An zabi kwallon Ronaldo a matsayin wanda ta fi kyau a bana A bana ne Cristiano Ronaldo ya ci Juventus wata kwallo da ta ba jama’a mamaki inda yayi tsalle ya watse ta baya har cikin ragar Gianluigi Buffon. Wannan kwallo aka zaba a matsayin
wanda ta fi kowace kwallo kyau a 2018..Sama da mutane 200, 000 cikin mutane.346, 915 da su ka shiga shafin UEFA su ka zabi kwallon da tsohon ‘Dan wasan Real Madrid Ronaldo a Turai. A bara ma dai ‘Dan wasan Juventus Mario Mandžukić ne ya lashe kyautar
Karin bayani
Ronaldo ya ci Juventus a Gasar Zakarun Nahiyar ne lokacin yana bugawa Real Madrid. Kwallon ‘Dan wasan Marseille Dimitri Payet ce ta zo na biyu yayin da kwallon da Eva Navarro ta ci a wasan Sifen da Kasar Jamus ta zo 3. Kwanan nan kun ji
cewa Gwarzon ‘Dan wasan Duniya Cristiano Ronaldo ya bayyana cewa tafin da Magoya bayan Juventus su ka yi masa a lokacin da ya zura kwallo a ragar su ce ta sa ya koma taka leda a Kungiyar a shekarar nan
No comments:
Write Please Share a Your Opinion.