Labarin wasu masoya ne zan baku da fatar zaku fahimce ni. Sudai wadannan masoya sun kasance
daga farkon soyayyar su,kamar ‘yan biyu ne koda yaushe suna tare,suna fadawa juna maganganun soyayya har ma da dariya,basu son abinda zai sosa ran daya.soyayya tayi karfi sosai har alkawarin aure ya shiga
tsakaninsu,saboda sun yarda da
junansu fiye da kima.To shidai yaron
dan talakawa ne.Gidansu ba masu wadata bane,amma duk da haka ta
nuna ta amince dashi,ya kamu da
kaunarta kauna mai tsanani.Ana cikin haka sai chanji ya shiga.masu kudi da manyan motoci suka fara farautarta kuma wani daga cikin
ya samu amincewarta,dan shi babban dan kasuwa ne kuma ya nada kudi.Ya aureta yakai gidansa.
Allah SWA ya arzuta ta da juna biyu
har ya kai wata ukku,sai ya fara jin ya gaji da ita,karshe dai ya sake ta saki
3 ta koma gidansu tana kokawa da
kannenta wajan cin abinci,rayuwarta ta lalace..Shi kuma tsohon saurayin nata Allah.ya bashi wadata bayan
ta auri mai kudi,shi kuma duk da yana talaka sai wani attajiri ya bashi ‘yarsa,kuma tafi ta kyau.wannan kenan,Dan Allah mu kiyaye maza da mata mu daina sanya kwadayi cikin
harkar aure dan gudun afkawa cikin
wahala.
No comments:
Write Please Share a Your Opinion.