. Dan Arewa ya kirkiri na'urar da ta girgiza duniyar fasaha - hausanet hausanet





Monday, 11 February 2019

Home › › Dan Arewa ya kirkiri na'urar da ta girgiza duniyar fasaha

Subscribe Our Channel


Arewa gida

Wani shehin malamin zamani daga yankin Arewacin Najeriya Dakta Idris Ahmed da yake da digirin digirgir a fannin ilimin Cryptology' dake zaman haifaffen garin Mubi jihar Adamawa mazaunin birnin Coventry a Kasar Burtaniya ya kafa tarihi. Dakta Idris Ahmed dai ya girgiza duniyar fasaha ne bayan da ya samu nasarar kirkira tare kuma da assassa fasahar tsaro na na'ura mai kwakwalwa da za'a yi anfani da ita akan mota wacce za ta iya tuka kanta


Kamar yadda muka samu dai cewa ita fasahar tsaron da ya kirkira an yi ta ne ta yadda ba za'a iya yiwa motar kutse (hacking) ba, wacce zata iya tuka kanta taje ko'ina ta dawo ba tare da direba ba. A wani labarin kuma, Wani matashi dake ikirarin zama dan a-mutun shugaban kasar Najeriya kuma dan takarar tazarce a jam'iyya mai mulki ta All Progressives Congress (APC) watau Shugaba Muhammadu Buhari mai suna Adamu Kabir Matazu yayi barazanar kashe kan sa idan Buharin ya fadi zabe