Shugaban Portugal Marcelo Rebelo de Sousa,
ya ce gwamnatinsa tana nazari kan yiwuwar
kwace babbar lambar yabo da ta baiwa dan
wasan kasar Cristiano Ronaldo.
Matakin a cewar shugaba Rebelo de Sousa, na
da nasaba da hukuncin biyan tara da kotun
Spain ta yanke kan Ronaldo, bayan samunsa da
laifin kin biyan haraji, yayin da yake wasa a
kungiyar Real Madrid.
A shekarar 2016 Portugal ta karrama Ronaldo
da lambar yabo mafi girma da ake baiwa farar
hula ta ‘Portuguese Order of Merit’ a turance,
bayan taimakawa kasar da ya yi, wajen lashe
gasar cin kofin kasashen nahiyar Turai.
Sai dai a ranar Talatar da ta gabata, wata kotun
Spain ta yanke hukuncin tilasatawa Cristiano
Ronaldo biyan Dala miliyan 3 da dubu 57 saboda
kin biyan makudan kudade na haraji ga
gwamnatin kasar.
Da fari hukuncin kan Ronoldo na daurin
shekaru 2 biyu ne a gidan Yari amma aka
sassauta hukuncin zuwa biyan tarar euro dubu
365 na take, tare da biyan karin euro miliyan 3
da dubu 200
No comments:
Write Please Share a Your Opinion.