Miyyeti Allah tace Atiku na amfani da
matsalar yan Fulani wajen yin kamfen
dinsa
- Kungiyar tace tsohon shugaban kasa ba
Bafulatani bane
- An tattaro cewa Atiku yace Buhari ba
Bafulatani bane
Kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore
Fulani ta bayyana cewa dan takarar
shugaban kasa na jam’iyyar Peoples
Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar
ba Bafulatani bane.
Jaridar Punch ta rahoto cewa Saleh
Alhassan wanda ya kasance babban
sakataren kungiyar na kasa na martani
ne ga ikirarin Atiku na cewa shugaban
kasa Muhammadu Buhari ba Bafulatani
usuli bane.
A wani gangami a igawa, an tattaro
inda Atiku yace: “Bafulatanin usuli ba
zai efa dan uwansa a cikin kangin
talauci ba kamar yadda yake faruwa a
yanzu a karkashin gwamnatin All
Progressives Congress."
Atiku ba Bafulatani bane – Miyetti Allah ta
bayyana daga inda tsohon mataimakin shugaban
kasar ya fito
Alhassan yace don Atiku na yaren
Fulatanci ba yana nufin shi Bafulatani
bane.
Yace: "Batun gaskiya shine, a wurare da
dama a jihar Adamawa, suna yaren
Fulatanci. Don Atiku ya iya Fulatanci ba
yana nufin shi Bafulatani bane.
"Idan ka kalli kirar Atiku, baya dauke da
siffar Bafulatani. Kana kallon Atiku ka
ga dan kabilar Bantu. Ba dan kabilar
Sudan bane.
No comments:
Write Please Share a Your Opinion.