. Kun san yatsan da za a dangwala kuri'a da shi? - hausanet hausanet





Wednesday, 13 February 2019

Home Kun san yatsan da za a dangwala kuri'a da shi?

Subscribe Our Channel



Batun yatsan da mutane ya kamata su yi amfanida shi domin dangwala kuri'arsu a lokacin zabe na neman ya kawo rudani a Najeriya. Wani sako da aka yi ta yadawa a shafukan sadazumunta musamman WhatsApp ya bayyana cewa

hukumar zabe ta canza tsarin yadda mutane za su jefa kuri'a. Cikin bayanin da ake yada wa har da yatsan da hukumar ta ce za a yi amfani da shi. Amma Hukumar INEC ta karyata labarin inda ta

ce masu zabe za su iya amfani da kowane yatsa yayin dangwala kuri'arsu. A wani bayani da ta wallafa a shafinta na Twitter, hukumar zabe ta bayyana cewa masu zabe za su iya amfani da kowane irin yatsa su dangwala kuri'arsu Mai kada kuri'a zai iya amfani da kowanne yatsa domin kada kuri'arsa. Amma ya tabbatar da cewa tawadarsa tana cikin zagayen akwatin jam'iyyar da ya dangwala wa, kada ta shiga cikin akwatin wata jam'iyyar daban," in ji INEC.

Saboda haka wannan labarin kanzon-kurege ne da wasu 'yan ta-da-zaune-tsaye suke yadawa Sakon karya da ake yada wa Sakon ya kunshi cewa "a yanzu ba za ka dangwala kuri'a da babban yatsa ba sai dai da dan ali wato manuniya. Duk kuri'ar da aka kada da babbar yatsa za a soke ta. Tambayar a nan ita ce, me ya sa ba a wayar da kan 'yan kasa ba har sai yanzu? "Me yasa INEC ta boye irin wadannan bayanai masu amfani har sai kwana kadan kafin zabe?"Don Allah ba wai karantawa kawai za ku yi ba ku tura wa sabbin masu kada kuri'a don su fadaka. "makomar kasarmu ta dogara ne a kan yatsan dan ali wato ('yar manuniya)", in ji sakon. Sai dai babu wata hujja da ke tabbatar da sahihancin sakon, domin kuwa hukumar zabe ta yi bayani akasin hakan.