Friday, 31 August 2018
![](https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEhNbX1LILTA5g0iJFR49IUaJ4082TXiyPHfqVAa_FTnBAR63OKDmUTOY92HZjBpoWXYiNra7F_yKzFyqN24uz4wcewUQHAdRB7YYXbjq8SHuBFAaIyLQAKhEY08VqG_Gdn7VpO0sIukkzY/s640/Kai+Ka%252Cisa+da+20140708_105313.jpg)
HANYOYIN MALLAKAR MACE CIKIN SAUKI!
![](https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEjco3_fD9PvbeL74usF16NyqyLrMo-e_C60Pdd68TokFqqVDCvvStHiog0C_1rreckyCHh89XviLmxTUqsn4Mp1xPJ4qgbPM_hRFUhRkoVo_Hu_YTOAt0xa5LKwX7IT0jmMTGHr3oKUqkI/s640/tansfaer+football.jpg)
Yadda za a rufe kasuwar ' yan wasa ta Turai
An saye Sahin daga Borussia
Werder Bremen ta kammala sayen Nuri Sahin daga Borussia Dortmund.
Zai saka riga lamba 17 a kulob din na Jamus.
Hull City ta sayi dan wasan bayan Villa
Hull City ta sayi dan wasan bayan Aston Villa Tommy Elphick, mai shekara 30,domin ya buga
mata wasan aro na kaka daya
Nariano ya maye Ronaldo
Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta bayyana dan wasanta Mariano Diaz a matsayin wanda zai cigaba da saka rigar Cristiano Ronaldo,mai lamba
bakwai.
Ina cikin wadanda suka fi iya aiki —Mourinho
Kocin Manchester United Jose Mourinho ya ce ko bai ci gasar Firimiya ba, zai kasance daya
daga cikin wadanda suka fi iya aikin horas da 'yan wasa. Mourinho ya ce shi kadai ne kocin da ya ci kofi
takwas a Italiya da Sifaniya da Ingila.
Ronaldo zai sayi kulob din La Liga
Tsohon dan wasan gaban Brazil Ronaldo zai sayi kulob din La Liga Real Valladolid ranar Litinin,
In
ji, AS.
Mourinho: Na ji dadin yadda masoya Man U
suka yi mini
Kocin Manchester United. Jose Mourinho ya ce shi ya ji matukar dadin yadda masoya kulob din
suka yi bayan kulob din ya sha kaye a Old Trafford ta hannun Tottenham.
A jawabin da ya yi wa manema labarai dazu, Mourinho ya ce masoyan Man U din sun nuna wa
kulob din goyon bayan duk da cewa ya sha kaye a gida
.Tsakanin Mo Salah ne da hukumar kwallon kafa
ta Masar
Kocin Liverpool Jurgen Klopp ya yi tsokaci kan matsalar Mo Salah da hukumar kwallon kafa ta
Masar: "Game da lamarin hukumar kwallon kafa ta Masar ba zan iya magana da yawa ba, abu ne
tsakanin dan wasan da hukumar kwallon kafar. Na yi magana da Mo game da shi. Ba mu da
hurumin tsoma baki a lamarin. Za su warware matsalar, na yi imanin hakan"
Liverpool za ta dauki koci kan 'throw-ing'
Kocin Liverpool Jurgen Klopp yana magana game da daukar kwararre kan wurga kwallo (wato throw-ing),Thomas Gronnemark. Klopp ya ce Gronnemark ne ya fi iya wurga
kwallo a wasan kwallon kafa. Ya kuke ganin wannan matakin da kocin Liverpool ke son daukawa?
Da wa Chelsea za ta fafata a gasar Europa?
Arsenal tana rukuni na E tare da Sporting Lisbon (ta Portugal) da Qarabag (Azebeijan) da kuma
Vorskla (ta Ukraine) Chelsea tana rukuni na L tare da PAOK (ta
Girka) da kuma Borisov (ta Belarus) da kuma Vidi (ta Hungary) Celtic tana cikin rukuni na B tare da Salzburg (ta Australiya) da Leipzig (ta Jamus) da kuma Rosenborg (ta Norway)
Ina Luka Modric ke son zuwa?
Dan wasan tsakiyar Croatia Luka Modric, mai aashekara 32, ya ce yana son cigaba da zama a
Real Madrid "na tsawon shekaru masu yawa nan
gaba ," yayin da shugaban kulob din, Florentino
Perez, ya ce Inter Milan ta so "ta ki biyan
komai" a zawarcin da ta yi wa dan wasan a
lokacin bazara, in ji Football Italia .
12:33
A wane rukuni Arsenal za ta buga a gasar
Europa?
FC Salzburg za ta kasance a rukunin B. Ita kuwa
Zenit St Petersburg za ta taka leda ne a rukunin
C. Anderlecht tana rukunin D yayin da Arsenal ke
ruykunin E. Olympiakos tana rukunin F. Ita kuwa
Villarreal tana G. An ambato Lazio a rukunin
H.An saka Besiktas a a rukunin I. Sevilla kuma
za ta shiga J. Dynamo Kiev za ta fafata a
rukunin K.
12:28
Ana fitar da jadawalin gasar Europa
Yanzu haka an fara fitar da jadawalin gasar
Europa. Bayer Leverkusen za ta kasance a
rukuni na A.
12:08
PSG na son kammala sayen dan Kamaru
Zakarar gasar Faransa Paris St-Germain tana
fatan ganin ta kammala yarjejeniyar sayen dan
wasan gaban Stoke City da Kamaru mai shekara
29, Maxim Choupo-Moting, in ji Mail.
12:03
Wane dan wasa ne zai bar Liverpool a yau?
Ta yiwu Lazar Markovic zai kasance dan wasa
daya tilo da zai bar Liverpool a yau, kamar yadda
Liverpool Echo ta ruwaito.
Jaridar ta ce dan kasar Serbiya din mai shekara
24 yana da zabi tsakanin kungiyar PAOK ta Girka
da kuma kungiyar Anderlecht ta Belgium.
Dan wasan gefen ya koma Anfield ne a lokacin
zafi na shekarar 2014, kan kudi fan miliyan 20
amma bai buga wa Reds wasa ba tun shekarar
2015, inda yi ta buga wasan aro cikin yawancin
shekaru ukun da suka gabata.
11:53
Chelsea ta ki sayen dan wasan Lyon
Chelsea ta yi watsi da damar sayen dan wasan
tsakiyar Lyon da Faransa Nabil Fekir, mai
shekara 25, a lokacin zafi, kamar yadda
shugaban kungiyar kwallon kafar ta Faransa
Jean-Michel Aulas ya fada. Liverpool dai tana
hakon Fekir, kamar yadda Mail ta ruwaito
11:46
Everton na da kwarin gwiwar rike Lookman
Everton tana da kwarin gwiwar cigaba da rike
Ademola Lookman, duk da cewar RB Leipzig,
wadda ta yarda ta biya fan miliyan 25, kan dan
wasan mai shekara 20, tana son dan wasa, in ji
Liverpool Echo
Assalamu alaikum
Jama'a barkanku da zuwa wannan shafin da za
mu kawo muku labarai game da yadda za a rufe
kasuwar musayar 'yan wasa ta Turai
![](https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEggW8I_-lE6G8PdXALK4wMVoVgG97Eqj9S0ttC13MAsbYfaqjv6OSVfmAfw27oLJjASIDFa5KPg6iPFE20adhhItkNmgnfVg_GLQkVk6AmQ09lVx16joT5wRd3QVFHdOnyvsmlRYzBGSNY/s640/vllkyt6p8qmrc5mtr.9fe191b5.jpg)
NI BA KALAR MATAN DA KUDI KE RUDA BANE- Inji Jaruma rahama sadau
![](https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEg77zMnFEWrFRFhVyufXaoOlGM7byxUleBkRZFI6p83ep7DHdB9TK2lcheEO7HzWGZItiCijnciFsZGiu-_aakhGJ75skZd8pNhV_a701jQuAs7K9BZ1kKuTvmHqP9MQidJ-Myln7FVtm8/s640/FB_IMG_1513168377707-696x437.jpg)
Zaki yayi masa rungumar soyayya
Thursday, 30 August 2018
![](https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEgI3bitFwSTYKvxS5_FNLOKsTp_xpZmNE4nhuzNje4kmGMA4RtLeiBiKHebQsnKVrB_sz-yenkl00qIGLyYT-4oMK0z3MqKBMtKBrfr9PUXsg-0btFhupwGB8ujgYjJCFbFyGZpA_zP-Bo/s640/IMG-20180618-WA0001.jpg)
WAYYO CIKINA
WAYYO CIKINA
Wani Mai Gida Ne Yaji Sanarwar Duk Wanda Yake D Yara 5 Xa A Qara Albashinsa Yakai Dubu Dari Sai Mai Gidan Nan Ya Cewa Matarsa Kinga Dama Inada Da Guda 1 Tare Da Wata Budurwata Amma Gudun Bacin Ranki...........
Yasa Ban Gaya Maki Ba To Yanxu Inaso Inje In Karbo Dana Daga Wurin Ta Kinga Saimu Hada Da "Ya"Yanmu Guda 4 Kinga Sun Cika Biyar Kenan Matar Dai Bata Ce Uffan B Mai Gida
Ya Dauki Hula Y Fita Koda Gogan Ya Dawo Da Shegen Dansa Sai Y Tarar Saura Guda 1 Mai Gida Ya Tambayi Matarsa Ina Sauran 3 Matar Tace Ashe Bakai Kadai Kaji Sanarwar Ba Suma Babansu Yaxo Y Tafi Dasu
![](https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEiQezV9sD9Grhfzhyphenhyphennu6JRRUrFxZ4-z6_zi6_K53IfaYYgt6QW8DgG_WLpSQSheheiW34xl5kgT0xBdym_wZZwP514s7f0yfA3VewDW_x7TzqS3Dhuo4EI04m5WRgx6wmMdlGso_P6ce40/s640/croatia-luka-modric-poses-with-the-fifa-golden-ball-award.jpg)
Modric ya lashe kyautar gwarzon dan wasan Turai
Hukumar kwallon kafar Turai UEFA ta mika kyautar gwarzon dan wasan shekara na nahiyar ga Luka Modric dan wasan kasar Crotia da ke
taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid yau a Monaco bayan rawar da ya taka a kakar wasan da ta gabata. Bayan karbar lambar yabon Modric, ya yaba da irin dawainiyar da ya ce mahaifinsa ya yi masa
wanda shi ne ya jajirce tare da bashi kwarin gwiwar ganin ya kai matsayin da ya ke yanzu. Modric wanda ya tallafawa Club dinsa wajen
lashe kofin zakarun Turai karo na 3 a jere ya
kuma yi rawar gani a gasar cin kofin duniya inda ya kusa kai kasar ta sag a nasarar lashe kofin duniya kafin faransa ta yi waje da su.
Modric mai shekaru 32 ya ce ya yi matukar alfahari da lambar yabon tare da mika godiya ga
ilahirin wadanda suka horar da shi tamaula a gida da kuma a bangaren kungiyoyi. Luka wanda ya faro
kwallonshi da Club din Dinamo Zagreb kafin kulla kwantiragin shekaru 4 da Tottenham daga bisani kuma Real Madrid
ta saye shi kusan shekaru 6 da suka gabata
![](https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEhjm3yfCi1ImCjoTFZDQnNghrPnAxW9ENsMETKt7u7qaDjfkvGZUpO1dGzVsX5awEvWMUBM4MdX8miEKb8N74X3Gn0cesfzdr8kL3YtgR096mUpsfinOCB9UXTsHzL-oRvHlM6HGsEmTQI/s640/champions-league.jpg)
UEFA Champion league ta fitar da jadawalin gasar zakarun Turai na bana
Hukumar kwallon kafar Turai UEFA ta fitar da jadawalin kungiyoyi 32 da za su fafata a gasar lashe kofin zakarun Turai, inda ta rarraba su
zuwa rukuni 8
Rukunin farko na jadawalin, wato rukuni A ya kunshi kungiyoyi irinsu
Atletico Madrid da Dortmund da Monaco da Club Brugge.
Sai kuma rukunin B da ya kunshi Barcelona da TOTTENHAM da PSV da kuma Inter Milan
Akwai kuma rukunin C da ya kunshi PSG da Napoli da LIVERPOOL da kuma Red Star Belgrade.
Yayinda rukunin D ya kunshi kungiyoyi irinsu Lokomotiv Moscow da Porto da Schalke da kuma Galatasararay
Akwai kuma rukunin E daya kunshi Bayern Munich da Benfica da Ajax da kuma AEK Athens
Ka zalika rukunin F ya kunshi kungiyoyi irinsu MAN CITY da Shakhtar da Lyon da kuma Hoffenheim
Rukunin G kuma akwai mai rike da kambu Real Madrid da Roma da CSKA Moscow da Viktoria Plzen
Yayinda rukunin H kuma ya kunshi Juventus da MAN UTD da Valencia da kuma Young Boys.
![](https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEjqcWrPyX_1Snc6-_fvEYX8te0s6g080ORZPqJkuineYK-vvGMjpX8NhTXIruPevmJCPW7ovgSDxzHyST1R5yQhBg4J4ozLSQHNUX_fGEFxCQrHPYhP9NcBzDQU81cdbISwo7kgUVyYujQ/s640/hutunan+masoya.jpg)
YAUCHE RANAR NUNA SOYAYYA
![](https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEhCHIYi8Pz9ZcDfrX4kQAOxl-FsB6OdVFAOvzcx7wakygXFty16FZqz-OsSZvxt9HZ_1A-33iTOgqm1aiRXL41FFFSf5ZRsUeLxj0GVt-M0zeTUZ3gdO9b9gjHFwiC7JKFltq5quU4ZKBc/s640/FB_IMG_14819092727475137.jpg)
YAR BIRNI KO YA QAUYE Part -1
YAR QAUYE KO 'YAR BIRNI PART 1
Na Rahamat Muh'md Rufa'i Nalele
Bismillahirrahamanur-rahim Part 1
0818 152 1679
Misalin qarfe 1:30am nadare ya tashi dan yin sallar dare wato lafula.
Bayan yayi alwa'la Zaiyi sallar kenan yaji kukan yarinya Abin yabashi mamaki Kamar zae share amma dae. Yafasa yabude kofar ahankali yana nazarin tsakar gidan Yayah me zaka kayi awaje Yaji qalinsa Amar yafa'di hakan Yace naji kukan wata yarinya ne saurara kaji Canko shima yaji kukan yarinyar yace plx yayah
karka tafi gunta dan Allah. kasanifa bamusan kan qauyan nanba plx don't leave Yace no brother bazan iyaba in fitaba inajin Kukanta har cikin zuciyata........
Bae jira cewar Amar ba yafita
Ga mamakinsa sae ya dinga jin kukan sosae Tsayawa yayi cak ya tattara nutsuwar shi dan tantance inda kukan yafi fitowa Kofar gidan yanufa yabu'de Ikwan Allah Wata yarinya ya gani durkushe bata hucce 10 years ba ya haskata da wayarshi
Sam baiji tsoron komae Ba ya nufeta
Yace keee mekikeyi anan tayi shuru
Yaqara tambayarta nanma shuru tayi. Abinfa ya bashi haushi ya daka mata tsawa Ba magana nake miki bah Aburkice tatashi tana cewa um am dan Allah.......
karka daken wlhi zan gayama Yace ina jinki Tace baba Larai ce tace saita kasheni inhar ban kawo mata kudintaba Kuma wlhi Iniya ne 'dan hansae ya bugemin farantin Yace farantin me Tace farantin tallan duk goran yazube akwata shine naje nagaya mata wae batasan zancan ba innemo mata ku'dinta. Kuma naje gan hansae tace ko asi bata maganinta bare nera talatin da
biyar Shine dana koma nagaya mata tace wlhi kudinta zanne momata kota kasheni Yace tun yanshe abin yafaru tace tun mangariba,,,,,,,,,,,
yace shine baki koma gidaba har yanzu tace To ai idan nakoma zata kashenin. dan ina kalla isma'ila 'dazo yazo nemana. Shine na6oyema
ganinsa Zamu ci gaba kukasance damu Dan kawo muku cigabansa
www.hausanet.ml zamuci gobe in Allah ya kaimu
Amin
Wednesday, 29 August 2018
![](https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEjlR8kfvThVj4nFQmHUmXrljRJ6DpLOaQx2KFhOXPZGAFEtA8ORT8Bfh9yRz-ebCvHRMT_SAT06RIit8hcl5OOaxLe-YRkjVRQ7kVGYOjsUsefKPHjA-bJYLnpIY3dHJmdxjZYUFY1CM4Q/s640/tiket+champion.jpg)
Yadda Ta Kaya A Gasar Neman Tikitin Shiga Wasannin Champions League
![](https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEjUXmK5uI97kbYJwUXSfRLnUPRsqKfC7Lws1D2jCH39fHdQFqTIrBAvwnjcbHOI01caUt3IV8gdzyH24Mn9jIt8rzS2ohs2bh022x9bgO26m9-2dQQ4yBvybWLGiyDzbcZworkkggN5b4U/s640/Dup%252801%2529FB_IMG_14619151782297637.jpg)
LABARIN WASU MASOYA
Labarin wasu masoya ne zan baku da fatar zaku fahimce ni. Sudai wadannan masoya sun kasance
daga farkon soyayyar su,kamar ‘yan biyu ne koda yaushe suna tare,suna fadawa juna maganganun soyayya har ma da dariya,basu son abinda zai sosa ran daya.soyayya tayi karfi sosai har alkawarin aure ya shiga
tsakaninsu,saboda sun yarda da
junansu fiye da kima.To shidai yaron
dan talakawa ne.Gidansu ba masu wadata bane,amma duk da haka ta
nuna ta amince dashi,ya kamu da
kaunarta kauna mai tsanani.Ana cikin haka sai chanji ya shiga.masu kudi da manyan motoci suka fara farautarta kuma wani daga cikin
ya samu amincewarta,dan shi babban dan kasuwa ne kuma ya nada kudi.Ya aureta yakai gidansa.
Allah SWA ya arzuta ta da juna biyu
har ya kai wata ukku,sai ya fara jin ya gaji da ita,karshe dai ya sake ta saki
3 ta koma gidansu tana kokawa da
kannenta wajan cin abinci,rayuwarta ta lalace..Shi kuma tsohon saurayin nata Allah.ya bashi wadata bayan
ta auri mai kudi,shi kuma duk da yana talaka sai wani attajiri ya bashi ‘yarsa,kuma tafi ta kyau.wannan kenan,Dan Allah mu kiyaye maza da mata mu daina sanya kwadayi cikin
harkar aure dan gudun afkawa cikin
wahala.
![](https://2.bp.blogspot.com/-pAkyABlSI9I/V5Vb3h5bgGI/AAAAAAAAEEg/03XLR_fUHfciuaylJJCi1GxDG2Lw9WqVwCLcB/s320/couper.jpg)
An kama wasu matasa 2 suna luwaɗi a makabartar jahar Kano
Allah ya tona asirin wasu matasa yan luwadi a jihar Kano, yayin da aka kama suna turmi da tabarya suna aikata badala a cikin wata. makabarta cikin birnin Kano kamar yadda rahotanni suka tabbatar. NAIJ.com ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a ranar Litinin data gabata na watan Agusta, inda wasu matasa a karamar hukumar Gwale suka kama yan luwadin a lokacin da suke tsaka da tafka wannan mummunan laifi Wannan lamari yayi matukar bata ma mutannen wannan unguwa rai, inda suka fusata suka yi ma yan luwadin
dukan kawo wuka, suka kusan kashesu, da kyar da sudin goshi Yansanda suka kwacesu. Kaakakin rundunar Yansandan jahar
Kano, Magaji Musa Majia ya tabbatar da.faruwar lamarin, inda yace a yanzu haka matasan suna hannunsu, kuma.bincike ya kankama zuwa yanzu..Jama’a da dama a jihar Kano sun koka da karuwar matasa masu shiga.mummunan dabi’ar nan ta luwadi inda.namiji ke neman namiji, da madigo.inda mace ke bin mace don samun.biyan bukata, sai dai yawancin jama’an.sun danganta lamarin ga illolin shaye.shaye.
![](https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEhqPnXUSCJzDJIqSXGQosC3KWoWLysMDWQRBmbyu0Ls6G7ufvKTHR5lvXPDO8UWdT8HdAMIWSBjvFt0PrypIlW8Kp8KAJjjW3nOqT6WOHTjCed_3oqLJwpYAiHlwxa6EA1R48q1GRESj3w/s640/IMG10009.jpg)
MATASHI lukman - banban buri a duniya na hadu da hadiza gabon
amar Yadda Hausawa Kance Kowa Da Abunda Ya Dameshi Haka Kuma Kowa Da Masoyinshi, Lallaikam Wannan Batu Haka Yake. Na Samu Damar Zantawa Da Wani Matashi Dan Asalin Jahar Naija Wanda
Yanzu Haka Yana Zaune Garin Kano
Tsawon Shekaru Hudu Domin Kawai
Allah Ya Hadashi Da Daya Daga Cikin Fittun Jaruman Masna’antar
Kannywood, Wato Jaruma Hadiza Aliyu Gabon, Wakilinmu Auwal M Kura Ya Samu Damar Tattaunawa Da Wannan Matashi Mai Kimanin Shekaru 23 A Duniya Mai Suna Lukuman
Wanda Akeyi Masa Take
Da (Na Gabon) Ga Kadan Daga Cikin Yadda Tattaunawa Tasu Ta Kasance:vAuwal M.kura: A Takaice Zanso Sanin Sunanka da Kuma Takai Tattacen Bayani
A kanka? Lukman: Sunana Lukman Amma Amfi Kirana da Na Gabon, Yan Zu Haka Inada Kimanin Shekaru 22 zuwa Da Uku Sannan Ni Haifaffan Garin Naija Ne, Kuma Nazo Jahar Kano Tsawon Shekaru Hudu Ke Nan .
Auwal M.kura: Mai Ya Kawo Jahar
Kano? Lukman : Toh Babban MaKasudin Zuwana Kano Tun 2014 Shine,Nazo ne Domin Na Hadu Da Hadiza Aliyu Gabon, Auwal M.kura: Toh Tsawon Wannan Shekaru Ko Kasamu Damar Ganin Ita Hadiza Gabon Din ? Lukman: Gaskiya Aa
Auwal M. Kura: Bakabi Hanyoyin Da
Kasan Zaka Ganta Bane ?
Lukman: A Tsawon Wadannan Shekaru Kullum Cikin Bin Duk Wata Hanya Da Zaisa Ko Sau Daya Na Ganta ne , Amma Haryana Bamu Hadu Ba,Akwai Gurare Da Yawa Wanda Har Kudi Sukan Amsa A
Gurina Da Sunan Zasu Hadani Da Ita
Amma Daga Baya Bazasu Hadani Da Ita Ba, Numbobin Waya kam Inada Sama Da Guda Ashirin Wanda Duk Sai Nabiya Ake Bani Ana Cemin Ta Hadiza Gabon Ce Daga Baya Koda Nakira Sai Wani Can Daban Zanji Ya Dauka , Auwal M kura: Toh Ganin Yadda Ka
Fuskanci Wadanan Kalubale, Kuma Baka Cimma Muradinka Na Ganin Abar Began Taka Ba , Wato Hadiza Gabon, Baisa Kaji Ka Hakura Ba?
Lukman: Kokadan Illa Kara Samun
Karfin Gwaiwa Danayi, Domin Kuwa
Yanzu Haka Nayi Mata Wakoki Da dama Ko Allah Zaisa Wakar Taje Gareta,
Auwal m.kura: Mai Yasa Duk Sauran
Jaruman Hausa Film Nan, Kai KazabivHadiza Gabon?
Lukman: Ni Dai Kawai Ita Allah Ya
Samun Naji Tana Burgeni , Kuma Ina
Matukar Girmamata Saboda Mace Mai Tausayi Da Kamala,
A Karshe Wani Kira Zakayi Da Ita
Wannan Jarumar Da Kuma Hanyar Da Zata Sameka Koda Ta Ga Wannan Fira Da Mukayi Da Kai Don Ganin Kun Hadu Da Juna?
Lukman: Toh Ni Yanzu Ina Zaune A
Kano ne, Amma Idan Allah Yasa
Wannan Sako Ya Isheta , To ina
ronkanta Data Cika Burin Na Haduwa Da Ita, Domin Kuwa Burina A Duniya Shine Naga Na Hadu Da Hadiza Aliyu Gabon, Ta Hanyar Tuntbarka Dan Jarida(Auwal M Kura) Ko Gidan Jaridu Koda Jaruma Hadiza Aliyu Gabon Ta Gamu Da
Wannan Sako Zata Iyya Tuntunbar Gidajen Jaridu Kamar Haka: Jaridar Tarayya Mikiya Rariya Ko Kuma Matashin Dan Jarida #Auwal M Kura A Number Kamar Haka :
0818 152 1679
![](https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEgIF3N6m1SJafJd8b8ARVdIZN1aSOfVWcTCyQ1ldGhJWSA6kObcYYYHpKxbiXbeGFGlmXVF2pbPz_1qMgE828OdYH_LrDqaGBLWSfz-cTou3GkbESYAezo24Hg475KYCWrxXs7I8sjQpg8/s640/cr7+ball+mafi+kyau.jpg)
An zabi kwallon Ronaldo a matsayin wanda ta fi kyau UEFA CHAMPION LEAGUE
![](https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEgr3TWItKXacSugZ4wSbtIeEODtzDqbIIh3uSUwmkkdt_Oax3jvBVUrTA36DzPxjF1MwZxDBaq0hCvOPrv0vTsRIeqyk_AzBIWMy_5GXU8aNK5-2l0_RBz7Y4YNRZHZpQpyuyL_r9QcjU8/s640/vllkyt1a274p9926qg.r320.08502432.jpg)
Tarar aradu da ka: wasu Matasan jihar Benuwe sun ɗana ma Sojoji tarko, sun kashe Soja 1
A ranar Lahadi ne wasu matasan kabilar Tibi na jihar Benuwe suka sake kashe wani jami’in rundunar mayakan Sojan kasa a jihar Benuwe, kamar yadda jaridar Daily Trust ta
ruwaito Premium Times ta ruwaito matasan sun kashe jami’in Sojan ne yayin da yake tafiya tare da wani abokinsa akan babur da misalin karfe 2 na rana, inda suka shirya masa tarkon rago, kuma ya.fada, a kauyen Gbeji dake cikinkaramar hukumar Logo
Tuesday, 28 August 2018
![](https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEi-fTJivE38qvafb9l5hOcYR45KYc1LtP9oATBi_AoBqboQsk-0HEliv0jcpswHC_fv-qSSAB46NyxLiTMLm3_7rquJUp3UqYDkCmm_BWYqBlDvFTESXiYF_WEcyyFSG4Lih5u_0YvuYBc/s640/gerad+pique.jpg)
Gerard Pique Ya Ce Zai Yi Kyau Paul Pogba Ya Koma Nou Camp
Dan wasan baya na
Barcelona mai suna Gerard Pique, mai shekaru 31, ya ce "zai yi kyau idan dan wasan Manchester United, Paul Pogba
mai shekaru 25, ya koma Nou Camp a nan gaba. Dan wasan Chelsea da Ingila Gary Cahill, mai shekaru 32, ya ƙuduri aniyar cigaba da zama a
kulob dinsa na Chelsea duk da yake fama da rashin shiga tawagar Kocin kungiyar Maurizio Sarri
Tsohon dan wasan Arsenal d Thierry Henry, mai shekaru 41, na duba yuwuwar zama a kungiyar Bordeaux a matsayin kocinta saboda tsoron
rashin kudi a kulob din. Matashin dan wasan baya na West Ham,
mai suna Reece Oxford, mai shekaru 19, yana shirin komawa kungiyar Eibar na kasar Spain a matsayin aro inda suke son biyan kudi fan miliyan 1.8
![](https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEjNK7sHszczdAOseO0Gths9rCCcc9vc1GhCEcx81XuGQhq8jCsCSxeNnKSSrrGPjt179myyJY1eADhZ2eGIfeJwAFWgnq_o22arAPeT6AILXyZfh8jsiPma6Cy0jF2HHTngUIVPrW_3R7E/s640/labaran+wasanni+na+wannan+makon.png)
Eden Hazard Ya Ce Zai Koma Real Madrid Saboda Zinedine Zidane
Dan wasan Roma da Netherlands Kevin Strootman, mai shekaru 28, ya yanke shawarar kammala shekaru biyar a Serie A ta hanyar komawa Faransa don shiga Marseille kan kudi fan miliyan £ 22.6m.
Tsohon dan wasan tsakiya na Chelsea kuma
dan wasan Brazil Ramires, mai shekaru 31, yana kusa da sake shiga Benfica a kan aro daga Jiangsu Suning ta kasar Sin. Paris St-Germain
sun yi watsi da "hasashe da
ake danganta su da dan wasan Tottenham da Denmark dan wasan tsakiya mai suna Christian Eriksen, mai shekaru 26, a duniya. Manchester United, sunki amincewa game da zawarcin da kungiyar AC Milan da kuma Atletico Madrid suke yi domin sayen Martiard Anthony mai shekaru 22 da haihuwa. Dan
wasan mai tsaron gida na Belguim da Liverpool Simon Mignolet ba zai bar Liverpool kafin karshen saye da sayarwa na kakar wasa ta.Turai ta ban aba, dan wasan mai shekaru 30 na da damar samun kansa a cikin ‘yan wasan farko a kungiyar.
Arsenal na kan gaba wajan kulla yarjejeniya
tare da kamfanin Adidas, na tallafin kudi fam miliyan £300m kasancewar kwangilarta da Puma da ta kare a karshen kakar wasa ta bana
SAKONNIN SOYAYYA
![](https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEjuexQHEUaZk0NWKHf6Qp_u8gNoG-DmbaUyRJWCgdBxupvX_NoHHqyip1aBfoehHe5ZDVe9bgvGyN4TVOLWC2bSR6C-vTGOuDF14m64Ryi00X9nT3ssYfGYsNfbr8tzIlbEKjn0CRIzYv0/s640/modric_ronaldo_salah2.jpg)
Za'a tantance gwarzon UEFA tsakanin Ronaldo Salah, da Modric
Yan wasan sun hada da Luka Modrić, Cristiano Ronaldo da kuma Muhammad Salah.bA ranar 30 ga watan Agusta da muke cikivhukumar ta UEFA za ta bayyana wanda zai
lashe kyautar ta gwarzon dan wasan kwallon kafar a nahiya Turai. A ranar 31 ga watan Agustan ne kuma
hukumar ta UEFA za ta bayyana gwarzon dan wasanta na nahiyar turai a bangaren gasar Europa a kakarwasan da ta gabata
Taron karrama ‘yan wasan dai zai gudana ne a birin Monaco da ke kasar Faransa. Sauran ‘yan wasa 10 da hukukmar UEFA ta zabo da fari sun hada da, Antione Griezman na
kungiyar Atletico Madrid Lionel Messi na Barcelona, Kylian Mbappe na PSG da Kevin De Bruyne na Manchester City.v‘Yan wasan da ke a matsayi na 8, 9 da kuma 10bsun hada da Raphael Varane na Real Madrid, Eden Hazard na Chelsea da kuma Sergio Ramos
Sharuddan da hukumar da UEFA ke yin amfani da su wajen zabar gwarzon dan wasanta dai sun hada da bajintar da ya nuna a baki dayan
wasannin da ya fafata a matakin kasarsa nahiya da kuma matakin kasa da kasa
Monday, 27 August 2018
![](https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEjIp_BSbd8QAV3uoM2frMk2Y-Up_8OxlPP-aGzJ6u2pGi2Sm1pjeEFNPL-ppgjywJ7ceGuPLAN68RiVhpRb7rFfe75NXneTknB__5vEzKH1elHj6wWSMl3Rlqi_80EAn5PobxPGTSzOOGQ/s640/FB_IMG_15113655573157171.jpg)
(BIDIYO) Yadda wasu masoya suka kwashi 'yan kallo a jami'ar Bayero ta garin Kano
Wani faifan bidiyo da yayi ta yawo a
kafafen sadarwar zamani da kuma ya dauki hankalin jama'a da dama
musamman ma a arewacin Najeriya nadauke ne da yadda wani soja ya nunawa budurwar sa kauna a gaban
jama'a a jami'ar Kano. Bidiyon dai ya nuna sojan sanye da kakin sa da ake kyautata zaton soyayya suke da budurwar ya durkusa a gaban ta yana rokon ta amince da soyayyar sa. Soyayya ruwan zuma: Yadda wasu masoya suka kwashi 'yan kallo a jami'ar Bayero ta garin Kano
(Bidiyo) NAIJ.com ta samu cewa saurayin a cikin wani irin salo na koyi da turawa, ya fiddo zobe daga aljihun sa inda ya
kuma bukaci budurwa da ta mika
hannun ta domin ya saka mata.
Sai dai budurwar wacce take a cikin
shiga ta hausawa sanye da doguwar riga da kuma jan gyale ta fashe da kukan murna ne inda ta ma kasa hada ido da shi......
![](https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEhrhLR7JIQT3uQH3FiONQzICUDWuUOvF0Wmf0nXEu0OUO8WT1ArP9zTwunk7FSfpyT5PLuD_LZE9w7-iN8PARgk3Bou98bZcoiGqkUdEDkUCSMU2vQd-oh9XZN9EPZAcIVyiFizuha5N_4/s640/AIRTEL+data.jpg)
Yanda Zaku Sami Kyautar 20GB A Layin Airtel
Wannan Ba Wai Cheat Bane Daga
Kamfanin ne suke bada Wannan Garabasar Domin Samun Wannan Kyautar Sai Maida Layin Da kuke Amfani Dashi Zuwa Layin Airtel ...
Domin Ku Sami Wannan Garabasar Ku Sami Kowanne Irin Layi daga nan Saiku je gurin ofis din Airtel Na Kusa daku Saiku je musu kunah son Ku Maida Layinku Zuwa Airtel Shikenan Zasu Yi Muku..nAmma Ku Tabbatar Kuna Voters Card,National Id Ko Driver Licenses Daga Nan Zasu Sanar Daku Lokacin da Layinku Zai Koma Airtel Daga nan dominb Samun Wannan Garabasar ..
Idan Layin Naku Ya Koma Airtel Saiku Sa Kati Amma Fah Dole Sai Ta Bank Basa Son Ka Siya Kati Wanda akasa a dan Karamin
Littafi Suna son Kasa Katin Naka Ta Hanyar Gizo Ta Yanda Killa Numbobi Kawai Zaka Danna A Wayarka Sai Su Baka Katin Ta Hanyar Cire Kudin Ka Ta Banki Daga Nan Idan Kasa Katin #100 Zaka Sami Garabasar 2GB idan Kasa Katin #1000 Zaka Sami Garabasar 20GB Kuma Sai Yayi Kwana Talatin Kafin Ya Kare Dadin abin zaka Iya Kara yi idan Ta Kare
ALLAH YA BADA SA'A DAGA HAUSANET.ML
![](https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEhYzxCs_jxIdgLLpKZTYPRbzaBLIGT1Kyk2SeHUhDqE0LGHGnlYu9VtfeGAlWfJurYjiUPQ9m4Gt8_xncE7rt4m4lMalI7vcqWh1A5FyIhSgmewM-D9QG2QfkKfzsEjYApEOOTOJfZ1yOY/s640/Zainab-Indomie.jpg)
Zainab indomie Meyasa Rayuwar Shirin Fim Dina Ta Lalace
jarumar da aka daina yayinta,
Zainab Abdullahi da aka fi sani da Zainab Indomie ta bayyana cewa ba ta san yaya aka yi rayuwar aktin dinta ta susuce ba duk da daukakar da ta samu a masana’antar fina-
finan Hausa Jarumar ta ce ta samu daukaka tun tana karama, amma saboda kaddara ba ta san abin da ya faru ba yanzu ta rasa komai. Ta ce, “Na samu daukaka tuna ina karama,
wani abu ya faru yanzu dai na rasa komai, babu ganganci a ciki, ba na kuma ganin laifin kowa, ban kuma zargi kowa ba sakamakon mawu yacin halin da na shiga. A halin da ake ciki ba zan iya tunawa da
komai ba, ba zan iya cewa ga abin da ya sa na samu kaina a cikin
mawuyacin hali ba Idan har laifina ne ina rokon Allah Ya yafe mini, idan ma laifin wani ne to Allah Ya yafe
masa inji ta. Jarumar ta kuma roki Allah Ya sanya ta da sauran jama’a a kan hanya madaidaiciya. Ta ce, “Na gode wa Allah saboda jarrabawar
da ya yi mini, ina rokon Allah Ya fitar da ni daga wannan jarrabawar. Na mika kaina ga hannun Ubangiji Amin summa amin
![](https://2.bp.blogspot.com/-pAkyABlSI9I/V5Vb3h5bgGI/AAAAAAAAEEg/03XLR_fUHfciuaylJJCi1GxDG2Lw9WqVwCLcB/s320/couper.jpg)
SHEDAN YANA DA WATA MATA GURGUWA
MATAR SHEDAN
SHEDAN YANA DA WATA MATA GURGUWA:
Wata rana zai wuce sai yace mata ta matsa Don bata da wani amfani, sai tai dariya Tace: "Na fi ka illah don nice nake zuwa a karshen fitsari, idan mutum yana fitsari INA rike kadan daga ciki, da ya mi'ke sai in sakar masa, ya mike ba tare da ya wanke ba!"
Sai Shedan ya bushe da dariya yace "Kin ga kuwa duk Wanda bai da tsarki baida alwala, duk kuma Wanda bai da alwala bai da sallah!" Yace lallai kuwa kin cika sheidaniya!".
MAFITA:
Ya Muslim Ummah, a duk lokacin da muke fitsari bayan mun gama mu jira kadan muyi nishi, zamu ji wani fitsari kadan mai 'dumi ya biyo baya.... WANNAN shine fitsarin da Matar Shaidan take ri'kewa don ta 6ata mana ibadanmu!!
LA'ILAHA ILLALLAH, MUHAMMADUR RASULULLAH (SAW).
Don Allah in ka karanta ka aikawa wasu don suma Su amfana, mu kuma samu tsari gabadaya daga azabar Qabari.
Allah Ya tsare mu Ameeen.
FATIHA DA SALATIL FATIHI