A yau, Alhamis ne shugaba
Muhammadu Buhari ya ce MInistan
Sufuri, Rotimi Amaechi ya jefa shi a
cikin matsala yayin da ya yi alkawarin
gina layin dogo da za ta hade yankin
Kudu maso Gabashin kasar da Arewa.
Shugaba Buhari ya yi wannan jawabin
ne a wurin taron kaddamar da yakin
neman zabensa da akayi a cikin filin
motsa jiki na Nnamdi Azikwe da ke
garin Enugu.
Buhari ya ce abu ne mai wahala
gamsar da majalisar zartarwa na kasa
su amince da ayyukan layin dogo amma
ya ce zai yi iya kokarinsa domin ganin
'yan majalisar sun fahimci
muhimmancin gudanar da aikin.
"Amaechi ya yi muku alkawari amma
ban san yadda zan cika alkawarin ba.
Amma zanyi iya kokari na domin ganin
'yan majalisar zartarwa sun amince da
gudanar da aikin," inji Buhari.
Ya ce ba a gabatar wa Majalisar
Zartarwa alkawarin da Amaechi ya yi
ba inda ya ce zai fi dacewa a bari
Majalisar su amince da aikin kafin a
bayyana wa mutane.
Shugaban kasar ya mika godiyarsa ga
mutanen yankin bisa yadda suka fito
kwansu da kwarkwata su tarbe shi
kuma ya shawarci su kasance masu
kishin Najeriya domin ba su da wata
kasar bayan ita.
Ya kara da cewa, " ya zama dole
dukkanmu mu hannu hannu wurin
guda domin ciyar da kasar mu gaba
saboda ba mu da wata kasar bayan
wannan."
A baya, Ameachi ya shaidawa 'yan
jam'iyyar da magoya bayansu cewar za
a farfado da layin dogo na yankin
kudu.
Ya ce babban aikin da za muyi shine,
"zamu amince da shimfida layin dogo
daga Fatakwal zuwa Maiduguri wanda
zai wuce Fatakwal zuwa Onitsa har
zuwa Awka.
"Na biyun kuma zai bi ta Fatakwal,
Umuahia, Enugu, Makurdi da Jos."
Amaechi ya ce, "sauya tsarin rabon
arzikin kasa zai yiwu ne idan aka sake
zaben shugaba Muhammadu Buhari
saboda dan kabilar Ibo ya zama
shugaban kasa bayan Buhari ya
kammala wa'adinsa
No comments:
Write Please Share a Your Opinion.