Atiku ya nada wannan jaruma ce mukamin jami’a mai kula da matasan Nollywood gaba daya, ta yadda zata karkato masa ra’ayin
matasan Nollywood da nufin su bashi goyon baya tare da tallatashi, har sai ya
kai ga nasara a zaben shugaban kasa
Regina
Jarumar mai shekaru goma sha takwas
a rayuwa ce ta sanar da wannan cigaba da ta samu a shafinta na kafar
sadarwar zamani ta Instagram, inda tace tana goyon bayan Atiku dari bisa dari, kuma zata bada duk gudunmuwar data dace don ganin ya samu nasara. “Sunana Regina Daniels, ina alfahari da kasancewata yar Atiku dari bisa dari, na amince da mukamin daya nadani na mai
kula da matasan Nollywood, zan yi aiki tukuru saboda Atiku mutum ne mutunta matasa, kuma yayi alkawarin zai baiwa matasa mukamin ministoci a gwamnatinsa Najeriya na cikin mawuyacin hali, jama’a na fama da yunwa, lokaci yayi da zamu karkatar da akalar kasar zuwa tudun mun tsira, tun daga Bama har zuwa Bori, Aba zuwa Abuja, Kaura Namoda zuwa Kaduna, lokaci yayi da matasan Najeriya zasu hada kai dani wajen zaban Atiku/Obi a 2019 don kare rayuwarmu Inji ta
Regina
na daga cikin fitattun jaruman fina finan Nollywood da suka bayyana goyon bayansu ga tafiyar Atiku Abubakar a shafukan sadarwar zamani, sai dai rahotanni sun tabbatar da cewar masana’antar Kannywood da ta Nollywood ta rabu gida biyu tsakanin yan Atiku da yan Buhari
No comments:
Write Please Share a Your Opinion.