Takanas wani da ke ikirarin babban masoyin Buhari ne zai shiga gidan rediyon jihar ya keta masa rigar mutunci. A lokacin da aka hana yin Gandun Shirya Fina-finan Hausa (Film Village) a jihar Kano Malamai sun zagu la’ada waje.
Malami a ko ina yake matukar yana kira abi Allah da ManzonSa abin girmamawa ne. Yana raye ko ya mutu Ba irin barazanar da ba su gani a rayuwa ba, a zage su a ci zarafin su har kashe Malamai an yi. Mutane da dama na cewa siyasa daban addini ma daban kuma bai kamata malamai da Sarakuna su shiga siyasa ba. Wannan ya sa muke ganin duk wani Malami da bai ce a zabi namu ba muna da ‘yancin mu zage shi mu ci zarafinsa. Amma abin tambaya shine
akwai wani abu a rayuwar mu da Allah Ya kebance shi Ya ce kada a fadawa Musulmi gaskiya a kansa? Shin ita Siyasa ba Allah a cikinta? Idan ba Allah a ciki me ya sa Musulmi zai yi ta? ‘Yan siyasa na amfani da Malamai domin biyan bukatunsu, amma ba domin son Allah da kishin addini ba. Idan Bala’I ya zo su nemi Malamai a yi addu’a idan suna son cin zabe su nemi
Malamai a yi addu’a. Mu kuma magoya baya a bar mu da zagin Malamai don kare ‘yan siyasa. Amma Ni Maje El-Hajeej Hotoro Malami mai tsoron Allah da yake kan tafarkin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam ya fi duk wani Dan siyasa daga Kansila zuwa Shugaban Kasa. Malamai ba Allah ba ne ba kuma Mala’ikun Allah ba ne sannan ba Wahayi ake yi musu ba. Suna iya yin daidai suna iya yin kuskure, kamar yadda akwai masu fakewa da addini a cikinsu suna yaudarar Al’umma. Amma Malaman kwarai suna da daraja da mutunci da kima fiye da kowa saboda su Magadan Annabawa ne kuma zaginsu da cin zarafin su Halaka ne.
Kun san yatsan da za a dangwala kuri'a da shi?
Batun yatsan da mutane ya kamata su yi amfanida shi domin dangwala kuri'arsu a lokacin zabe na neman ya kawo rudani a Najeriya. Wani sako da aka yi ta yadawa a shafukan sadazumunta musamman WhatsApp ya bayyana cewa
hukumar zabe ta canza tsarin yadda mutane za su jefa kuri'a. Cikin bayanin da ake yada wa har da yatsan da hukumar ta ce za a yi amfani da shi. Amma Hukumar INEC ta karyata labarin inda ta
ce masu zabe za su iya amfani da kowane yatsa yayin dangwala kuri'arsu. A wani bayani da ta wallafa a shafinta na Twitter, hukumar zabe ta bayyana cewa masu zabe za su iya amfani da kowane irin yatsa su dangwala kuri'arsu Mai kada kuri'a zai iya amfani da kowanne yatsa domin kada kuri'arsa. Amma ya tabbatar da cewa tawadarsa tana cikin zagayen akwatin jam'iyyar da ya dangwala wa, kada ta shiga cikin akwatin wata jam'iyyar daban," in ji INEC.
Saboda haka wannan labarin kanzon-kurege ne da wasu 'yan ta-da-zaune-tsaye suke yadawa Sakon karya da ake yada wa Sakon ya kunshi cewa "a yanzu ba za ka dangwala kuri'a da babban yatsa ba sai dai da dan ali wato manuniya. Duk kuri'ar da aka kada da babbar yatsa za a soke ta. Tambayar a nan ita ce, me ya sa ba a wayar da kan 'yan kasa ba har sai yanzu? "Me yasa INEC ta boye irin wadannan bayanai masu amfani har sai kwana kadan kafin zabe?"Don Allah ba wai karantawa kawai za ku yi ba ku tura wa sabbin masu kada kuri'a don su fadaka. "makomar kasarmu ta dogara ne a kan yatsan dan ali wato ('yar manuniya)", in ji sakon. Sai dai babu wata hujja da ke tabbatar da sahihancin sakon, domin kuwa hukumar zabe ta yi bayani akasin hakan.
Kudin gyaran Wuta dala biliyan 16: Obasanjo ya mayarwa da Buhari martani
Kudin gyaran Wuta dala biliyan 16: Obasanjo ya mayarwa da
Buhari martani: Na riga na wanke kaina a cikin littafin dana rubuta idan baka iya karantawa kasa a karanta maka a kuma fassara maka a yaren da zaka fahimta
Bayan da rahotanni suka bayyana cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya sha alwashin bincikar kudin da aka kashe akan gyaran wutar lantarki da suka kai dala biliyan 16
lokacin mulkin tsohon shugaban kasa, Obasanjo daga 1999 zuwa 2007, Obasanjon ya mayar wa da Buhari martani inda yace yayi mamakin fitowar wannan kalami daga bakin Buharin A sanarwar da ya fitar ta hannun me bashi shawara kan kafofin watsa labarai, Kehinde Akinyemi, Obasanjo yace yaji abinda Buharin yace amma bai yi tunanin shugaba me cikakkiyar fahimtar abubuwa ba zai iya yin wannan magana.
Yace rahoton majalisar tarayya a wancan lokacin da binciken da hukumar EFCC tayi da kuma kwamitin wucin gadi da aka kafa wanda Aminu Waziri Tambuwal ya jagoranta, kan binciken yanda aka kashe kudi wajan gyaran wutar lantarki a zamaninshi sun wankeshi daga dikkan wani zargi.
Obsanjon ya kara da cewa ya kuma yi bayani dalla-dalla akan badakalar gyaran wutar lantarkin ta zamanin mulkinshi a cikin littafin da ya rubuta na My Watch, dan haka ya bukaci Buharin da 'yan koranshi da suje su karanta Fannoni 41, 42, 43 da 47 na littafin nashi..Ya kara da cewa, idan kuma Buharin bazai iya karantawa ba to yasa masu taimakamishi su karanta mai su kuma fassaramai a yaren da yafi fahimta. Ya kara da cewa, mutane su fahimci cewa dala biliyan 16 da ake maganar kashewa a zamanin mulkinshi ba fa shine da kanshi yace ya kasheta ba, a'a zargi ne aka yi kuma tuni ya wanke kanshi, kamar yanda The Nation ta ruwaito.
Tuesday, 12 February 2019
Champions League: 'Yan wasan Madrid da za su je Ajax
Real Madrid za ta ziyarci Ajax a wasan farkozagaye na biyu a gasar cin kofin Zakarun Turai ta Champions League da za su kara a ranar Laraba.
A Champions League takwas da suka buga, Real ta yi nasara a karawa shida, Ajax ta ci wasa biyu. Sun kuma buga European Cup hudu, inda Ajax ta ci wasa biyu, Real ta yi nasara a daya da kunnen doki a fafatawa daya.
Real Madrid tana da kofin Zakarun Turai na
Champions League guda 13, ita kuwa Ajax tana da shi hudu. Yan wasan Real Madrid:
Masu tsaron raga: Navas da Courtois da kuma Altube.
Masu tsaron baya: Carvajal da Vallejo da Ramos da Varane da Nacho da Marcelo da
Odriozola da kuma Reguilón. Masu buga tsakiya: Kroos da Modric da
Casemiro da Valverde da Asensio da Brahim da kuma Ceballos.
Masu cin kwallo: Mariano da Benzema da Bale da Lucas Vázquez da kuma Vinicius Jr.
Aisha Buhari tayi karin haske game da wasu halayya da dabi'un Mijin ta
Uwar gidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha, a yau Talata tayi karin haske dangane wasu dabi'un Mai gidan ta sabanin yadda wasu ke jingina ma sa dabi'u na tsanani da rashin jin kai ko
kuma hali na ko in kula. A yayin da ake daf da gudanar da babban zaben kujerar shugaban kasa, Aisha a yau Talata ta ce mai gidan ta da ya kasance shugaban kasar Najeriya mutum ne mai tsananin tausayi gami jin kai da nuna ga ƙauna ga al'umma. Aisha wadda ta jagoranci tawagar Mata da Matasa na kungiyar yakin neman zaben Buhari, ta bayyana hakan ne a hedikwatar cibiyar ma'aikatan sufurin ta NURTW da ke babban birnin kasar nan na tarayya.
Gwamnati ta bankado sabuwar hanyar da Atiku ya shirya yiwa zaben Najeriya kafar-angulu
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce jam'iyyar adawa ta PDP tare da dan takarar ta na shugaban kasa da sauran jiga-jigan ta sun dauri aniyar haifar da rikici da tarzoma da za ta kawo yamutsi har ta kai ga lalata zabukan gama gari da ake shirin yi.
Ministan yada labarai na gwamnatin tarayyar, Mista Lai Mohammed ne dai ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da ya gudanar a ofishin sa dake a garin Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya.
NAJERIYA Dawo Da PDP Karagar Mulkin Najeriya Kuskure Ne - Ribadu
Tsohon shugabanhukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC a Najeriya, Malam Nuhu Ribadu, ya nuna fargabar cewa dawowar jam’iyyar adawa ta PDP karagar mulki zai iya maido da hannun agogo baya ga abin da ya ce gagarumar nasarar da aka samu a fannin yaki da
cin hanci. Ribadu wanda shi ne babban jami’in tuntunba na kamfen din ta-zarcen shugaba Muhammadu Buhari, ya ce aikin yaki da cin hanci da gwamnatin APC ta yi, ya fi duk abin da PDP ta gudanar a tsawon shekaru 16 da ta yi
tana mulki. "Ka ga mutum shi kadai, duk duniya yana da gida a ko ina, kana da shi a ingila kana da shi a America, kana da shi a Dubai. Mutumin da ya yi shekara uku ya zo ya kawo canji a rayuwarmu, za ka ce in cire shi, in dawo da wanda ya yi min lalaci, duk irin nadamar da ya yi, ai ni ba wawa ba ne." inji Ribadu.
Kalaman nasa na zuwa ne kwanakin kadan kafin 'yan Najeriya su yi zaben shugaban kasa Sai dai babbar jam'iyyar adawa ta PDP, ta ce, kushe ta da APC ke yi, alamu ne Na rashin adalci da kuma rashin hujjar rashin cika alkawuran kamfen da hakan ya jefa ‘yan Najeriya cikin kunci.
"A kasar nan, babu tsaro, babu abinci, babu ayyuka, tattalin arzikin kasa ya lalace, matasa sai shaye-shaye, kai har harkokinmu da kasashen waje ya tabu To idan aka ce wannan gwamnati ta komo ta sake shekara hudu, sai mu ce Najeriya Allah ya sawwake in akwai ta." Inji Sakataren PDP na kasa, Sanata Umar Tsauri. Tuni dai hukumar zabe ta fara tura kayayyakin zabe da hakan ke nuna ba damuwar dage zaben kamar yadda aka gani a 2015.
SIYASA:: Masoyin Atiku ya fara tafiya akan jaki daga Adamawa zuwa Abuja dan nuna mishi soyayya
Wannan hoton wani bawan Allahne masoyin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar da ya fara tafiya akan Jaki daga Adamawa zuwa babban birnin tarayya, Abuja dan nuna soyayya ga Atikun
HOTUNA;; Kalli Zahara da Yusuf Buhari nawa mahaifinsu shugaba Buhari yakin neman zabe
Wadannan hotunan 'ya'yan shugaban kasa, Muhammadu Buhari ne, Zahara da Yusuf a yayin da suke wa mahaifinsu yakin neman zabe.
SIYASA:: Maganar Buhari a Zamfara da ta jawo cece-kuce
Darektan yada labarai na Kwamitin Kamfen din shugaban kasa Muhammadu Buhari Festus Keyamo ya bayyana cewa ba daidai bane yadda ake ta yada wa wai ya yi kira ga mutanen Zamfara da su kwana da shirin ko ta kwana.
A ziyarar Kamfen da ya kai garin Gusau, Buhari ya ce ‘Ina son kowa ya cika cikin sa in ma fitinan ne aje ayi Hakan bai yi wa mutane da dama dadi ba musamman ‘yan adawa inda suka rika cewa wannan magana bai dace ya fito daga bakin shugaban kasa ba.
Keyamo ya ce duka wanda ya san Buhari ya san mutum ne mai yawan barkwanci saboda haka ko a wancan lokacin da yake wannan bayani ya hada ne za zolaya ba wai da gaske yake yi ba. ” Abinda Buhari yake nufi shine ‘Irin yadda aka samu yalwa a noman shinkafa, mutane su
tabbata sun dame cikin tam da tuwo saboda gujewa rudin shaidan kada su kai ga fadawa cikin fitintinun da babu gaira-babu dalili. Kuma ma dai Buhari ba’a ya ke yi. Muna kira ga dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar da ya daina ruruta abin. Ya sani cewa Allah ke ba da mulki. Ya dai na ruruta abin kamar sama da kasa zasu hade. Ya sani cewa Najeriya ba ta siyarwa bace
KANNYWOOD:: Tarihin fati washa
Tarihin fati washa
Jarumar tayi fice a masana'antar wasan kwaikwayo na Kannywood kuma kai ga yanzu tauraron ta na cigaba da haskawa.
Fatima Abdullahi Washa kamar yadda asalin sunan ta yake ba bakuwa bace a
harkar fim din Hausa don kuwa ta fito a fina-finai da dama inda tayi fice Duniya ta
san ta
Jarumar tana daya daga cikin manayna jarumai mata da tauraron su ke haskawa a
farfajiyar Kannywood.
An haife ta ranar 21 na watan Febreru na shekarar 1993.
Kwarerwar da kuma himma da take badawa a wajen aikin yasa tayi fice cikin yan
matan Kannywood.
Wasu daga cikin tsoffin fina-finanta akwai Sarki, 'Yar Tasha, Ana Wata ga Wata,
Mijin Biza, Hindu, Dangin miji, Matar Wani da, Gwaska returns sauransu.
Fatima ba ruwanta da fada da kowa domin tunda take ba'a taba jinta da wani ko
wata ba suna rigima ko kuma jan fada.
Kyakkyawar jaruma har yanzu bata yi aure ba amma akwai jita-jita da yadu
shekarun baya cewa wasu daga cikin masana'antar Kannywood na neman ta da
aure.
Daya daga cikin Nuhu Abdullahi ya bayyana cewa hakika yana son ta kuma zai so
ta zama matar sa sai dai bai shirya yin aure ba.
Yace jarumar tana nuna masa biyayya kuma ta taimaka mashi sosai don haka
yake matukar girmama ta.
Akwai jita-jita da take yawo akan Jarumar tana soyayya da jarumi Adam A Zango ,
duk dai basu fito fili sun tabbatar ko karyata hakan ba, Amma kowa ya yadda fati
washa tafi kowace jaruma kusa da Adam A Zango domin tun daga fim din 'Sarki'
har yanzu suna tare.
Tana kuma cikin fitattun jarumai dake da dinbim masoya masu binta a dandalin
sadarwar zamani.
Tana da mabiya dubu shida da casa'in da daya a shafin ta na Instagram kana
mabiyanta dubu saba'in da daya ne a Tuwita. Jarumar ta samu lamban yabon da dama cikin gida har da wajen gida. Cikin jerin kyautar girmamawa da ta karba akwai City people awards
ABUBUWAN DA YAKAMATA A SANI DANGANE DA TSOHUWAR JARUMA KANNYWOOD MARIGANYIYA HAUWA MAINA
KANNYWOOD NEWS
ABUBUWAN DA YAKAMATA A SANI DANGANE DA TSOHUWAR JARUMA KANNYWOOD MARIGANYIYA HAUWA MAINA
Takaitaccen tarihin jaruma wanda ta taka rawar gani wajen raya masana'antar nishadi ta arewacin Nijeriya Jarumar ta rasu daren ranar laraba 2 ga watan Mayu , a asibitin Malam Aminu kano inda take jinya bayan wata rashin lafiya da tayi. Ga takaitaccen tarihin rayuwar ta Haifafiyar yar garin Biu na jihar borno, an haife Hauwa Maina a cikin shekarar 1970.
Tana fara haskawa a cikin shirin fim a shekarar 1999. Fim na farko da ta fara fitowa a ciki shine tuba wanda tsohon ma'aikacin NTA, Musa Yahaya Ya bada umarni. Kamar yadda ta shaida, a farko dai iyayen ta sun nuna rashin jituwa da sana'ar da ta zaba sai dai daga baya sun amince ta cigaba da harkar fim
ganin irin fa'idar da yin haka yake da ita ga cigaban al'umma. Banda fitowa a fim, Hauwa Maina tana bada umarni tare da shirya fim, tayi karatu kan wannan ilimin a kasar Amurka. Ta dauki nauyin shirya wasu fina-finai karkashen kamfanin ta mai suna Ma'inta Enterprise Limited. A tsawon shekara 20 da tayi a masana'antar fim, marigayya ta haska a fina-finai fiye da 50 masu kayatarwa. mafi birgewa cikin fina - finai da ta taka rawar gani akwai fina-finan tarihi kamar, 'bayajidda' da 'Queen Amina'. Banda fina-finan hausa ta Kannywood, jarumar ta
haska a cikin fina-finan nollywood da dama. A wata hira da tayi, ta sanar cewa bata karban aikin fitowa a fim matukar bata gamsu da labarin shirin musamman idan bata da ma'ana ko bata ilmantarwa Allah ya albarkace ta yara biyu Maryam da Abdulrahman. Diyar ta Maryam wanda ta shahara a fagen wake kuma daya daga cikin matasa dake jajircewa wajen daukaka addinin musulunci.
Kamar yadda hauwa maina ta shaida, akwai kyakyawar dangantaka tsakanin ta da diyar ta Domin mafi yawancin lokaci bata yin wata aiki ba Tare da ta nemi shawarar ta ba. Hakika wannan dangantakar tasu yayi kaurin suna Kana hakan ya bayana ga bainar jama'a yayin
daurin auren diyar. Jarumar tayi sharara hawayen ga bikin ganin cewa zata rabu da aminiyar ta. Ta kasance tamkar uwa ga sauran jaruman Kannywood. Mafi yawancin abokan sana'ar ta ta kannywood na girmama ta. Ta kasance tamkar uwa ga sauran Jarumai. Rasuwar ta ya girgiza mutane da dama na Kannywood tare da dinbim masoya da masu
bibiyan fina-finan hausa. Jarumai da dama sun yi jimamin rasuwar ta inda suka wallafa hotunan ta a shafukar su na kafafen sada zumunta tare da yi mata fatan Allah ya jikan Ta da rahama. Hakika Kannywood tayi babbar rashi kuma samun wacce zata maye gurbin ta zaiyi wuya. Muna fatan Allah ya jikan ta da rahama, ya kuma gafarta mata.
LABARAI:: Najeriya ta soki Amurka kan yi mata kutse cikin harkokin gida
Najeriya ta soki Amurka kan yi mata kutse cikin harkokin gida Jam’iyyar APC dake mulkin Najeriya ta bayyana damuwar ta da abinda ta kira katsalandan daga Amurka da wasu kasashen duniya kan shirin zaben kasar da za’a gudanar a karshen wannan mako. Sanarwar da Daraktan yada labaran Jam’iyyar Festus Keyamo ya rabawa manema labarai ta bayyana damuwa kan sukar da kasashen ke yiwa shirin zaben da kuma dakatar da babba mai shari’a Walter Onnoghen daga kujerar sa.
WASANNI:: Rashin Neymar zai shafi wasan PSG da United - Buffon
Mai tsaron ragar Paris Saint Germain Gianluigi Buffon ya bayyana fargaba kan yadda sakamakon wasan gasar zakarun Turai da za su fafata Yau Talata tsakaninsu da Manchester United.
Buffon ya ce fargabar ta zama dole, ganin yadda kungiyar ta PSG za ta buga wasan ba tare da gwarzon dan wasanta ba wato Neymar. Neymar ba zai samu bugawa PSG was aba har sai cikin watan Afrilu, saboda raunin da ya samu a kafafunsa, yayin wasansu da Starsbourg a cin
kofin Faransa. Duk da cewa raunin bai kai ga yi masa tiyata ba, likitoci sun ce tilas ya yi jiyyar makwanni 10 Buffon mai shekaru 41 ya dade yana fatan samun nasarar lashe kofin gasar zakarun Turai a kungiyoyin da ya bugawa, sai dai hakarsa ba ta cimma ruwa ba, la’akari da cewa sau uku yana kaiwa wasan karshe, damarsa tana barewa. To baya ga wasan PSG ta Manchester United, za a fafata tsakanin AS Roma da FC Porto a gasar ta zakarun Turai.
Kotu ta umurci EFCC ta ci gaba da tsare Babachir Lawal, ba beli
Wata babbar kotun gwamnatin tarayya ta bayar da umurnin cewa Mr Babachir Lawal, zai ci gaba da zama a hannun hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa EFCC Kotun ta sanya ranar Laraba, 13 ga watan Fabreru a matsayin ranar da za ta ci gaba da sauraro shari'ar
Hukumar tana zargin tsohon sakataren gwamnatin tarayyar da aikata laifuka 10 da suka shafi hada baki tare da sama da fadi da kudaden gwamnati
Wata babbar kotun gwamnatin tarayya da ke da zama a Abuja, ta bayar da umurnin cewa tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Mr Babachir Lawal zai ci gaba da zama a hannun hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa da yiwa dukiyar gwamnati zagon kasa (EFCC) Hakan na nufin cewa hukumar EFCC za ta ci gaba da tsare Mr Babachir Lawal, bayan da kotun a ranar Talata ta ki amincewa da bukatar bayar da belinsa Kotun ta sanya ranar Laraba, 13 ga watan Fabreru a matsayin ranar da za ta ci gaba da sauraro shari'ar.
Monday, 11 February 2019
[Music] sabuwar wakar Nura M Inuwa - Sakon INEC
Kwallon kafa;; Champions League Man United da PSG
Man United za ta karbi bakuncin Paris Saint-Germain a wasan zagaye na biyu a gasar cin kofin zakarun Turai da za su kara a Old Trafford a ranar Talata. Wannan ne karon farko da kungiyoyin za su fafata a babbar gasa musamman ta zakarun
Turai ta Champions League. Jose Mourinho ne ya kai United zagaye na biyu a gasar ta Champions League ta bana, daga baya ta kore shi a cikin watan Disamba ta nada kocin rikon kwarya Ole Gunnar Solskjaer. Solskjaer ya ja ragamar United wasa 11, ya kuma ci 10 da canjaras daya, tun bayan da ya maye gurbin Mourinho. Rabon da United ta kai karawar daf da na kusa da na karshe tun kakar 2014, ita kuwa PSG tun 2016 rabon da ta kai matakin. Dan wasan PSG, Neymar da kuma Meunier ba za su buga karawar ba, sakamakon jinya da suke yi haka kuma da kyar ne idan Edison Cavani zai buga wa kungiyar Faransa fafatawar. Manchester United tana da kofin Zakarun Turai uku, ita kuwa PSG ba ta taba dauka ba.
Dan Arewa ya kirkiri na'urar da ta girgiza duniyar fasaha
Arewa gida
Wani shehin malamin zamani daga yankin Arewacin Najeriya Dakta Idris Ahmed da yake da digirin digirgir a fannin ilimin Cryptology' dake zaman haifaffen garin Mubi jihar Adamawa mazaunin birnin Coventry a Kasar Burtaniya ya kafa tarihi. Dakta Idris Ahmed dai ya girgiza duniyar fasaha ne bayan da ya samu nasarar kirkira tare kuma da assassa fasahar tsaro na na'ura mai kwakwalwa da za'a yi anfani da ita akan mota wacce za ta iya tuka kanta
Kamar yadda muka samu dai cewa ita fasahar tsaron da ya kirkira an yi ta ne ta yadda ba za'a iya yiwa motar kutse (hacking) ba, wacce zata iya tuka kanta taje ko'ina ta dawo ba tare da direba ba. A wani labarin kuma, Wani matashi dake ikirarin zama dan a-mutun shugaban kasar Najeriya kuma dan takarar tazarce a jam'iyya mai mulki ta All Progressives Congress (APC) watau Shugaba Muhammadu Buhari mai suna Adamu Kabir Matazu yayi barazanar kashe kan sa idan Buharin ya fadi zabe
tur kashi:: An yiwa shugaba Buhari ruwan duwatsu a Ogun
A yayin yakin neman zaben da shugaban kasa Muhammadu Buhari yaje yi jihar Ogun an samu wata 'yar hatsaniya da tasa aka jefeshi tare da shugaban jam'iyyar,Adams Oshimhole Lamarin dai ya aukune a yayin da shugaban
jam'iyyar APC, Adams Oshiomhole ya hau dandamali zai fara jawabi, daga nanne sai aka samu wasu suka fara jifar shi da robar ruwa hadda dutsen, rahotanni daga Punch da Thisday sun tabbatar da cewa daya daga cikin duwatsun Da aka jefo yayi kan shugaban kasa Muhammadu Buhari dake zaune saidai daya daga cikin masu tsaron lafiyarshi ya tare dutsen be isa ga shugaban ba Hakan na faruwa sai jami'an tsaro suka kewa
shugaba Buharin da mataimakinshi, Farfesa Yemi Osinbajo Rahotannin sun nuna cewa hakan ya farune sanadiyyar 'yan takarar gwamna biyu da ake cece-kuce akan su a jihar wanda kowane ke
ikirarin cewa shine dan takarar jam'iyya, wannan lamari ya sa Uban jam'iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu yin jifa da tutar APC sannan ya fice daga gurin taron cikin fushi yayin da shugaba
Buhari ke yin jawabi A jawabinshi, shugaba Buhari ya bukaci jama'ar jihar da su zabi shugaban kasa na APC amma a matakin gwamna su zabi wanda suke so. Kamin wannan lamari saida gwamnan jihar, Ibikunle Amosun amosun ya roki jama'ar da suka taru a gurin da kada su kunyatashi a gaban shugaban kasa.
TUNA BAYA:: YAN FINA-FINAN KANNYWOOD DA SUKA RIGAMU GIDAN GASKIYA
Allahhu Akbar duniya ba gidan zamaba Allah
Ubangiji yasa muyi kyakyawan karshe ga wadansu daga cikin yan Film din Hausa na Kannywoood da suka rigamu gidan gaskiya fatanmu Allah Ubangiji yasa sun huta
Gasu Kamar Haka
1. Balaraba Muhammed
2. Ahmed S. Nuhu
3. Jamila Haruna
4. Husaina Gwambe (Tsigai)
5. Shu'aibu Dan Wanzam
6. Nura Muhammed
7. Ali Bala
8. Night Kasim
9. Maijidda Muhammed
10. Hamza Jos
11. Tijjani Ibrahim
12. Umar Katakore
13. Shu'aibu Kulu
14. Baffa Yautai
15. Hajiya Hasana
16. Aisha Kaduna (Shamsiyya)
17. Rabiu Maji Magani
18. Kabiru Kabuwaya
19. Rabilu Musa (Dan ibro)
20. Hauwa Ali Dodo (Biba problem)
21. Hafsat Sharada (Mai Aya)
22. Zurkifulu Muhammed
23. Aisha Dan kano (Sima)
24. Malam Waragis
25. Safiya Ahmed
26. Maryam umar
Ya Allah ka jikansu da gafara. Amin.