. June 2018 - hausanet hausanet





Thursday, 7 June 2018

Babu Jarumar Kannywood Da Zata Iya Fice Kamar Rahma Sadau

Rahama Sadau wata Jaruma ce a kasar Najeriya wadda tayi fice wajen a fanninwasan kwaikwayo na masana’antar Kannywood. An haifi Sadau a ranar 7 da watan Disamba na shekara ta alif dari tara da casa’in da uku (7 December 1993) a
unguwar Sarki dake cikin garin Kaduna na Jihar ta Kaduna a Najeriya. Ta shiga masana’antar Kannywood a shekarar 2013. Sadau ta kasance daya tilo wajen tafka mahawara a cikin yaren Hausa,
Turanci da Indiyanci baki daya. Jaruma Sadau ta samu fice bayan fitowar ta a wani shiri mai suna “Gani Ga Wane” tare da Jarumi Ali Nuhu Duk da dai cewar Jaruma Rahama Sadau ta samu fice a ita masana’antar ta Kannywood,
sai dai kuma a ranar 2 ga watan Oktoba na wannan shekata ta dubu biyu da sha shida (2 October 2016) kungiyar MOPPAN ta samu
dakatar da Jarumar kasancewar samunta da laifin rungumar wani mawaqi a wani faifan bidiyo mai suna ClassiQ wanda ya fito daga
yankin Jos na jihar Filato a Najeriya. Ita dai wannan dakatarwa bata samu cirewa ba har a yanzu inda wadansu kan kalle ta a matsayin kora gaba daya daga cikin
masana’antar. Kungiyar MOPPAN tayi tsokaci da cewar rungumar da Jarumar tayi ya saba tarbiya da
tsari irin na duk wani mai yin shirin fim na Hausa. Sai dai korar Jaruma Rahama Sadau bai hana fina finai masu hoton ta fita ba duk da cewar masu wallafa shirin na fina finan
basu ci gaba da sakata ba a cikin shirin sabbin fina finai. Hakan kuwa tana faruwa ne sakamakon cewar akwai fina finai da dama

Www.hausanet.ml

wadanda Jaruma Sadau take cikin su da basu samu fita ba a kasuwannin fina finai a lokacin da akayi kata ita waccan kora. Duk Da Hakan Kamfanin Google Suna Nuna
Cewa Anfi Duba Labarin Rahma Sadau Fiye Da Sauran Jaruman A Lokacin Da Majiyarmu Ta Duba. Hakan Yasa Jarumar Ta Samu Kyautuka Da Da-ma Daga Kamfani Da Kuma Masu Bada Award Wasu Sunce Mah Korarta Kannywood
Albarka CE Agareta Domin Ya Kawo Mata cigaba Ciki Sauri Fiye Da Sauran Jarumai Mata NaKannywood
Akwai Manyan Mata Irin Su Hadiza
Gabon,Nafisa Abdullahi Wanda Sunfi Ta Dadewa Amma Ta Kera Su Wajan Fice Duk Da Yanzu Suma Sun Koma Fim Din Kudancin Nijeriya. Rahma Sadau Yanzu Na Koma Abun Koyi Ga Manyan Mata A Arewacin Nijeriya Inda Manyan Gidan Jarida Na Leadership Sun Kira Sunanta Amatsayin Jaruma Mai Jarumta Da
Kuma Gwazo Inda Har Ta Samu Kyautar babbar jaruma ta Kannywood. Wasu Suna Ganin Cewa Ilmin Ta Shine Ya Taimake ta Sosai

Za'a nada Adam Zango da sarautar 'Sarkin Kannywood

Kungiyar kannywood ta bayyana dalilain da ya sanya zasu nada jarumin da sarautar bayan tattaunawa da
suka yi tsakanin su 





Kungiyar masu kallon fina-finan hausa na
shirin nada jarumi Adam A. Zango da
sarautar sarkin kannywood bisa
gwagwarmayar da yake a masana'antar nishadantarwa. Falla M Sherrif wanda yake shine shugaba mai
riko na kungiyar ya zanta wa jaridar RARIYA cewa kungiyar zata nada jarumin da sarautar bayan tattaunawa da tayi kan wanda yafi
cancanta. Ya bayyana dalilai da yasa zasu ba Adam Zango sarauta kamar haka : "Don kasancewar sa mai hakuri, iliminsa mutuncinsa, kyautarsa, biyayyarsa, ibadarsa, yafiyarsa ida an yi masa laifi da kuma daukakarsa. Sannan kuma mawaki ne, makadi ne,furodusa ne, darakta ne, edita ne, jarumi ne, dan rawa ne da dai sauransu. Shugaban kungiyar ya kuma kara da cewa, yanci da masu kallo ke dashi a wajen masu shirya fina-finai yana daga cikin dalilin nada shi saboda a dalilin su ake shirye fina-finan hausa
domin su siya. Al'amarin ya janyo farin cikin ga dinbim
masoyan jarumin 'Gwaska" inda suka gudanar da biki na taya murnar samun wannan sarauta. Sai dai wannan sabon sarauta zai raba hankalin jama'a ya kuma sanya alamar tambaya ga masu
bibiyan masana'antar Kannywood.
Sanin jama'a ne cewa an nada jarumi Ali Nuhu da wannan sarautar kuma mafi yawanci ma
dashi aka yi masa lakabi.






A wata sako da ya wallafa a shafin sa na Instagram kwanan baya, jarumi Bello Muhammed Bello yayi kira na a gudanar da zabe domin nada sarautar Sarkin kannywood domin bada hanyar zaben wanda
yafi cancanta da ya zama sarkin

FARKON SO LABARIN QAUNA AKOI DADI DAGA WWW.HAUSANET.ML

Ashe haka so yake na A lokacin da na
Fara kallon ta tana tafiya

cikin nutsuwa, burgewa, da takun Isa, Sanye take cikin doguwan rigan material, kalan brown da milk, saita yafa k'aramin mayafi akai, tana rik'e da wasu littafai a hannunta. Bata ankara ba sai dai taji abu ya dakar mata goshi harta kusa faɗuwa, kafin ta ɗago kanta kawai taji an kwashe da dariya, cikin kaunar

zuciya ta ɗago da kanta tana k'arema wurin kallo, gaba ɗaya cike wurin yake da ɗaliban jami'ar kuma kusan duka hankalinsu na akanta. Dariyarshi tafi shigar mata kunne, juyawa tayi ta watsa mishi harara. Dariya yayi irinta gogaggun en iskannan, "zo mana" ya kirata da hannu, yana zaune saman motah da en korenshi zagaye dashi, taso ace zata iya komawa ta sauke mishi duk masifan dake ranta, anma jin kanta da tak'ama bazai taɓa barinta ba, kuma shi bai kai ajin da zata tsaya gaban mutane tana maida magana dashi ba. Juyawanta kawai tayi taci gaba da tafiyanta,
Batasan sanda ya diro daga saman motan ba, sai dai kawai taji yana neman rik'o hannunta, cikin zafin nama ta juyo ta wankeshi da marin da yazo mishi a bazata, ɗaga kanshi yayi yana kallon mutanen da sukayi cincirindo suna kallonsu, sannan kowa ya fara k'ok'arin riƙe dariyanshi don
babu wanda baisan halin Abdallah ba. "Ni kika mara?" "an mareka ɗin, wannan shine gargaɗin dazan maka na ƙarshe akan shiga harkata da

kake "ke kinsan waye Abdallah, wallahi sai kinyi dana sanin marina da kikai"
Anma bakasan wacece Rabi'ah ba, kuma ina mai baka shawaran karka zaƙe akan saika sani ɗin" Nunata yayi da ɗan yasha, "zan ramane a
inda zaifi miki ciwo, kuma ki sani ban taɓa son abu na rasa ba, ko bakiso dole kiyi soyayya dani" Tofar da yawu tayi a k'asa, "Allah ya kiyayemun soyayya da ɗan shaye-shaye" ta juya ta barshi wurin a tsaye yana huci yama
kasa maida mata magana, ya watsa ma mutanen wurin kallo ba shiri kowa ya ɓace, ya shige motanshi ya jata a guje. Hankalinta kwance ta gama lecturenta suka fito tare da Aminiyarta Amrah, hannunta taja suka koma gefe, "Faɗamin Rabi'ah meye gaskiyar abinda naji wai kin mari Abdallah" "toh meye naga duk kin wani ruɗe kaman wani babban abune ya faru?" haba Rabi'ah, naga hankalinki kwance kaman bakisan halin Abdallah ba" "ni mamaki kike bani wallahi, siyasa ne kawai zai nunamun, anma kuɗi kam har ke kinsan Yayana yafi mahaifinshi sosae, don haka duk abunda zaiyi nima zan iya, ban taɓayin abunda nayi dana sani ba

"hakane fa, anma ni dai duk a tsorace nake "kinma warware," Tun daga bakin gate, ma'aikatan gidan ke
kawo mishi gaisuwa anma ko kallo basu isheshi ba, ganin motoci da yawa ya tabbatar mishi Daddyn nashi na a ciki, don haka kai tsaye falon Mai girma mataimakin Governor ya wuce, Zaune yake yana amsa waya, bodyguards
nashi zagaye dashi, yana ganin yanayin da Abdallah ya shigo dashi, ba tare da yaa gama ba ya katse wayan.
"Yadai Son?" cikin sham ƙamshi ya kalli bodyguards ɗin, sannan ya maida kallonshi kan Dad din nashi, alama ya musu da su fito, cikin bin Umarni duk suka fita. waye kuma ya taɓomin kai?" Saida ya ƙara ɓata fuska sannan ya faravmagana, "Haba Dad! Ni bansan me yasa baka damu da abinda nakeso ba, ba ruwanka dani sai harkan siyasarka kawai" akwai abinda ka taɓa nuna kanaso banyi maka bane?" "A'ah kawai dai wannan ne nake tunanin
bazan samu ba babushi, indai Kuɗi da Mulki na iyayin komai a duniya babu abinda zaka nema bazanyi maka ba"I know Dad, but uh should promise me" "promise" thank you Dad,

i love you

Sannan ya fara fara'a, jinsa yake wasai kaman yama riga da yaa rama abinda Rabi'ah ta mishi

MINENE HASSADA, KUMA YA AKE HASSADA, KUMA SU WANENE MASU YIN HASSADA

1- Hassada wani mugun ciwo ne da ke Nukurkusar mai yinta a cikin zuciyarsa shi kadai.

Hassada shine Jin Zafi, Daci, ko Bacin Rai a yayin da kaga wani Dan'uwanka, Makwabci, Aboki ko ma wani kawai da ka sani a duniya ya samu daukaka, ko wani iri

Hassada kala uku ce (3)

A- Akwai jin kyashi, shine mutum yaji a zuciyarsa don me wani zai fishi wani abu a rayuwa. Kudi, Mulki ko kuma Baiwa ko Mukami.

B- Mutum yaji shi bayason kowa ya samu wani abun alkhairi ko karuwa sai shi kadai.

C- Wannan shine yafi kowanne muni, wato mutum yaji cewa idan dai shi bazai samu abu ba to gara kar kowa ya samu.  Irinsu sune suke yin a fasa kowa ya rasa

2- Mutane da yawa suna fadawa cikin aikata Hassada ba tare da sun ankara ba misali:

A- Yawan yin magana akan ci gaban wani ko wata e.g 1- oh su wane an haye, sai kace da ba teburin mu daya ba a wajen aiki, lokacin nan kuwa kayansa basu wuce kala biyar ba.

2-  Mutum ya rinka gamin wane an samu shiga, ji wai yanzu shine kaza, sai kace ba tare aka daukemu aiki ba.

3- Dubi daga malami ya shigo aji sai ya fara wani iyayi wai shi a dole ga mai kwakwalwa

YA ZA'AYI MUTUM YA GANE CIWON HASSADA YA FARA SHIGARSA

Yanda mutum zai gane idan ya fara koyon Hassada shine

A-Yawan damuwa da al'amarin wani ko wata, wanda kwata kwata bai shafeka ba ta ko wani hanya.

B- Damuwa da son sanin halin da wata ko wani yake ciki, idan kaji mummunar labari game da wani kaji dadi a ranka ko ma kayi dariya ko shewa, idan kuma kaji labari mai dadi game da mutum sai kaji ranka ya baci, ka kasa yi masa fatan alkhairi, ka fara jin tsoron kar ya wuceka a level na rayuwa. Sai ka fara kokarin kai sukarsa a wajen abokan arzikinsa, ko kokarin fadin miyagun maganganu game dashi, ko kuma fadin kalamai na batanci game dashi. Musamman ma idan ba'a tambayeka labarinsa ba, shine Hassada

4- lllolin Hassada suna da yawa amma ga kadan daga ciki

1- Hassada tana cinye kyawawan ayyukan mai yinta kamar yanda wuta take cinye karmami(Kirare/kara).

2- Hassada tana haifar da ciwon Zuciya da kuma Muni ga mai yinta.

3- Hassada tana hana mai yinta samun cigaba a cikin rayuwarsa da kuma duk abunda yasa gaba ba zaiga nasara bayyanan ne akai ba.

4- Hassada tana rage lmani kuma tana taimakawa wajen aikata Shirka da fita ma daga addini ba tare da mai yin Hassadar ma ya ankara ba.

5- Hassada shine kofa na aikata mafi yawancin manya manyan kaba'irai, kamar

A- Gulma
B- Munafunci
C- Makirci
D- Rashin yadda da Kaddara
E- Rashin hakuri
F- Karya
G- Yaudara e.t.c

YA ZA'AYI KA KARE KANKA DAGA CUTAR HASSADA

Yanda zaka kare kai daga Hassada shine yafi komai sauki, saboda ai yin Hassadar tafi wuya, takurawa kanmu mukeyi sai munyi Hassadar duk da mun san illarta da kuma nauyin Zunubinta

1- Mutum yayi kokarin cire kansa akan duk wani al'amurran da basu shafeshi ba.

2- Mutum yayi kokari yayi focusing akan inganta rayuwarsa.

3- Kiyayewa daga kananan Gulmace-Gulmace.

4- Son iyawa ko son bada shawara a inda ba'a nemi taimakonka ba.

5- Addua da yima zuciyarka addu'ar tsarkakuwa daga dukkanin miyagun ayyukan da ka iya gurbata ta

Mutane da dama sukan tsinci kansu a cikin wani yanayi mai ban al'ajabi, za kaga mutum yana yawaita Azumi, Nafilfili, tsayuwar dare, Sallolin Farilla sam basa wuceshi amma sam baya cigaba a rayuwarsa, kodai yaci baya ko kuma kullum yana nan a inda yake, babban dalilin haka shine

Zuciyarsa Baka ce sam babu alkhairi a mu'amalarsa da mutane, kullum ya bude bakinsa sai dai ya fadi Sharri ko ya kulla Makirci, ko kuma zargi akan abinda ba damuwarsa bace.

Sau da yawa za kaga mutumin Banza, Mashayi ko Mazinaci amma duk abunda yasa a gabansa zai samu, wani ma sam ko Sallah ba kullum yakeyi ba, amma da ya fara neman abu sai kaga ya samu, ba komai Allah ya keso ya nuna mana anan ba, illa, mu fahimci cewa shi Allah da Zuciyoyinmu yake aiki

Saboda haka da zarar mutum yayi Addu'a yayi Addu'a yaga ba'a amsa masa ba, to ya fara bincikar Zuciyarsa, Sannan kuma sai ya binciki Ayyukansa lallai  akwai inda yake da matsala.
Allah ya shiryar da mu

Monday, 4 June 2018

Sunayen yan wasan Najeriya 23 da zasu wakilci kasar a Rasha

Mai horar da yan wasan Najeriya Gernot Rohr ya bayyana sunayen ‘yan wasan kasar 23 da zasu fafata a gasar cin kofin duniya da za’a
fara ranar 23 ga watan nan a Rasha.
Bayan karawar da kungiyar tayi da Ingila,

Rohr ya sauke ‘yan wasa biyu daga cikin 25 da ya tafi da su da suka hada da Ola Aina da Mikel
Agu. Wadanda suka samu shiga sun hada da masu
tsaron gida 3 da ‘yan tsaron baya 8 da ‘yan
tsakiyar fili 6 da ‘yan wasan gaba 6.
Sunayen masu tsaron gidan sun hada da

Ikechukwu Ezenwa da Daniel Akpeyi da Francis
Uzoho. Yan wasan baya sun hada da Wiliam Ekong da Leon Balogun da Kenneth Omeruo da
Bryan Idowu ad Chidozie Awaziem da Abdullahi
Shehu da Elderson Echiejile da Tyronne Ebuehi.

Yan wasan tsakiya sun hada da kaftin Mikel
John Obi da Ogenyi Onazi da John Ogu da
Wilfred Ndidi da Oghenekaro Etebo da Joel Obi.
Sai kuma yan wasan gaba da suka hada da
Odion Ighalo da Ahmed Musa da Victor Moses
da Alex Iwobi da Kelechi Ihenacho da Simeon
Nwankwo.

Najeriya zata kara da Croatia da Iceland da kuma Argentina a zagayen farko

Sunday, 3 June 2018

Adam Zango zai yi wasa a kasar Faransa

Shararen jarumin Kannywood kuma
mawaki, Adam Zango, zai tafi kasar Faransa domin hallartan nadin sarauta da za'ayi wa wasu hausawa

mazauna kasar inda kuma ake sa ran zaiyi wasa a wajen taron
Masoya jarumin sunyi tururuwa zuwa shafinsa na dandalin sada zumunta na Instagram don taya shi murnar wannan karamci da akayi masa tare da yi masa fatan alkhairi.
Zango yana daya daga cikin jaruman
Kannywood da su kayi fice wajen
wakokin Hausa wanda hakan yasa wasu ke yi masa lakabi da 'Davido na Arewa inda suke kwatanta shi da shahararen mawakin Najeriya Davido Baya ga haka Zango ya sami nasarori

sosai a matsayinsa na jarumin fim da kuma mai shirya fina-finai. Wasu daga
cikin fina-finansa da su kayi farin jini sosai sun hada da Basaja da Gwaska.
A shekarar 2016, Zango ya samu rashin jituwa da jaruma Rahama Sadau inda su kayi ta musayar maganganu amma daga baya Sadau ta shaidawa majiyar hausanet.ml cewa tuni sun shirya da Zangon
I na murnar sanar da ku masoya na
cewa an gayyace ni zuwa nadin
sarauatan wasu muhimman mutane da hausawa mazauna kasar Faransa za su dauki nauyin gudanarwa . Ma Za'a karama mutane da dama daga
kasashen Kamaru, Chadi, Jamhuriyar

Congo, Ghana da kuma wasu kasashen turai kuma ina daga cikin wanda aka gayyata don inyi waka a wajen taron inji shi

MUSHA dariya BA QAU QAU TAWA

Musha dariya

Wani dan fulani ne yaje kano yaga yara suna ta sayen sweetcamfo (alewar larabawa) sai abin ya
bashi sha'awa sai ya bada kudinsa a bashi,koda aka bashi ya saka ta (alewar) a bakinsa kun san yadda take sai ta narke ya neme ta ya rasa Sai yaji zaki ,budar bakinsa sai yace

SHEGU KANAWA SUN FARA SAIDA BABU


LABARIN DANFULANI

Wani bafullatani ne ya ga wani gida an yi masa farin fenti yana ta sheki, sai ya zauna ya fashe da kuka,
akayi akayi yayi shiru yaki. Da kyar aka samu ya daina kukan....
.Sai aka tambaye shi, wai bawan Allah mai ya saka kukan ne?
sai ya ce shi wallah I wulaqancin mutanen birni ne ya ishe shi. Yanzun su rasa da abinda zasu yi fenti sai da

KINDIRMO!!!!!(NONO)

Wasu fulanine su uku sun shigo birni sai suka ga ana wasa da biri suka tsaya suna kallo akace biri
yayi tafiyar Karuwa taga mai kudi Biri yai far da ido yana tafiya yana yanga da kwarkwasa kai kace wata tsohuwar karuwa a kai ta sanya shi yana kwaikwayon abubuwa daban daban yana yi aka ce
yayi tsallen kwado sai yayi sai Dan fulani yaji haushin biri yace yau ga shege. Sai akace biri yi zaman Dan fulani shanu sun kare
sai biri ya dauko sandaâ ya sa a kafadar shi ya lankwashe kafarsa Ya murtuke fuska ya zare ido ya
langabe kai jikin sanda, Dan fulani na ganin haka ya bushe da dariya ha ha
ha ha ha ya ce "Kwal uba Aradu kamar Baffa nah!!!"
              
By Dan Fulani
S!r
Angamu

Watarana wani Malami yana wa'azi yadda ake zama da mata sai yace ko wanne mai gida idan matarsa tayi girki idan yanaci yadinga cewa yayi dadi. Idan tayi kwalliya ya yaba. Dajin haka da Tanko yakoma gida da matar sa takawo abinci yafara ci sai yatuna da wa'azin Mallam. Sai yace kai amma abincinan yayi dadi. Yana fadin haka sai matar ta dauki murfin kwano ta kwada masa aka tace  shekara ashirin muna tare baka taba cewa abincina yayi dadi ba sai da na karbo a makwobta

LABARIN SIRRIN MASOYA DAGA HAUSANET.ML

Naci kwalliyata me rai da motsi na shiryawa mijina abincinsa mai dadi na gyara gidana ko ina yadauki kamshi babu abin danake jira sai shi kadai chan gefe naji wayata na ringing Sunan brother dina nagani na danna nasa akunnena shashshekar kuka naji Ana ta fadin ina lillahi wainna ilaihirrajuun Meke faruwa dani jinayi yana fadi allah yayiwa

mama da baba rasuwa yanzunnan hatsarin mota sukayi dif wayar ta katsi ga shi saura minti kadan mijina Ya shigo sati biyu baya gari Yace min yakusa zuwa gida nan da minti goma shabiyar zai shigo gida haka na daure na Dan dai daita fuskata kawai jinayi Ya rungumeni my babyn na daure narungumesa nima nai mishi oyoyo na kaishi yayi wanka na daukomai kayan da zaisa jallabiya muka huce wajan cin abinci yagama sai yake tambayata yanaga Bana murna kamar dazu daya jini awaya Nace mai ka koshi yanxu mai kake bukata Yace min ni Nace kasamu na biya mai bukatarsa natabbatar Ya

gamsu sannan muna Dan hira sai nake gaya mashi dazu dab dazaka shigo aka bugo min waya Mamana da babana sun rasu to nikuma naga ka kusan zuwa shiyasa na danne zuciyata na baka hakinka yanzu sai mu tafi ko razana yayi yasa kuka mai tsanani nima nasa kuka Yace indai aljanna na wajena yabani duniya da lahira in kece zakiya haka

BINCIKE YA NUNA AKAN MATAN AREWA

BINCIKE YA NUNA AKAN MATAN AREWA

<<ABUJA FCT">>
Idan kàna nemar mace mai ji dakài dakuma son girma  To kaje ABUJA.... Idan Kuma Mai son Maza Masu Kudi kake nema   To tafi Gwagwalada...

<<KADUNA STATE>>
Idan kanason mace
Mai ilmin boko
Wayewa
Rashin tarbiya
Wankan swagger
  To kaje KADUNA... Idan kuma kanason mace..
Bagidajiya
Mai biyayya
Ga shegen bleaching
   To ka tafi ZARIA...

<<KANO STATE>>
Idan kanaso mace..
Mayyar kudi
Mayyar mota
Yin bleaching
Mayyar Maza
  To tafi KANO....

<<KATSINA STATE>>
Idan kanason mace..
Mai aji
Mai kwalliya yar kwalisa
Mai biyayya da ladabi
Mai addini
  To tafi KATSINA...

<<NIGER STATE>>
Idan kanason mace ..
Gajeruwa
Doguwa
Kakkarfa
Mai biyayya
Mai kashema maza kudi
Mai ladabi
Mai juya maza
Mai wahala kan maza
Mai son girma
  To tafi NIGER....  Idan kuma mai jan Aji  ne tafi MINNA....    Idan kuma mai yawar yangane tafi BIDA

<<GOMBE STATE>>
idan kanason mace.
  Mai rashin iya girki
  Ga rashin iya kwalliya
  Amma ga tsafta
   To tafi GOMBE...

<<ADAMAWA STATE>>
Idan kanason mace..
  Mai kyau
  Gogaggiya a soyayya
  Amma ga rashin ilmi
     To tafi ADAMAWA... Idan kuma kana nemar mace me son kudi To ka tafi YOLA...

<<YOBE STATE>>
Idan kanason mace..
Mai hakuri
Mai ladabi
Mai wauta
  To ka tafi YOBE....

<<SOKOTO STATE>>
Idan kanason mace..
Mai shan maganin mata
Kafaffiya
Mai son kudi
Marar iya magana
   To ka tafi SOKOTO...

<<PLATEAU STATE>>
Idan kanason mace..
  Yar gayu
  Iya sa kananan kaya
  Ga Iyayi da turanci
  Amma sai rashin ilmi
  To ka tafi JOS.

<<BORNO STATE>>
Idan kanason mace
  Mai kyau
  Yar malamai
  Mai yawan sa turare
  Mai son kudi
  Amma ta iya girki
  Yar boko haram
   To ka tafi BORNO... Idan kuma kana nimar mace mai Karya kuma babu kyau To ka tafi MAIDUGURI....

<<ZAMFARA STATE>>
Idan kanaso mace..
  Mai yawan sa hijab
  Mai tsoron Maza
  Mai rowa
  Amma tana da kyau
    To kaje ZAMFARA

<<KEBBI STATE>>
Idan kana son mace
  Yar boko
  Mai tsadar aure
  Mai wankan
  Mai kyauw jiki
    To kaje KEBBI...  Idan kuma kana nimar Mace mai kyau Amma ga nemar Maza  To Kaje BIRNIN KEBBI...

<<KOGI STATE>>
Idan kanason mace.
  Yar swagger
  Mai yawan kwalliya
  Amm ba wanka
  Sai iya turanci
To ka tafi KOGI....  Idan Kuma Kana nimar Mace mai saurin magana da yanke Hukunci To ka tafi LOKOJA...
   
<<<-BAUCHI->>>
Idan kanason mace
Mai illimi
Ga iyasa himar
Ga kyau
Basa iya  zaman aure
Saikazo bauchi
    
TOH
YAN MATA

        DA
SAMARI  

 

TSAKANIN MAZA DA MATA WA YAFI YAUDARA?

Amsa Daga cikin matsalolin da samarisuke dashi a tasu soyayyar sun hada da 1Mata nasan wasunku zasu yi mamaki idan nace muku
yawancin maza suna yin soyayya ne
kawai ba wai dan sun shirya yin aure ba, kawai su dai burinsu ace suna da budurwa ko kuma suna soyayya, amma batun aure kuwa wannan ba ma ya gabansu! Abin gasa ne a tsakani samari cewa wannan yana da budurwa wancan bashi da ita.
Da mu samari zamu ji shawara to da sai ince babu amfanin muyi soyayya da macen da muka san ba aurenta zamu yi ba kar ma mu tunkareta tun
farko idan musan bamu shiyar yin
aure ba, yana daga cikin dalilan da yasa ‘yan mata suke tunanin cewa duk maza mayaudare ne, saboda dama soyayyar ba’a san ma dalilin
yinta ba, sai lokacin auren nasu na

gaske yazo sai suga cewa  wacce suke soyayyar da ita ba itace suke son aura ba, sai su koma ga wata ita kuma ta farkon sai tace an yauda reta Ku kuma mata shawarar da zan baka anan itace

1 Duk saurayin da yazo muku da
soyayya kuma kuka yaba da halinsa to ku saurareshi, idan yayi muku bayanin abinda yazo dashi na game da soyayya kuma to sai ku nemi ya baku wani dan lokaci da zaku yi tunani a kansa Hikimar hakan shine cewa shi zai samu damar qara bayyanar da soyayyarsa a lokacin da ku kuma kuke qara karantar halayensa kuskurene namiji yatakura mace cewa sai tace tana sonshi a lokaci daya, sai ka bata lokaci ta gama karantarka tukuna a lokacinda kai kuma zaka yi ta qoqarin nuna
mata jarumtakarka ta ‘da namiji dan ka saye zuciyarta

2 Sannan idan kuka karbi soyayyarsa
har soyayyar ta fara ginuwa kuma sai ku fara tattauna batun aure, banga dalilin da zai sa soyayya tayi tsaho har zuwa
kamar wata biyu ba ba tare
da an fara maganar aure ba. Zai iya
yiyuwa budurwa ance ta
fito da miji shi kuma saurayi yana
lissafin sai nan da shekara
biyar zaiyi aure, kunga kenan idan
baku tattauna ba baza ku gane hakan ba

3 Idan aka samu dacewa masoyan
biyu suka yarda zasu auri juna kuma suka yarda akan lokacin da zasu yi auren to sai a gaggauta shigo da manya cikin maganar, wannan zaisa kowa yasan cewa abinda gaske ne kuma hankalin kowa ya kwanta,
kama daga su masoyan, iyayensu da
duk sauran ‘yan uwa da abokan arziki. Duk saurayin da kika ce ya turo manya ya kama yi miki hanya-hanya to ki sani cewa akwai matsala a tare dashi.

4 A lokacin da kuka riga kuka tsayar
da wanda zaku aura to ku daina kula sauran samari, duk wanda
yazo kuce masa kuna da mijin aure, karku sake kuyi tunanin
zaku iya samun wanda yafi na farko, domin kuwa ko mutumin da
yafi kowa zama salihi ne yazo dalilin yaudarar wancan da kuka yi sai Allah ya debe albarkar abin koda anyi auren da sabon sai kuga ana ta samun matsala, babu wanda zai auri wani sai wanda Allah SWT ya rubuta a cikin Lauhil-Mahfuuz

2. Matsala ta biyu da mu samari muke da ita wacce muka yi
tarayya da mata a ciki shine ruwan
ido. Duk da dai namu ruwan idon yana da bambanci dana mata; su mata saboda saurayin ne zaizo yace yana so to ruwan idon nasu zasu jira nehar sai wani yazo, amma mu maza da yake mu muke zuwa
muce muna so to duk macen da muka ce tayi mana to fa hakanne. Yadda maza muke namu ruwan idon shine a lokacin da muka hadu da wata wacce ko dai take da wasu abubuwa na halitta da tafi na baya ko kuma wacce tafi iya kisisina,
rangwada, yanga da iyayi; to nan da
nan sai kuga ta qwace saurayin

3. YAUDARA: Akwai tambayarda take
yawo sosai a bangaren soyayya, wacce in dai za’a zauna
maganar soyayya to da wuya a gamata ba tare da anyi wannan tambayar ba, tambayar kuwa itace

A TSAKANIN MAZA DA MATA
WA YAFI YAUDARA?

Duk da dai kowa yana iya qoqarinshi
wajen ganin ya bayar da amsar wannan tambayar tare da hujjojinshi; amma ya kamata mu gane cewa dalilan da yake sa maza yaudara sun bambanta
da na mata! Kamar yadda muka fada
a baya cewa yawancin dalilan da suke sa mata yaudare basu wuce saboda abin duniya ba, su kuwa maza bayan kyau da tsarin siffar mace da
yakan sa su canja budurwa; wani babban abinda yake sa maza
yaudara shine SHA’AWA!!! Kasancewar sha’awar namiji tafi ta
mace nesa ba kusa ba yasa yawancin maza basa gane
banbancin SO da SHA’AWA. Bincike
ya nuna cewa mafi yawancin lokutan da namiji zai kalli
mace sai sha’awarsa ta
motsa, hakan yasa wani lokaci sai
namiji ya nutsa cikin kogin soyayyar mace amma bazai gane so ne
ko sha’awa ba har sai
zuwa ranar da ya santa ‘ya mace. Idan akayi rashin sa’a ya santa ‘ya mace kafin aure to a irin haka ne tunda dama sha’awace amma bai gane ba sai kawai yaji ta fita daga ranshi
tunda ya riga ya biyar buqatarsa da
ita, hakan yasa nake bawa
mata shawara a kullum cewa duk irin soyayyar da zasu yi da
namiji kar su sake su bawa namiji
kansu; saboda bayan sabon
Allah SWT da suka yi da rage kima da darajarsu a idon
saurayin to kuma akwai yiwuwar
saurayin zai gudu ya barki
tunda ya dandana romonki!!! Idan
kuma ya zamo shi wannan
saurayi mai yi miki son sha’awa ya
sai bayan ya aureki ne ya
sanki ‘ya mace, to anan ma mace
takan fita daga ran namiji tunda dai sha’awarce dama ta ja shi, a
irin haka ne zaku ga
kulawar da namiji yake bawa mace ta ragu, sai dinga cewa ko
ya daina sonta ne? SHAWARA: Shawara ta ga maza anan itace ya kamata mu gane cewa

DA HANKALI AKE ZABEN MATAR AURE BA DA ZUCIYA BA

abinda hakan yake nufishine karka biyewa macen da kaji kana sonta ba tare da kasan dalilin da yasa kake sonta ba, kamata yayi ka zauna kayi tunani ina son mace mai addini,
mai kama kai, mai tarbiyya, mai zuwa
M Islamiyya, mai iya karatun Qur’ani, to idan ya zama cewa dan haka ka zabe ta a matsayin mata to kulluma ka kalleta zaka ga cewa wadannan
abubuwan fa sunana, ko sau dubu
zaka kwanta da ita baza ka
iya goge mata wadannan dabi’u masu nagarta nata ba. Amma
idan ya zama cewa haka kawai kaji
kana sonta babu dalili to
lallai kyawunta da tsarin jikinta ne
yake burgeka, wato dai sha’awace, ta hakanne da anyi auren bayan kamar wata daya ka gama saninta waje da baya sai kuma kaga ai bata da wani
abu da ya rage da yake burgeka, sai kawai kaji ka daina sonta daga www.hausanet.ml

LABARAN SAYE DA SAYAR WAN YAN WASAN KWALLON KAFA TA DUNIYA


MAURO ICARDI YA JINKIRTA QARAWA INTER MILAN KWANTIRAGI.

A wasu rahotanni dake fitowa daga qasar Italy sun bayyanA cewar Babban Dan wasan gaban inter Milan wato Mauro icardi yaqi

yarda yaqarawa kungiyar tasa ta inter Milan
Milan kwantiragi sakamakon rade radin da akeyi Na komawarsa Real Madrid inda qungiyar tasa ta inter Milan ketsoron rasa Dan wasan nasu sakamakon sun bayyana release clause din Dan wasan da yakai £97.5m

(€110m) inda real Madrid din kuma ka iya
biyan wadannan maqudan kudaden saboda kudi. ba matsalarsu bane.
Dan wasan Dan qasar Argentina yaciwa Inter Milan din kwallaye 17 cikin wasanni 19 daya buga a wannan kakar

MAN CITY TA AMINCE TA SAYARWA REAL MADRID AGUERO BISA YARJE JENIYA DAYA.

Hukumar kwallon qafa ta Manchester city dake a England sunce sun amince su sayarwa da real Madrid Dan wqsan gabanta Dan qasar
Argentina wato Sergio aguero amma bisa sharadi guda. sharadin kuwa shine real Madrid din ta sayar mata da mai tsaron ragarta Dan qqqasar Costa Rica wato keylor navas sannan suma saisu saida musu da agueron wanda yabayyana qudirinsa nason koma Real Madrid saka makon rashin jin dadin da yakeyi a
qarqashin kochi pep guardiola.

FLORENTINO PEREZ YASHIRYA TATTAUNAWA DA TOTTENHAM SPURS AKAN DELLE ALLI.

Shugaban qungiyar kwallon qafa ta real Madrid wato Florentino Perez yace yashirya tattaunawa da Tottenham spurs kan daukar
matashin Dan wasan tsakiyarta wato Delle alli Inda Perez din yace yashirya gwabzawa da Manchester united kuma yayi waje road da ita
yakuma biya £177m akan Dan was an tun abaya dai Real Madrid din ta yi yunqurin daukar Dan wasan sai dai kochinta zinedine zidane ne yadatse wannan maganar sai dai
kuma yanzu Florentino Perez yadawo da wannan maganar a matsayinsa Na shugaban qungiyar ta real Madrid din

Saye Da Sayarwan Yan Wasan Kwallon Kafa na duniya na wannan makon

Kungiyar kwallon Kafa ta Mancester City tana shirin kammala cinikin dan wasan gefe daga kulob din Leicester City, mai suna Riyad Mahrez, mai shekaru 27 da    haihuwa akan kudi fam miliyan £75. Liverpool ta kara kaimi wajan sayen dan wasan
tsakiya kuma Kaftin a kungiyar Lyon, mai suna Nabil Fekir mai shekaru 24 a duniya bisa darajar kudi fam miliyan £60 wanda zasu fara
tattaunawa a satin da za a shiga kan

batun Manchester United, ta sa ido kan dan wasan tsakiya na kungiyar Aston Villa, mai suna Jack Grealish dan shekaru 22 a duniya, don ganin ta kawo shi kungiyarta. Napoli ta yi watsi da tayin kudi fam miliyan £39
wanda kungiyar Manchester City, ta yi akan dan wasan tsakiyarta mai suna Jorginho, inda ta bukaci a biya ta fam miliyan £52 kan dan wasan dan kasar Itali. Daraktan wasanni na kungiyar Kwallon Kafa ta AS Roma. ya ce babu wata kofa da zasu bayar

kan mai tsaron ragarsu mai suna Alisson mail shekaru 25, wanda ake alakant ashi da komawa kungiyar Liverpool. Dan wasan gaba na
Everton Wayne Rooney, ya fara tattaunawa da mahukuntan kungiyar Kwallon Kafa ta DC United, dake kasar Amurka kan batun komawarsa kulob din da taka leda a bana.
Manchester United, tana dab da kammala sayen dan wasan tsakiya na kungiyar Shakhtar Donestk, mai suna Fred, wanda ta ce tana da
karfin guiwar za'a kammala cinikin nan da sati mai zuwa. Manchester City, zata biya fam miliyan £60
wajan ganin ta cimma dogon burinta na sayen dan wasan gefe Leicester City, Riyad Mahrez, wanda tun a
watan janairu ta ke kokarin ganin ta kawo shi kulob din ta. Hausanet.ml

Saturday, 2 June 2018

SAKONA NA FARKO DANA KAIWA MASOYIYATA

Labarin ya fara ne a lokacin da Ina tsaye a bakin titi ina hangen mutane suna ta wucewa, wasu a mota wasu a mashina! Wasu kuma a kasa! Yayin da wasu ke tafe a adaidaita sahu, kai harma na kan ga masu
wucewa a kekuna Idanuna suna ta bin su da kallo kowane ina ta hangen inda zanga masoyiya ta, duk motar datawuce sai nayi tunanin masoyiya ta tana ciki! Duk mashin din da ya zo wucewa sai na zaci an goyo ta a baya! Idanuna suna ta leka adaidaita sahu a kokarin neman masoyiyata

Ban ganta ba! Kamar yadda dafin so
da tsananin kauna suka tunzuro hasashe na nake zaton zan ganta, kamar yadda zuciyata take ta hadamin haka. A bakin titi na wuni. Ina sake tuno wasu kalamai da masoyiyata take fada min Idan so ya dade a jikin mutum shigewa yake zuciya! Yana mulkata ba tare da sanin hanyar saita kai ba Na yarda. Na fara tunanin ko na fara tare jama'a ne ina fada musu sako zuwa ga masoyiyata Wata budurwa na tare na fara mata magana Ki taimaka ki tsaya zan baki sako Ta tsaya tana min kallon tara kwabo
"Dube ka tsami da kai zaka tare ni,
kar ka kuskura ka sake kuskuren aikata haka a wurina mtssssswwbullshit" Tayi gaba na tsaya ina kallonta maimakon naji haushi sai nayi murmushi wani farin ciki naji a raina ina tunanin dan bata san yadda naji dadi a raina bane, saboda masoyiyata aka yi min
haka, na kara tare wani gabjejen kato
ya kalle ni yana jiran yaji sakona
Ka jira ubanka yazo ka bashi sakon"
Ya ce dani a fusace bayan yaji magannan        ta, sannan ya juya ya
wuce yana hararta, ya dauka zanji haushi? Tab! Bai san farin.  ciki naji a raina akan an zageni saboda masoyiyata ba Wani dan acaba yazo wucewa na sa masa hannu yana tsayawa nayi masa magana Abunda basu sani ba akan masoyiyata
Bani da zuciya Bana fushi Ni jimirau ne Bana raggwanci Wa zan ba sakona ya kaiwa masoyiyata domin samun zafafan labaran soyayya kawai ka kasance damu ako yaushe

LA ILAHA ILLAL LAAH!! HAKIKA MUTUWA TANA DA RADADI!

MECECE MUTUWA? Daga Dr Ahmad Muhammad gumi

Hakika Fitan rai yana da wani irin radadi wanda babu mai saninsa sai dai Mamaci..

Mamaci yayin da ransa ya kusan fita, Muryarsa takan karye, Qarfin jikinsa yakan tafi.. Babu damar Eehu ko kururuwar zafin da yake ji. Domin zafin mutuwa ya riga ya ratsa dukkan sassan jikinsa..

Ba zai samu damar neman taimako ba, ballantana adauke masa zafin radadin da yake ji. Sai yayi fatan wannan nishin da yakeyi ko zai zama dalilun samun rangwame, amma inaa!!.

Idan har akwai ragowar wani Qarfi gareshi shine za'a rika jin wani irin gurnani yana fitowa daga chan cikin Qirjinsa da Makogoronsa yayin da rai yazo fita.. Alhali launin fuskarsa ya chanza saboda tsananin halin da yake ciki.

Yayin da ranka yazo Makogoro, awannan lokacin zaka manta da Makusantanka, iyalanka ko 'Ya'yanka, balle Makobta. Awannan lokacin ne 'Dan Adam yakan ji wata irin Qishirwa mai tsanani wacce sai ya gwammaci inama ya bayar da dukkan abinda ya mallaka domin a bashi ruwan da zai kurba koda kurbi guda ne!!.

A wannan lokacin duniya da dukkan abin cikinta zasu zamanto ba komai ba... Ballantana dukiya ko Mulki ko wani gata... 'Dan Adam zai gane cewa ashe shi ba komai bane.. Kuma tun daga sannan zai fara nadamar lokutan rayuwarsa da suka tafi wajen sa'bon Allah!!

Tunda Shugaban Halitta (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) ya 'dan'dana zafin mutuwa, Ka sani cewa kaima sai ka 'dan'dana!!

Imamul Bukhariy ya ruwaito daga Nana A'isha (rta) tana bayar da labarin jinyar da Manzon Allah (saww) yayi adakinta, har zuwa rasuwarsa. Tace :

"Hakika Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) ya kasance a gabansa akwai wata guga wacce akwai ruwa acikinta, yana shigar da hannayensa acikin ruwan sannan ya shafe fuskarsa dasu. Yana cewa :

LA ILAHA ILLAL LAAH!! HAKIKA MUTUWA TANA DA RADADI!

Sannan ya chira hannunsa sama yana cewa : "ACIKIN TAWAGA MADAUKAKIYA!''. (Alokacin an bashi za'bi ne tsakanin ci gaba da zaman duniya, ko kuma komawa zuwa ga Ubangijinsa).

Yana fa'dar haka har sai da aka karbi ransa sannan hannunsa ya karkato...

Annabi Muhammadu kenan (saww) Shugaban halittun Allah baki daya, wanda bai ta'ba sa'ba ma Allah ba. ballantana kai wanda kullum acikin sa'bon kake kwana kake tashi.

Lokacin da Amru bn Al-As (ra) yazo rasuwa, an tambayeshi shin yaya yake ji?.  Sai yace "Ji nakeyi tamkar sammai sun fa'do akaina, Qassai kuma sun matseni".

Sayyiduna Umar bn Al-Khattab (ra) ya tambayi Ka'abul Ahbari ya siffanta masa yadda mutuwa take. Sai yace : "Ya Kai Sarkin Muminai! Hakika ita mutuwa kamar wani reshe mai yawan Qayoyi ajikinsa, ashigar dashi cikin cikin mutum. Bayan kowacce Qaya ta rike wata jijiya daga jijiyoyin jikinsa, sai kuma a samo wani mutum Ma'abocin Qarfi, ya kama wannan reshen ya fizgoshi da Qarfi, ya fizgoshi kenan tare da tsoka da jijiyoyin jikin!!!.

Yanzu 'Yan uwa koda tunanin wannan ranar bai ishemu dalilin rage sa'bon Allah ba!!.

Wannan ranar fa sai ta riskeni, sai ta riskeka, sai ta riskeki, sai ta riskemu baki dayanmu kamar dai yadda ta riski wadanda suka rayu kafinmu.

Daga cikin abubuwan dake haddasa tsananin zafin fitan rai tare da gigicewa akwai :

- Wulakantar da Sallah.
- Wulakanta Mahaifa.
- Chutar da Manzon Allah (saww) ko iyalan gidansa da zuriyarsa ko kuma Sahabbansa (Radhiyallahu anhum).
- Cin Mutuncin Malamai Waliyyai da salihan bayin Allah.
- Shan giya ko Miyagun Kwayoyi.
- Cin haram (Cin hanci, wawure kudin gwamnati ko Kudin Marayu, ko Satar dukiyar jama'a, etc).
- Kisan rai ba tare da hakki ba.
- Zina, Luwadi, Madigo.

Ya Allah yasa mu cika da imani ya kiyayemu daga Mummunar mutuwa. Ameen.

Friday, 1 June 2018

SHIN HAR YANXU MUNADA MACE IRIN WANNAN?

SHIN HAR YANXU MUNADA MACE IRIN WANNAN?

Waya tayi ringing
(Matar ta dauka)

Matar: Hello Love.

Mijin: Yes Honey, ki shirya zamu fita yau.

Matar: Ina zamuje kuma ni 'yasu? bayan hakama ina busy yau.

Mijin: Ki bar duk abinda kikeyi ki shirya kawai yau rana ta musamman ce.

Matar: Alright Love.

Mijin: Sharp-sharp fa, nan da mintuna 30 ina xuwa.

Matar: Ok, bye.

Mijin: Cool (Sai ya kashe wayar)
...............

Cikin mintuna 30 ya iso gida kamar yadda yayi alqawari.

Mijin: Waye a gida??? (Kwan! Kwan! Kwan).

Matar: (Ta leqo ta windo), shigo honey a bude kofar take.

Mijin: Baby meye ke damunki ne? Bakifa shirya kanki ba har yanxu? 

Matar: Tabbass, bazan shirya ba har sai ka fadamin ina zaka kaini.

Mijin: yau kwanan wata nawane?

Matar: 30th of January.

Mijin: Great! Today is my pay day, bayan hakama nasamu Karin albashi, don haka Ina son naje na kashe miki sosai. Toh Shikenan, yi sauri maza kije kiyi wanka Sharp-sharp.

Matar: No my love, babu inda zanje tare dakai.

Mijin: meye kike nufi ne kam haka?

Matar: My love, I know you love me, ammana hakan bazai zamto dalilin dalilin da zai sanya kana 6arnata kudi a kaina sosai ba.

Mijin: meye ke damunki ne kam haka? Kefa mata tace, masoyiyata ta farko, kuma Uwar yaya nah, don haka inada duk daman da zan kashe kudi a kanki.

Matar: My love, last time naje gida naga qaninka an koroshi a makaranta saboda ba'a biya kudin makaranta ba. Kuma sanin kanka ne da Kai kadai duk xuriyar suke gadara. Wannan gidan da mama ke ciki (surukarta) ya tsufa yana buqatar gyara sosai lura da yadda ya lalace.

Mijin: (ya nutsu sosai yana sauraronta)

Matar: Maimakon ka kashe kudi a kaina, kayi amfani da albashin naka mana wajen biyawa wadanda suka dogara da sai ka musu domin gudanar da rayuwarsu. A wajena inaga wadannan mitane sune na farko, dadin dadawa ma bawai ina qaunarka bane saboda abun hannunka, ina qaunarka ne  a matsayin ka na nagartaccen namiji

Mijin: ammana  bae..........

Matar: (tayi sauri ta katse shi) But bae nothing, yi sauri maza kaje ka biya kudin makarantar qaninkannan, ka kuma tallafawa wadanda keda wata buqatar muhimmiya matuqar albashin naka zai isa. Idan ansamu wani abu ya saura, inyaso sai kazo gida musan yaya zamuyi mu fasaltashi. Maigida nake gani tattare da kai bawai Bank Account ba.

Mijin (sai yafara qwalla): meye kuma zan roqa daga wajen Ubangiji? Ya wadatani da mata tagari mai abun mamaki. I Love you so so much my wife, you are one in a million. Wallahi naga nagartacciyar mace tattare dake, bawai wata slut ba ko slay queens na wannan zamanin namu.

Matar: I love you too my husband.

Mijin: taho gareni (ya bude hannuwan shi domin su rungumi juna) suka rungume juna.

Mijin ya zauna da matar domin bashi wassu shawarwari akan yadda zaiyi su kashe Wadannan kudaden akan masu buqata.

*Wannan shine ake kira nagartacciyar soyayya*.

Abin tambaya anan shine:

*SHIN ANA SAMUN IRIN WADANNAN MATAN DAYAWA A NIJERIYA KUWA?*

*Idan macece ke kike karanta wannan saqon, yaya kika auna kanki? Meye kika shirya domin zamewa nagartacciyar mace wacce mijinta zai na shawara da ita koda a critical condition yake*

Be wise yake mai karatu,  Kiyi abinda yadace. Ki zamto mace mai nagarta da sanin yakamata.