Sunday, 27 January 2019
Fati washa __Nagode maka da sani farin ciki---Fati Washa tagayawa masoyinta
Nagode maka da sani farin CikiFati Washa tagayawa masoyinta
- Tauraruwar fina-finan Hausa da turanci, Rahama Sadau ta godewa masoyinta inda tace, Masoyi na musamman, nagode da shigowa rayuwata, Nagode da sani farin ciki Da ka yi WWW.HAUSANET.ML
Aisha Buhari ta karyata masu cewa ta yi Allah-wadai da korar ----- Onnoghen
war gidan shugaban kasa, Aisha Buhari ta karya rahotannin da ake Yadawa na cewar ta yi Allah-wadai da Hukuncin da shugaban kasa Buhari ya Dauka na korar mai shari'a Walter Onnoghen daka mukamin Alkalin Alkalai na kasa (CJN) Mrs Buhari a cikin wata sanarwa ta Hannun Daraktanta na watsa labarai, Mr Suleiman Haruna da ya rabawa
manema labarai a ranar Asabar aBAbuja, ta bayyana wannan labarin da Ake yadawa na cewa ta yi Allah-wadai da korar Onnoghen a matsayin 'labarin kanzon kurege an ankarar da uwar gidan shugaban kasa kan wani labari da ake yadawa a Kafofin sada zumunta na zamani wanda Har ake cewa ta yi Allah-wadai da Dakatarwar da aka yiwa Walter Onnoghen, daga mukamin Alkalin Alkalai na kasa
Rundunar sojin Najeriya ta fara kera motocin yaki (Hotuna
Rundunar sojin Najeriya a karkashin jagorancin Safsan ta, Laftanal Janar Tukur Yusuf Buratai sun soma kera motocin sulke da na yaki manya da kanana domin fuskantar abokan gaba da sauran masu Tada kayar baya a kamfanin su dake a Jihar Kaduna
Friday, 25 January 2019
Manchester City zata iya lashe kofuna 4 a wannan kaka inji Guardiola
Kocin kungiyar kwallon kafa ta Manchester City Pep Guardiola ya ce abin alfahari ne ya zamana Club din ya yi nasarar lashe kofuna har 4 cikin kaka guda dai dai lokacin da ya ke shirin Komawa wasannin cin kofin FA bayan
takaitaccen hutu. City dai ita ce kungiya daya tilo da ta ke da zarafin iya lashe kofunan Firimiya da FA da kofin League da kuma zakarun Turai la’akari da
matakin da ta ke a kowacce gasa.
Yanzu haka dai City na da tazarar maki 4 ne
kacal tsakaninta da Liverpool da ke saman
Teburi, a bangare guda kuma an ga rawar da ta
ke takawa a gasar ta FA da ma yadda ta ke
shirin tunkarar wasan karshe a gasar League
tsakaninta da Chelsea cikin watan Fabarairu
baya ga gasar zakarun Turai. A gobe asabar ne Manchester City za ta kara da Burnley a zagaye na 4 na wasannin cin
kofin FA
ka Karanta Abinda Shi'a Babban Darakta Falalu Dorayi Akan Bashar Chiroki
Allah shi yake kaddarawa bawa samu da rashi, wanda Allah ya nufe shi da zama cikin kunci ko rashin wadatar abubuwa da saba rayuwa dasu, ba
kaskanci ba ne face jarraba da kuma
kaddarar Allah akansa.
Mai hankali yasan duniya bala'ice gida
ne na jarrabawa tsakanin wadata da
tsanani.
Ubangiji Yace;
“Kuma za mu jarraba ku da sharri da
alheri a matsayin fitina, kuma gare Mu
kuke komawa.'' (Anbiya:35). Bai
kamata ga mutum idan ya tsinci kansa
a cikin Jarrabawa ta kunci ko talauci
ko dusashewar daukaka ko ciwo ya
zargi wasu mutane ba. Allah yana
jarabtar bawa Sakamakon abin da ya
aikata ga ‘Yan uwansa mutane na
Alfahari, Dagawa da Girman kai. To
shin Ina ma matsayin takawakkali da
yadda kaddara?
Tawakkali ga Allah shine abin bukata
daga ko wane mutum,
a ko wanne hali ya tsinci kansa.
Cikakken tawakkali shin zuciya ta
nutsu ta mika komai ga Allah ta haka
za’a samu alkairi da kariyar daga
sharri.
Babu wanda ya isa ya baka daukaka ko
ya kwaceta sai Allah in dai ka dagara
ga Allah hakikani dogaro, Allah zai
azurtaka kamar yadda yake azurta
tsuntsu da sauran dabbobi.
In gaske ne mutum ya fawwala
lamuransa ga Allah, ya yadda da Allah
shi yake bada daukaka da daukewarta to sai a nisanci Kage, zargi, camfi, da
tazarta masana’antar da Allah ya baka Suna a cikin ta kai aure kai gida kasai
babur. Lallai in da kake yanzu haka
Allah ya so ya ganka
Ubangiji Yace; cikin Qurani
“Kuma Idan Allah ya shafe ka da wata Cuta, babu mai yaye ta, sai shi, idan kuma ya shafe ka da wani alheri, babu mai iya ture falalarsa. Yana samun wanda ya so daga cikin bayinsa da ita,
kuma shi mai gafara ne, mai jin kai
Portugal za ta kwace lambar yabo mafi girma da ta baiwa Ronaldo
Shugaban Portugal Marcelo Rebelo de Sousa,
ya ce gwamnatinsa tana nazari kan yiwuwar
kwace babbar lambar yabo da ta baiwa dan
wasan kasar Cristiano Ronaldo.
Matakin a cewar shugaba Rebelo de Sousa, na
da nasaba da hukuncin biyan tara da kotun
Spain ta yanke kan Ronaldo, bayan samunsa da
laifin kin biyan haraji, yayin da yake wasa a
kungiyar Real Madrid.
A shekarar 2016 Portugal ta karrama Ronaldo
da lambar yabo mafi girma da ake baiwa farar
hula ta ‘Portuguese Order of Merit’ a turance,
bayan taimakawa kasar da ya yi, wajen lashe
gasar cin kofin kasashen nahiyar Turai.
Sai dai a ranar Talatar da ta gabata, wata kotun
Spain ta yanke hukuncin tilasatawa Cristiano
Ronaldo biyan Dala miliyan 3 da dubu 57 saboda
kin biyan makudan kudade na haraji ga
gwamnatin kasar.
Da fari hukuncin kan Ronoldo na daurin
shekaru 2 biyu ne a gidan Yari amma aka
sassauta hukuncin zuwa biyan tarar euro dubu
365 na take, tare da biyan karin euro miliyan 3
da dubu 200
Amaechi ya saka ni a matsala - Buhari
A yau, Alhamis ne shugaba
Muhammadu Buhari ya ce MInistan
Sufuri, Rotimi Amaechi ya jefa shi a
cikin matsala yayin da ya yi alkawarin
gina layin dogo da za ta hade yankin
Kudu maso Gabashin kasar da Arewa.
Shugaba Buhari ya yi wannan jawabin
ne a wurin taron kaddamar da yakin
neman zabensa da akayi a cikin filin
motsa jiki na Nnamdi Azikwe da ke
garin Enugu.
Buhari ya ce abu ne mai wahala
gamsar da majalisar zartarwa na kasa
su amince da ayyukan layin dogo amma
ya ce zai yi iya kokarinsa domin ganin
'yan majalisar sun fahimci
muhimmancin gudanar da aikin.
"Amaechi ya yi muku alkawari amma
ban san yadda zan cika alkawarin ba.
Amma zanyi iya kokari na domin ganin
'yan majalisar zartarwa sun amince da
gudanar da aikin," inji Buhari.
Ya ce ba a gabatar wa Majalisar
Zartarwa alkawarin da Amaechi ya yi
ba inda ya ce zai fi dacewa a bari
Majalisar su amince da aikin kafin a
bayyana wa mutane.
Shugaban kasar ya mika godiyarsa ga
mutanen yankin bisa yadda suka fito
kwansu da kwarkwata su tarbe shi
kuma ya shawarci su kasance masu
kishin Najeriya domin ba su da wata
kasar bayan ita.
Ya kara da cewa, " ya zama dole
dukkanmu mu hannu hannu wurin
guda domin ciyar da kasar mu gaba
saboda ba mu da wata kasar bayan
wannan."
A baya, Ameachi ya shaidawa 'yan
jam'iyyar da magoya bayansu cewar za
a farfado da layin dogo na yankin
kudu.
Ya ce babban aikin da za muyi shine,
"zamu amince da shimfida layin dogo
daga Fatakwal zuwa Maiduguri wanda
zai wuce Fatakwal zuwa Onitsa har
zuwa Awka.
"Na biyun kuma zai bi ta Fatakwal,
Umuahia, Enugu, Makurdi da Jos."
Amaechi ya ce, "sauya tsarin rabon
arzikin kasa zai yiwu ne idan aka sake
zaben shugaba Muhammadu Buhari
saboda dan kabilar Ibo ya zama
shugaban kasa bayan Buhari ya
kammala wa'adinsa
Thursday, 24 January 2019
Kun San Abin Da Buhari Ya Fadawa Sakkwatawa?
Tawagar yakin neman zaben shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ta isa jihar Sakkwato da ke arewa maso yammacin
kasar a yau Laraba, a ci gaba da neman
kuri’u da shugaban yake yi na neman
wa’adi na biyu.
Ga kadan daga cikin abin da ya fadawa
al’umar jihar Sakkwato kamar yadda
wakilinmu Muratala Faruk Sanyinna ya
aiko mana da rahoto:
Boko Haram: “Cikin ikon Allah, ku ne
shaidu, mun yi iyakar kokarinmu,
kuma a jiya, mutanen Borno sun
tabbata mun ci karfin Boko Haram.
Noma: “Batun arzikin kasa da wadata,
Allah ya taimake mu, damunoni biyu
da suka wuce, sun yi albarka.”
Cin Hanci Da Rashawa: “Batun cin hanci
da rashawa, wannan gwamnatin tana
kokari akan ka’idodin da aka kafa. Na
yi muku alkawarin, ni ba zan ci
amanarku ba, ba kuma zan ga ana cin
amanarku ba in kyale.” Yayin nasa jawabin, Ministan sufuri kuma shugaban gangamin yakin
neman zaben shugaba Buhari, Rotimi Amaechi, ya sha alwashin za a gina layin dogo da zai hade yankunan jihohin Sakkwato, Kebbi da Zamfara.
Akwai dadi aLadidi abdullahi 'Tubeless' ta yi kira ga maza su rika auren 'yan fim
Daya daga cikin fitattun jaruman nan na
masana'antar shirya fina-finan Hausa na
Kannywood mai fitowa a matsayin uwa
wadda Ladidi Abdullahi amma wadda aka
fi sani da Ladidi Tube less ta yi ikirarin
cewa duk duniya babbu mace mai dadin
aure kamar 'yar fim.
Ladidi ta kara da cewa ita 'yar fim
saboda irin yadda take taka rawa a
cikin fina-finai, tana kara ilimin
zamantakewa irin ta aure sosai a don haka ne ma take kira ga maza su rika
auren 'yan fim din
Na Samu Komai Sauran Abu Daya Amina Amal Umar
1. Amal Umar
-Na Samu Komai Sauran Abu Daya.
2. Shirin fim a 2018: Da dadi, ba dadi!
3.Burin Hairat Abdullahi Zabiya mai
muryar zinari.
4.Karairayin Aliyu Ibrahim Kankara kan
tarihin Shata.
5.2019: ‘Yan takarar da ‘yan fim su ke
so
6.Marin Adam A. Zango saboda gulma!
7.Matsalolin auren ‘yan fim, daga
Zakiyya Ibrahim.
8.Sai yaushe Sadiq Zazzabi zai yi aure?
9. Yaushe Nafisa Abdullahi ta soma
Bilicin?
Wednesday, 23 January 2019
Sabon photon Maryam yahya Wanda babu dan kwali akanta abindai sai Wanda yagani
Sabon photon Maryam yahya Wanda
babu dan kwali akanta abindai sai Wanda
yagani wow kai wlh kinyi matukar kyau
Ko a dajin Sambisa za'a ajiye akwatin zabe zamu je mu sakawa Buhari kuri'a Inji wani dan jihar Yobe
Wannan wani hoton masoyan shugaban kasa,
Muhammadu Buharine a jihar Yobe inda yaje
yakin neman zabe, jiya, hoton ya dauki hankula
saboda irin sakonnin da mutanen ke dauke dashi
a kan kwalayen da suke rike dasu.
Daya daga cikin kwalayen yace, na yadda da
Buhari fiye da yadda na yarda da kaina.
Dayan kuwa yace, mu 'yan jihar Yobe dole mu
sake zabenka a karo na biyu ko da kuwa a dajin
Sambisa za'a ajiye akwatin zaben
Tuesday, 22 January 2019
Ko a dajin Sambisa za'a ajiye akwatin zabe zamu je mu sakawa Buhari kuri'a Inji wani dan jihar Yobe
Wannan wani hoton masoyan shugaban kasa,
Muhammadu Buharine a jihar Yobe inda yaje
yakin neman zabe, jiya, hoton ya dauki hankula
saboda irin sakonnin da mutanen ke dauke dashi
a kan kwalayen da suke rike dasu.
Daya daga cikin kwalayen yace, na yadda da
Buhari fiye da yadda na yarda da kaina.
Dayan kuwa yace, mu 'yan jihar Yobe dole mu
sake zabenka a karo na biyu ko da kuwa a dajin
Sambisa za'a ajiye akwatin zaben
Kalli Chiroki lokacin da yake karbar tallafin Naira dubu dari biyu da tamanin 280 da aka bashi
Tauraron fina-finan Hausa, Bashir Bala Chiroki
kenan a wannan hoton yayin da ya karbi
gudummuwar Naira dubu 215 da aka tara mai ta
hanyar shafin NorthernHibiscus dake dandalin
Instagram.
Labarin halin da Chiroki yake ciki ya watsune
bayan da aka yi hira dashi a gidan talabijin na
Arewa24 inda yace yanzu sana'ar saida kunu
yake sanadiyyar watsi dashi da masana'antar
fina-finan Hausa tayi.
Tauraro Ali Nuhu dai ya musanta wannan ikirari
na Chiroki inda yace har yanzu ana yi dashi
sannan kuma irin talaucin da ake tunanin
Chirokin ya shiga a zahiri ba haka bane
wata masoyiyar buhari Ta fashe da kuka bayan da taga shugaba Buhari
Wannan wata baiwar Allah ce, da ta fashe da
kuka yayin da ta yi arba da shugaban kasa,
Muhammadu Buhari a gurin yakin neman zabe
da ya je yi a jihar Borno.
Atiku ba Bafulatani bane Miyetti Allah ta bayyana daga inda tsohon mataimakin shugaban kasar ya fito
Miyyeti Allah tace Atiku na amfani da
matsalar yan Fulani wajen yin kamfen
dinsa
- Kungiyar tace tsohon shugaban kasa ba
Bafulatani bane
- An tattaro cewa Atiku yace Buhari ba
Bafulatani bane
Kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore
Fulani ta bayyana cewa dan takarar
shugaban kasa na jam’iyyar Peoples
Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar
ba Bafulatani bane.
Jaridar Punch ta rahoto cewa Saleh
Alhassan wanda ya kasance babban
sakataren kungiyar na kasa na martani
ne ga ikirarin Atiku na cewa shugaban
kasa Muhammadu Buhari ba Bafulatani
usuli bane.
A wani gangami a igawa, an tattaro
inda Atiku yace: “Bafulatanin usuli ba
zai efa dan uwansa a cikin kangin
talauci ba kamar yadda yake faruwa a
yanzu a karkashin gwamnatin All
Progressives Congress."
Atiku ba Bafulatani bane – Miyetti Allah ta
bayyana daga inda tsohon mataimakin shugaban
kasar ya fito
Alhassan yace don Atiku na yaren
Fulatanci ba yana nufin shi Bafulatani
bane.
Yace: "Batun gaskiya shine, a wurare da
dama a jihar Adamawa, suna yaren
Fulatanci. Don Atiku ya iya Fulatanci ba
yana nufin shi Bafulatani bane.
"Idan ka kalli kirar Atiku, baya dauke da
siffar Bafulatani. Kana kallon Atiku ka
ga dan kabilar Bantu. Ba dan kabilar
Sudan bane.
Monday, 21 January 2019
Mutane ashirin da shida 26 sun mallaki dukiyar rabin al'ummar duniya
Wani rahoton Kungiyar Agaji ta Oxfam ya
bayyana cewa, mutane 26 da ke kan gaba
wajen yawan arziki, sun mallaki
kwatankwacin kadarorin rabin al'ummar
duniya. Oxfam ta bukaci gwamnatocin
kasashe da su tsauwala haraji kan
mawadatan domin rage ratar da ke tsakaninsu
da talakawa.
Sabon rahoton da aka wallafa gabanin taron
tattalin arziki na Davos, ya bayyana cewa,
attajiran da suka mallaki biliyoyin kudi a duniya,
sun samu habbakar duniya da akalla Dala biliyan
2.5 a kowacce rana a shekarar da ta wuce.
Oxfam ta ce, shugaban Kamfanin Amazon, Jeff
Bezos da ya zarce kowa arziki, ya samu
habbakar dukiyarsa da Dala biliyan 112 a bara
kadai, yayin da kungiyar ta ce, kashi daya na
dukiyarsa, shi ne ya yi daidai da kasasfin kudin
kiwon lafiyar kasar Habasha mai yawan al’umma
miliyan 105.
A gefe guda kungiyar ta ce, talakawa biliyan 3.8
sun samu karayar tattalin arziki da akalla kashi
11 cikin shekarar bara, abin da ke nufin cewa,
wannan banbancin da ke tsakanin matalauta da
mawadata ya dada nuna gazawar hukumomi
wajen yaki da talauci a duniya.
Shugabar Oxfam, Winnie Byanyima ta ce,
talakawan duniya sun fusata saboda yadda
matsalar tattalin arzikin ta dabaibaye su.
Kungiyar ta zargi gwamnaton kasashen duniya
da rura matsalar rashin daidaito tsakanin
talakawan da masu hali saboda gazawarsu
wajen samar da kudaden gina al’umma
Atiku Abubakar ya zabo wata jarumar fim domin ta tayashi yakin neman zaben 2019
Atiku ya nada wannan jaruma ce mukamin jami’a mai kula da matasan Nollywood gaba daya, ta yadda zata karkato masa ra’ayin
matasan Nollywood da nufin su bashi goyon baya tare da tallatashi, har sai ya
kai ga nasara a zaben shugaban kasa
Regina
Jarumar mai shekaru goma sha takwas
a rayuwa ce ta sanar da wannan cigaba da ta samu a shafinta na kafar
sadarwar zamani ta Instagram, inda tace tana goyon bayan Atiku dari bisa dari, kuma zata bada duk gudunmuwar data dace don ganin ya samu nasara. “Sunana Regina Daniels, ina alfahari da kasancewata yar Atiku dari bisa dari, na amince da mukamin daya nadani na mai
kula da matasan Nollywood, zan yi aiki tukuru saboda Atiku mutum ne mutunta matasa, kuma yayi alkawarin zai baiwa matasa mukamin ministoci a gwamnatinsa Najeriya na cikin mawuyacin hali, jama’a na fama da yunwa, lokaci yayi da zamu karkatar da akalar kasar zuwa tudun mun tsira, tun daga Bama har zuwa Bori, Aba zuwa Abuja, Kaura Namoda zuwa Kaduna, lokaci yayi da matasan Najeriya zasu hada kai dani wajen zaban Atiku/Obi a 2019 don kare rayuwarmu Inji ta
Regina
na daga cikin fitattun jaruman fina finan Nollywood da suka bayyana goyon bayansu ga tafiyar Atiku Abubakar a shafukan sadarwar zamani, sai dai rahotanni sun tabbatar da cewar masana’antar Kannywood da ta Nollywood ta rabu gida biyu tsakanin yan Atiku da yan Buhari
Siyasar 2019 ta dauki sabon salo Buhari ba bafulatani bane –inji Atiku
Dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ba asalin bafulatani bane tunda dai baya jin fillanci.
Atiku ya bayyana haka ne yayin
gangamin yakin neman zabensa daya
gudana a garin Dutse, babban birnin jahar Jigawa, inda yace idan ba Buhari cikakken bafulatani ne, da bai jefa mabiyansa cikin halin tsiya da talauci da yan Najeriya ke fama dashi a gwamnatinsa ba
Saye Da Sayarwar Zaratan 'Yan- wasan Kwallon Kafa Na Duniya
James zai cigaba da zama a Bayern Munich har
izuwa karshen kakar bana.
Manchester United, Liverpool suna neman dan
wasan Benfica mai shekaru 21 mai suna Joao
Felix.
Coach din Chelsea wato Maurizio Sarri yace
bazai taba canza salon buga wasansa ba dukda
ya samu rashin nasara a hannun Arsenal. Chelsea da Manchester City suna neman matashin dan wasan Barcelona mai suna Ilaix
Moriba, Coach din Liverpool yace zai iya hakura da sayen yan wasa a January din nan dukda matsalar rauni dan wasu daga cikin yan wasansa suke fuskanta.
Arsenal da Monaco suna neman dan wasan Atletico Madrid mai suna Gelson Martins.
Agent din dan wasan baya na Porto mai suna Eder Militao yace dan wasan bazaije Manchester United a wannan watan ba, kuma idan ma zai bar
Porto din to Spain zai koma.
Shugaban Barcelona wato Josep Maria Bartomeu
ya tafi Amsterdam domin kokarin tattaunawa da
dan wasan tsakiya na Ajax – dan wasan dai an
rawaito yafi sha’awar zuwa zuwa PSG domin
kuwa sune zasu ringa biyansa kudi mai yawa fiye
da Barcelona.
Dan wasan gaba na West Ham wato Andy Carroll
ka iya komawa Tottenham sakamakon rauni da
dan wasan gaban Tottenham din yayi wato Kane.
Ana sa ran cewa Chelsea yau zata kammala
daukan dan wasa Higuain a matsayin aro – shi
kuma dan wasa Emerson zai koma Juventus din.
Matashin dan wasan gaba na Genoa mai suna
Krzysztof Piatek zai koma AC Milan akan kudi
Euro Million 30.
Juventus tana daf da daukan dan wasan baya na
Manchester United mai suna Darmain a matsayin
aro.
Hadiza Gabon ta yi kyau a wadannan hotunan
Tauraruwar fina-finan Hausa, Hadiza Gabon kenan a wadannan hotunan nata da ta sha kyau
tubarkallah, muna mata fatan Alheri