. Aisha Buhari tayi karin haske game da wasu halayya da dabi'un Mijin ta - hausanet hausanet





Tuesday, 12 February 2019

Home Aisha Buhari tayi karin haske game da wasu halayya da dabi'un Mijin ta

Subscribe Our Channel


Uwar gidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha, a yau Talata tayi karin haske dangane wasu dabi'un Mai gidan ta sabanin yadda wasu ke jingina ma sa dabi'u na tsanani da rashin jin kai ko

kuma hali na ko in kula. A yayin da ake daf da gudanar da babban zaben kujerar shugaban kasa, Aisha a yau Talata ta ce mai gidan ta da ya kasance shugaban kasar Najeriya mutum ne mai tsananin tausayi gami jin kai da nuna ga ƙauna ga al'umma. Aisha wadda ta jagoranci tawagar Mata da Matasa na kungiyar yakin neman zaben Buhari, ta bayyana hakan ne a hedikwatar cibiyar ma'aikatan sufurin ta NURTW da ke babban birnin kasar nan na tarayya.