. Gwamnati ta bankado sabuwar hanyar da Atiku ya shirya yiwa zaben Najeriya kafar-angulu - hausanet hausanet





Tuesday, 12 February 2019

Home Gwamnati ta bankado sabuwar hanyar da Atiku ya shirya yiwa zaben Najeriya kafar-angulu

Subscribe Our Channel


Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce jam'iyyar adawa ta PDP tare da dan takarar ta na shugaban kasa da sauran jiga-jigan ta sun dauri aniyar haifar da rikici da tarzoma da za ta kawo yamutsi har ta kai ga lalata zabukan gama gari da ake shirin yi.

Ministan yada labarai na gwamnatin tarayyar, Mista Lai Mohammed ne dai ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da ya gudanar a ofishin sa dake a garin Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya.