. SAKONNIN SOYAYYA - hausanet hausanet





Tuesday, 28 August 2018

Home › › SAKONNIN SOYAYYA

Subscribe Our Channel



Kin wadata zuciyata da farin-ciki,
kin haskaka rayuwata da haskenki, kulawarki a gare ni ta musamman ce, hakan ya sa
nake jin kaina tamkar sarkin wata
masarauta mafi girma da
karfin iko. Ina Son Ki


2 Ke ce kaddarar da na jima ina
tsimayin tarar da ita a
rayuwata, zan kasance a duk inda
kike, zan tsaya a duk inda
kika tsayar da ni. Ina son ki, adadin
son da kalmomi ba zasu
iya siffantawa ba


3 Ina jin labarin soyayya ne a da,
tamkar tatsuniya, amma a
yanzu bayan na haɗu da ke, na
gaskata soyayya wata aba ce
wadda ke da tasirin sanya farin-ciki a
cikin zuciya. Ina fatan
zaki kasance tare da ni, domin zama
maganin damuwata na
tsawon rayuwa? Ina Son Ki


4 Koda a ce zaki sa wuta a jikina na
babbake na zama toka,
ba zan damu ba, matukar zaki ɗauke
ni, ki kasance tare da ni
a duk inda kike. Fatana mu kasance
tare da juna a cikin wuya
ko daɗi. Ina Son Ki


5 Son da nake yi miki, tamkar ruwan
lemo ne da ke rufe a
cikin kwalba, irin wanda babu irin sa
ko makamancin sa a faɗin
wannan duniyar. Ina fatan zaki karɓa
domin jin irin ɗanɗanon
da ke kunshe a cikinsa? Ina son ki.
6 Ina fatan Allah Ya bar mu tare, cikin
aminci da kaunar juna


7 Tun ranar da na fara ganin ki, na ji
a jikina, watarana
hannuwanki zasu zamo masharin
hawayena, kuma zasu
kasance rike da ni na tsawon rayuwa,
zuciyarki zata zamo
makwancina na har abada. Na gode da
irin kulawar da kike
nuna min a kullum. Ina Son Ki Sosai


8 Kin zamo cikin baitukan wakar da
zuciyata ke rerawa a
kullum, waɗanda a dukkan lokacin da
na ji su, na kan ji dukkan
damuwata na gushewa. Tabbas ina jin
na kamu da son ki
ne kai babu ko shakka matsanancin
son ki ya shiga
zuciyata. Ina son ki ina kuma fatan
zaki amince da ni a
matsayin masoyi na hakika?


9 So tamkar wutar murhu ne da ke ci
a cikin zuciyar masoya.
Tini zuciyata ta babbake da son ki
abar tinanina. Ina son ki, so
mara misaltuwa


10 Ba zan taɓa mantawa da wannan
ranar ba, wadda dare ya
yi na kasa bacci a cikinta, saboda
tsabar tinaninki, wato ranar
da na fara ganin ki. Na Yi Kewar Ki.
11 Idan har ba kya jin irin yadda nake
ji a kan ki a yanzu, to
tabbas na san zaki ji irin hakan bayan
na mace


12 Babu wani sinadari da zai iya
mayar da zuciya, ya haɗe ta
guri guda, ta dawo da aiki kamar
yadda take a da, bayan ta
fashe ta targwatse. A saboda haka
nake rokon, da ki kasance
cikin ba wa zuciyata tsaro, karda ta yi
fashewar da za a rasa ni
gabaɗaya. Ina Son Ki


13} Ke kaɗai ce nake gani kullum a
cikin baccina, ke ce abar
begena kuma ke ce wadda nake so,
domin a gurin ki nake
tsammanin samun farin-cikin da nake
fata. Ina Son Ki


14 A wasu lokuta so yana zama wani
abu mara tausayi ga duk
wanda ya raɓe shi, ya raba mutum da
duk abun da yake da shi
na farin-cikin rayuwa, amma ni na yi
sa'a kuma na tsallake wa
sharrinsa tunda na same ki


15 A dukkan lokacin da tinaninki ya
bujuro a cikin zuciyata, na
kan tina irin yadda son ki ya zamo
abu mai matukar
muhimmanci a rayuwata. Ke ce wadda
nake so, kuma nake
fatan na rayu tare da ita, rayuwa ta
har abada


16 Za ki fahimci ma'anar soyayya, da
kuma irin muhimmancin
girman son da nake nuna miki, a
lokacin da aka ce na mutu ba
na raye. Har Yanzu Ni Dai Ina Son Ki


17 A kullum zuciyata kan nutsu ta yi
tinani, domin tsara sakon
da zan aikewa da abar tinanina a dare
ko rana, domin ganin
yalwatuwar murmushi a saman
fuskarta. Ina fatan sakonnin
nawa suna yin tasirin sanya ki farin-
ciki? Ina Son Ki


18} dukkan lokacin da masoyi ya rabu
da abar kaunarsa, ya
kan tsinci kan sa cikin kaɗaici da
damuwa na tsawon lokaci,
ya kan tsinci kan sa cikin rashin
yarda da gujewa amincewa
sauran mata. Ki kasance tare da ni na
tsawon rayuwa, karda ki
bari zuciyata ta ɗanɗani raɗaɗin
zafin rabuwa da abar so. Ina
Son Ki


19 So shi ne abu mafi tasirin warkar
da kowane irin ciwo a
cikin zuciya, kuma shi ke sanya mu jin
kanmu a matsayin wasu
mutane na musamman, a dukkan
lokacin da muke tare. Na Yi
Kewar Ki


20 Shigowar ki cikin rayuwata, gami
da irin tsantsar son da
kike nuna min, sun zama dalilan yin
murmushina a kowane
lokaci. Ba ni da wata da nake so sama
da ke. Ke ce karfina, ke
ce karsashina. Ina Son Ki


NA MATA


1 Kowace soyayya da kake gani, tana
samuwa ne a bisa wasu
dalilai, saboda haka, ina son bayyana
maka cewa, ina son ka
ne saboda, kai ne da ma wanda
zuciyata ta daɗe tana jira. Ina
tare da kai a duk inda na shiga. Ina
Son Ka


2 Matsayinka a gare ni, tamkar na
wani dutse ne na
musamman da yake jikin wani zobe,
wanda ya kasance a
dukkan lokacin da babu shi, zoben zai
zamo mummuna mara
daraja abar nunawa. Ka kasance tare
da ni masoyina. Ina son
ka, so mara misaltuwa


3 A lokacin da ka shigo cikin
rayuwata, na ji tsoron kar ka
raunata zuciyata, amma yanzu da na
same ka, ina jin fargabar
rasa ka. Ina fatan zuwan ranar da zan
zamo mata a gare ka.
Ina Son Ka

4 Ina son kasancewa ne tare da wanda
zai kasance cikin saka
ni farin-ciki, ya sa ni murmushi a
lokacin da nake cikin
damuwa, wanda zai kasance cikin so
na a kowane irin yanayi.
Na san babu wanda zai iya hakan sai
kai, a saboda haka nake
kara bayyana maka cewa, ina son ka


5 Ina fatan zuciyata da taka su narke
su zama abu guda, har
zuwa karshen rayuwa. Zan kasance
cikin yi maka addu'ar
samun nasara a dukkan al'amuranka,
kuma zan kasance cikin
son ka har karshen rayuwata


6 Kai ne ke bayyana kullum a cikin
baccina, ta cikin mafarkin
da nake fatan ya zamo gaskiya
watarana. Ina son ka, irin son
da ke kawar da zuciya daga yin
tinanin kowa face naka


7 Na yi kewar ka sosai. Na kan yi
tinanin lokacin da muke
shafewa tare, mu yi raha tare da
farin-ciki a cikinsa. Wannan
tini ne na abun da ya faru tsakanina
da kai a dangane da
soyayyarmu, ko zai sa ka tino da ni.
Na yi rashin ka a kusa da
ni

8}Zan so mu kasance tare a matsayin
miji da mata, ka
tarairaye ni ka nuna min irin yadda
kake ji na a cikin zuciyarka
a zahiri. Ni wannan shi ne kaɗai abun
da nake muradi. Ina Son
Ka

9 Idan har da a ce wasu zasu tambaye
ni wanda nake fatan
na aura, amsar ba zata wuce kai ba,
domin kai ne wanda
zuciya ke fatan ta kasance tare da shi
har abada.

10 Wanda nake fatan na aura, mutum
ne na musamman mai
baiwa ta musamman a cikin
dubunnan samari, shi ne wanda
zan iya kasancewa tare da shi a cikin
wuya ko daɗi, domin na
san tinaninsa a kullum, bai wuce
neman hanyar da zai inganta
rayuwata ba. Ina Son Ka.
LURA


A kiyaye hakkin mallaka, a guje wa
satar fasaha.
Kana da damar tura wa abokiyar
tsinkar furenka,
amma ba a amince wani ya yi amfani
da shi da
niyyar yaudarar wata ruhi ba. Akwai
Mai ganin ka/ki a ko'ina