. Yadda za a rufe kasuwar ' yan wasa ta Turai - hausanet hausanet





Friday, 31 August 2018

Home Yadda za a rufe kasuwar ' yan wasa ta Turai

Subscribe Our Channel


An saye Sahin daga Borussia

Werder Bremen ta kammala sayen Nuri Sahin daga Borussia Dortmund.
Zai saka riga lamba 17 a kulob din na Jamus.

Hull City ta sayi dan wasan bayan Villa

Hull City ta sayi dan wasan bayan Aston Villa Tommy Elphick, mai shekara 30,domin ya buga
mata wasan aro na kaka daya

Nariano ya maye Ronaldo

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta bayyana dan wasanta Mariano Diaz a matsayin wanda zai cigaba da saka rigar Cristiano Ronaldo,mai lamba
bakwai.

Ina cikin wadanda suka fi iya aiki —Mourinho

Kocin Manchester United Jose Mourinho ya ce ko bai ci gasar Firimiya ba, zai kasance daya
daga cikin wadanda suka fi iya aikin horas da 'yan wasa. Mourinho ya ce shi kadai ne kocin da ya ci kofi
takwas a Italiya da Sifaniya da Ingila.

Ronaldo zai sayi kulob din La Liga

Tsohon dan wasan gaban Brazil Ronaldo zai sayi kulob din La Liga Real Valladolid ranar Litinin,
In
ji, AS.

Mourinho: Na ji dadin yadda masoya Man U
suka yi mini

Kocin Manchester United. Jose Mourinho ya ce shi ya ji matukar dadin yadda masoya kulob din
suka yi bayan kulob din ya sha kaye a Old Trafford ta hannun Tottenham.
A jawabin da ya yi wa manema labarai dazu, Mourinho ya ce masoyan Man U din sun nuna wa
kulob din goyon bayan duk da cewa ya sha kaye a gida

.Tsakanin Mo Salah ne da hukumar kwallon kafa
ta Masar

Kocin Liverpool Jurgen Klopp ya yi tsokaci kan matsalar Mo Salah da hukumar kwallon kafa ta
Masar: "Game da lamarin hukumar kwallon kafa ta Masar ba zan iya magana da yawa ba, abu ne
tsakanin dan wasan da hukumar kwallon kafar. Na yi magana da Mo game da shi. Ba mu da
hurumin tsoma baki a lamarin. Za su warware matsalar, na yi imanin hakan"

Liverpool za ta dauki koci kan 'throw-ing'

Kocin Liverpool Jurgen Klopp yana magana game da daukar kwararre kan wurga kwallo (wato throw-ing),Thomas Gronnemark. Klopp ya ce Gronnemark ne ya fi iya wurga
kwallo a wasan kwallon kafa. Ya kuke ganin wannan matakin da kocin Liverpool ke son daukawa?

Da wa Chelsea za ta fafata a gasar Europa?

Arsenal tana rukuni na E tare da Sporting Lisbon (ta Portugal) da Qarabag (Azebeijan) da kuma
Vorskla (ta Ukraine) Chelsea tana rukuni na L tare da PAOK (ta
Girka) da kuma Borisov (ta Belarus) da kuma Vidi (ta Hungary) Celtic tana cikin rukuni na B tare da Salzburg (ta Australiya) da Leipzig (ta Jamus) da kuma Rosenborg (ta Norway)

Ina Luka Modric ke son zuwa?

Dan wasan tsakiyar Croatia Luka Modric, mai aashekara 32, ya ce yana son cigaba da zama a
Real Madrid "na tsawon shekaru masu yawa nan
gaba ," yayin da shugaban kulob din, Florentino
Perez, ya ce Inter Milan ta so "ta ki biyan
komai" a zawarcin da ta yi wa dan wasan a
lokacin bazara, in ji Football Italia .
12:33

A wane rukuni Arsenal za ta buga a gasar
Europa?

FC Salzburg za ta kasance a rukunin B. Ita kuwa
Zenit St Petersburg za ta taka leda ne a rukunin
C. Anderlecht tana rukunin D yayin da Arsenal ke
ruykunin E. Olympiakos tana rukunin F. Ita kuwa
Villarreal tana G. An ambato Lazio a rukunin
H.An saka Besiktas a a rukunin I. Sevilla kuma
za ta shiga J. Dynamo Kiev za ta fafata a
rukunin K.
12:28

Ana fitar da jadawalin gasar Europa
Yanzu haka an fara fitar da jadawalin gasar
Europa. Bayer Leverkusen za ta kasance a
rukuni na A.
12:08
PSG na son kammala sayen dan Kamaru
Zakarar gasar Faransa Paris St-Germain tana
fatan ganin ta kammala yarjejeniyar sayen dan
wasan gaban Stoke City da Kamaru mai shekara
29, Maxim Choupo-Moting, in ji Mail.
12:03

Wane dan wasa ne zai bar Liverpool a yau?
Ta yiwu Lazar Markovic zai kasance dan wasa
daya tilo da zai bar Liverpool a yau, kamar yadda
Liverpool Echo ta ruwaito.
Jaridar ta ce dan kasar Serbiya din mai shekara
24 yana da zabi tsakanin kungiyar PAOK ta Girka
da kuma kungiyar Anderlecht ta Belgium.
Dan wasan gefen ya koma Anfield ne a lokacin
zafi na shekarar 2014, kan kudi fan miliyan 20
amma bai buga wa Reds wasa ba tun shekarar
2015, inda yi ta buga wasan aro cikin yawancin
shekaru ukun da suka gabata.
11:53

Chelsea ta ki sayen dan wasan Lyon
Chelsea ta yi watsi da damar sayen dan wasan
tsakiyar Lyon da Faransa Nabil Fekir, mai
shekara 25, a lokacin zafi, kamar yadda
shugaban kungiyar kwallon kafar ta Faransa
Jean-Michel Aulas ya fada. Liverpool dai tana
hakon Fekir, kamar yadda Mail ta ruwaito
11:46

Everton na da kwarin gwiwar rike Lookman

Everton tana da kwarin gwiwar cigaba da rike
Ademola Lookman, duk da cewar RB Leipzig,
wadda ta yarda ta biya fan miliyan 25, kan dan
wasan mai shekara 20, tana son dan wasa, in ji
Liverpool Echo

Assalamu alaikum
Jama'a barkanku da zuwa wannan shafin da za
mu kawo muku labarai game da yadda za a rufe
kasuwar musayar 'yan wasa ta Turai