. Modric ya lashe kyautar gwarzon dan wasan Turai - hausanet hausanet





Thursday, 30 August 2018

Home Modric ya lashe kyautar gwarzon dan wasan Turai

Subscribe Our Channel


Hukumar kwallon kafar Turai UEFA ta mika kyautar gwarzon dan wasan shekara na nahiyar ga Luka Modric dan wasan kasar Crotia da ke

taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid yau a Monaco bayan rawar da ya taka a kakar wasan da ta gabata. Bayan karbar lambar yabon Modric, ya yaba da irin dawainiyar da ya ce mahaifinsa ya yi masa

wanda shi ne ya jajirce tare da bashi kwarin gwiwar ganin ya kai matsayin da ya ke yanzu. Modric wanda ya tallafawa Club dinsa wajen
lashe kofin zakarun Turai karo na 3 a jere ya

kuma yi rawar gani a gasar cin kofin duniya inda ya kusa kai kasar ta sag a nasarar lashe kofin duniya kafin faransa ta yi waje da su.

Modric mai shekaru 32 ya ce ya yi matukar alfahari da lambar yabon tare da mika godiya ga
ilahirin wadanda suka horar da shi tamaula a gida da kuma a bangaren kungiyoyi. Luka wanda ya faro

kwallonshi da Club din Dinamo Zagreb kafin kulla kwantiragin shekaru 4 da Tottenham daga bisani kuma Real Madrid
ta saye shi kusan shekaru 6 da suka gabata