James zai cigaba da zama a Bayern Munich har
izuwa karshen kakar bana.
Manchester United, Liverpool suna neman dan
wasan Benfica mai shekaru 21 mai suna Joao
Felix.
Coach din Chelsea wato Maurizio Sarri yace
bazai taba canza salon buga wasansa ba dukda
ya samu rashin nasara a hannun Arsenal. Chelsea da Manchester City suna neman matashin dan wasan Barcelona mai suna Ilaix
Moriba, Coach din Liverpool yace zai iya hakura da sayen yan wasa a January din nan dukda matsalar rauni dan wasu daga cikin yan wasansa suke fuskanta.
Arsenal da Monaco suna neman dan wasan Atletico Madrid mai suna Gelson Martins.
Agent din dan wasan baya na Porto mai suna Eder Militao yace dan wasan bazaije Manchester United a wannan watan ba, kuma idan ma zai bar
Porto din to Spain zai koma.
Shugaban Barcelona wato Josep Maria Bartomeu
ya tafi Amsterdam domin kokarin tattaunawa da
dan wasan tsakiya na Ajax – dan wasan dai an
rawaito yafi sha’awar zuwa zuwa PSG domin
kuwa sune zasu ringa biyansa kudi mai yawa fiye
da Barcelona.
Dan wasan gaba na West Ham wato Andy Carroll
ka iya komawa Tottenham sakamakon rauni da
dan wasan gaban Tottenham din yayi wato Kane.
Ana sa ran cewa Chelsea yau zata kammala
daukan dan wasa Higuain a matsayin aro – shi
kuma dan wasa Emerson zai koma Juventus din.
Matashin dan wasan gaba na Genoa mai suna
Krzysztof Piatek zai koma AC Milan akan kudi
Euro Million 30.
Juventus tana daf da daukan dan wasan baya na
Manchester United mai suna Darmain a matsayin
aro.
No comments:
Write Please Share a Your Opinion.