Shararen jarumin Kannywood kuma
mawaki, Adam Zango, zai tafi kasar Faransa domin hallartan nadin sarauta da za'ayi wa wasu hausawa
mazauna kasar inda kuma ake sa ran zaiyi wasa a wajen taron
Masoya jarumin sunyi tururuwa zuwa shafinsa na dandalin sada zumunta na Instagram don taya shi murnar wannan karamci da akayi masa tare da yi masa fatan alkhairi.
Zango yana daya daga cikin jaruman
Kannywood da su kayi fice wajen
wakokin Hausa wanda hakan yasa wasu ke yi masa lakabi da 'Davido na Arewa inda suke kwatanta shi da shahararen mawakin Najeriya Davido Baya ga haka Zango ya sami nasarori
sosai a matsayinsa na jarumin fim da kuma mai shirya fina-finai. Wasu daga
cikin fina-finansa da su kayi farin jini sosai sun hada da Basaja da Gwaska.
A shekarar 2016, Zango ya samu rashin jituwa da jaruma Rahama Sadau inda su kayi ta musayar maganganu amma daga baya Sadau ta shaidawa majiyar hausanet.ml cewa tuni sun shirya da Zangon
I na murnar sanar da ku masoya na
cewa an gayyace ni zuwa nadin
sarauatan wasu muhimman mutane da hausawa mazauna kasar Faransa za su dauki nauyin gudanarwa . Ma Za'a karama mutane da dama daga
kasashen Kamaru, Chadi, Jamhuriyar
Congo, Ghana da kuma wasu kasashen turai kuma ina daga cikin wanda aka gayyata don inyi waka a wajen taron inji shi
No comments:
Write Please Share a Your Opinion.