Kocin kungiyar kwallon kafa ta Manchester City Pep Guardiola ya ce abin alfahari ne ya zamana Club din ya yi nasarar lashe kofuna har 4 cikin kaka guda dai dai lokacin da ya ke shirin Komawa wasannin cin kofin FA bayan
takaitaccen hutu. City dai ita ce kungiya daya tilo da ta ke da zarafin iya lashe kofunan Firimiya da FA da kofin League da kuma zakarun Turai la’akari da
matakin da ta ke a kowacce gasa.
Yanzu haka dai City na da tazarar maki 4 ne
kacal tsakaninta da Liverpool da ke saman
Teburi, a bangare guda kuma an ga rawar da ta
ke takawa a gasar ta FA da ma yadda ta ke
shirin tunkarar wasan karshe a gasar League
tsakaninta da Chelsea cikin watan Fabarairu
baya ga gasar zakarun Turai. A gobe asabar ne Manchester City za ta kara da Burnley a zagaye na 4 na wasannin cin
kofin FA
No comments:
Write Please Share a Your Opinion.