Tauraron fina-finan Hausa, Bashir Bala Chiroki
kenan a wannan hoton yayin da ya karbi
gudummuwar Naira dubu 215 da aka tara mai ta
hanyar shafin NorthernHibiscus dake dandalin
Instagram.
Labarin halin da Chiroki yake ciki ya watsune
bayan da aka yi hira dashi a gidan talabijin na
Arewa24 inda yace yanzu sana'ar saida kunu
yake sanadiyyar watsi dashi da masana'antar
fina-finan Hausa tayi.
Tauraro Ali Nuhu dai ya musanta wannan ikirari
na Chiroki inda yace har yanzu ana yi dashi
sannan kuma irin talaucin da ake tunanin
Chirokin ya shiga a zahiri ba haka bane
No comments:
Write Please Share a Your Opinion.