Allah shi yake kaddarawa bawa samu da rashi, wanda Allah ya nufe shi da zama cikin kunci ko rashin wadatar abubuwa da saba rayuwa dasu, ba
kaskanci ba ne face jarraba da kuma
kaddarar Allah akansa.
Mai hankali yasan duniya bala'ice gida
ne na jarrabawa tsakanin wadata da
tsanani.
Ubangiji Yace;
“Kuma za mu jarraba ku da sharri da
alheri a matsayin fitina, kuma gare Mu
kuke komawa.'' (Anbiya:35). Bai
kamata ga mutum idan ya tsinci kansa
a cikin Jarrabawa ta kunci ko talauci
ko dusashewar daukaka ko ciwo ya
zargi wasu mutane ba. Allah yana
jarabtar bawa Sakamakon abin da ya
aikata ga ‘Yan uwansa mutane na
Alfahari, Dagawa da Girman kai. To
shin Ina ma matsayin takawakkali da
yadda kaddara?
Tawakkali ga Allah shine abin bukata
daga ko wane mutum,
a ko wanne hali ya tsinci kansa.
Cikakken tawakkali shin zuciya ta
nutsu ta mika komai ga Allah ta haka
za’a samu alkairi da kariyar daga
sharri.
Babu wanda ya isa ya baka daukaka ko
ya kwaceta sai Allah in dai ka dagara
ga Allah hakikani dogaro, Allah zai
azurtaka kamar yadda yake azurta
tsuntsu da sauran dabbobi.
In gaske ne mutum ya fawwala
lamuransa ga Allah, ya yadda da Allah
shi yake bada daukaka da daukewarta to sai a nisanci Kage, zargi, camfi, da
tazarta masana’antar da Allah ya baka Suna a cikin ta kai aure kai gida kasai
babur. Lallai in da kake yanzu haka
Allah ya so ya ganka
Ubangiji Yace; cikin Qurani
“Kuma Idan Allah ya shafe ka da wata Cuta, babu mai yaye ta, sai shi, idan kuma ya shafe ka da wani alheri, babu mai iya ture falalarsa. Yana samun wanda ya so daga cikin bayinsa da ita,
kuma shi mai gafara ne, mai jin kai
No comments:
Write Please Share a Your Opinion.