Hukumar kwallon kafar Turai UEFA ta fitar da jadawalin kungiyoyi 32 da za su fafata a gasar lashe kofin zakarun Turai, inda ta rarraba su
zuwa rukuni 8
Rukunin farko na jadawalin, wato rukuni A ya kunshi kungiyoyi irinsu
Atletico Madrid da Dortmund da Monaco da Club Brugge.
Sai kuma rukunin B da ya kunshi Barcelona da TOTTENHAM da PSV da kuma Inter Milan
Akwai kuma rukunin C da ya kunshi PSG da Napoli da LIVERPOOL da kuma Red Star Belgrade.
Yayinda rukunin D ya kunshi kungiyoyi irinsu Lokomotiv Moscow da Porto da Schalke da kuma Galatasararay
Akwai kuma rukunin E daya kunshi Bayern Munich da Benfica da Ajax da kuma AEK Athens
Ka zalika rukunin F ya kunshi kungiyoyi irinsu MAN CITY da Shakhtar da Lyon da kuma Hoffenheim
Rukunin G kuma akwai mai rike da kambu Real Madrid da Roma da CSKA Moscow da Viktoria Plzen
Yayinda rukunin H kuma ya kunshi Juventus da MAN UTD da Valencia da kuma Young Boys.
No comments:
Write Please Share a Your Opinion.