Wani rahoton Kungiyar Agaji ta Oxfam ya
bayyana cewa, mutane 26 da ke kan gaba
wajen yawan arziki, sun mallaki
kwatankwacin kadarorin rabin al'ummar
duniya. Oxfam ta bukaci gwamnatocin
kasashe da su tsauwala haraji kan
mawadatan domin rage ratar da ke tsakaninsu
da talakawa.
Sabon rahoton da aka wallafa gabanin taron
tattalin arziki na Davos, ya bayyana cewa,
attajiran da suka mallaki biliyoyin kudi a duniya,
sun samu habbakar duniya da akalla Dala biliyan
2.5 a kowacce rana a shekarar da ta wuce.
Oxfam ta ce, shugaban Kamfanin Amazon, Jeff
Bezos da ya zarce kowa arziki, ya samu
habbakar dukiyarsa da Dala biliyan 112 a bara
kadai, yayin da kungiyar ta ce, kashi daya na
dukiyarsa, shi ne ya yi daidai da kasasfin kudin
kiwon lafiyar kasar Habasha mai yawan al’umma
miliyan 105.
A gefe guda kungiyar ta ce, talakawa biliyan 3.8
sun samu karayar tattalin arziki da akalla kashi
11 cikin shekarar bara, abin da ke nufin cewa,
wannan banbancin da ke tsakanin matalauta da
mawadata ya dada nuna gazawar hukumomi
wajen yaki da talauci a duniya.
Shugabar Oxfam, Winnie Byanyima ta ce,
talakawan duniya sun fusata saboda yadda
matsalar tattalin arzikin ta dabaibaye su.
Kungiyar ta zargi gwamnaton kasashen duniya
da rura matsalar rashin daidaito tsakanin
talakawan da masu hali saboda gazawarsu
wajen samar da kudaden gina al’umma
No comments:
Write Please Share a Your Opinion.