. Za'a tantance gwarzon UEFA tsakanin Ronaldo Salah, da Modric - hausanet hausanet





Tuesday, 28 August 2018

Home Za'a tantance gwarzon UEFA tsakanin Ronaldo Salah, da Modric

Subscribe Our Channel


Yan wasan sun hada da Luka Modrić, Cristiano Ronaldo da kuma Muhammad Salah.bA ranar 30 ga watan Agusta da muke cikivhukumar ta UEFA za ta bayyana wanda zai
lashe kyautar ta gwarzon dan wasan kwallon kafar a nahiya Turai. A ranar 31 ga watan Agustan ne kuma

hukumar ta UEFA za ta bayyana gwarzon dan wasanta na nahiyar turai a bangaren gasar Europa a kakarwasan da ta gabata

Taron karrama ‘yan wasan dai zai gudana ne a birin Monaco da ke kasar Faransa. Sauran ‘yan wasa 10 da hukukmar UEFA ta zabo da fari sun hada da, Antione Griezman na
kungiyar Atletico Madrid Lionel Messi na Barcelona, Kylian Mbappe na PSG da Kevin De Bruyne na Manchester City.v‘Yan wasan da ke a matsayi na 8, 9 da kuma 10bsun hada da Raphael Varane na Real Madrid, Eden Hazard na Chelsea da kuma Sergio Ramos

Sharuddan da hukumar da UEFA ke yin amfani da su wajen zabar gwarzon dan wasanta dai sun hada da bajintar da ya nuna a baki dayan
wasannin da ya fafata a matakin kasarsa nahiya da kuma matakin kasa da kasa