Tawagar yakin neman zaben shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ta isa jihar Sakkwato da ke arewa maso yammacin
kasar a yau Laraba, a ci gaba da neman
kuri’u da shugaban yake yi na neman
wa’adi na biyu.
Ga kadan daga cikin abin da ya fadawa
al’umar jihar Sakkwato kamar yadda
wakilinmu Muratala Faruk Sanyinna ya
aiko mana da rahoto:
Boko Haram: “Cikin ikon Allah, ku ne
shaidu, mun yi iyakar kokarinmu,
kuma a jiya, mutanen Borno sun
tabbata mun ci karfin Boko Haram.
Noma: “Batun arzikin kasa da wadata,
Allah ya taimake mu, damunoni biyu
da suka wuce, sun yi albarka.”
Cin Hanci Da Rashawa: “Batun cin hanci
da rashawa, wannan gwamnatin tana
kokari akan ka’idodin da aka kafa. Na
yi muku alkawarin, ni ba zan ci
amanarku ba, ba kuma zan ga ana cin
amanarku ba in kyale.” Yayin nasa jawabin, Ministan sufuri kuma shugaban gangamin yakin
neman zaben shugaba Buhari, Rotimi Amaechi, ya sha alwashin za a gina layin dogo da zai hade yankunan jihohin Sakkwato, Kebbi da Zamfara.
No comments:
Write Please Share a Your Opinion.