. An kama wasu matasa 2 suna luwaɗi a makabartar jahar Kano - hausanet hausanet





Wednesday, 29 August 2018

Home › › An kama wasu matasa 2 suna luwaɗi a makabartar jahar Kano

Subscribe Our Channel


Allah ya tona asirin wasu matasa yan luwadi a jihar Kano, yayin da aka kama suna turmi da tabarya suna aikata badala a cikin wata. makabarta cikin birnin Kano kamar yadda rahotanni suka tabbatar. NAIJ.com ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a ranar Litinin data gabata na watan Agusta, inda wasu matasa a karamar hukumar Gwale suka kama yan luwadin a lokacin da suke tsaka da tafka wannan mummunan laifi Wannan lamari yayi matukar bata ma mutannen wannan unguwa rai, inda suka fusata suka yi ma yan luwadin

dukan kawo wuka, suka kusan kashesu, da kyar da sudin goshi Yansanda suka kwacesu. Kaakakin rundunar Yansandan jahar
Kano, Magaji Musa Majia ya  tabbatar da.faruwar lamarin, inda yace a yanzu haka matasan suna hannunsu, kuma.bincike ya kankama zuwa yanzu..Jama’a da dama a jihar Kano sun koka da karuwar matasa masu shiga.mummunan dabi’ar nan ta luwadi inda.namiji ke neman namiji, da madigo.inda mace ke bin mace don samun.biyan bukata, sai dai yawancin jama’an.sun danganta lamarin ga illolin shaye.shaye.