Musha dariya
Wani dan fulani ne yaje kano yaga yara suna ta sayen sweetcamfo (alewar larabawa) sai abin ya
bashi sha'awa sai ya bada kudinsa a bashi,koda aka bashi ya saka ta (alewar) a bakinsa kun san yadda take sai ta narke ya neme ta ya rasa Sai yaji zaki ,budar bakinsa sai yace
SHEGU KANAWA SUN FARA SAIDA BABU
LABARIN DANFULANI
Wani bafullatani ne ya ga wani gida an yi masa farin fenti yana ta sheki, sai ya zauna ya fashe da kuka,
akayi akayi yayi shiru yaki. Da kyar aka samu ya daina kukan....
.Sai aka tambaye shi, wai bawan Allah mai ya saka kukan ne?
sai ya ce shi wallah I wulaqancin mutanen birni ne ya ishe shi. Yanzun su rasa da abinda zasu yi fenti sai da
KINDIRMO!!!!!(NONO)
Wasu fulanine su uku sun shigo birni sai suka ga ana wasa da biri suka tsaya suna kallo akace biri
yayi tafiyar Karuwa taga mai kudi Biri yai far da ido yana tafiya yana yanga da kwarkwasa kai kace wata tsohuwar karuwa a kai ta sanya shi yana kwaikwayon abubuwa daban daban yana yi aka ce
yayi tsallen kwado sai yayi sai Dan fulani yaji haushin biri yace yau ga shege. Sai akace biri yi zaman Dan fulani shanu sun kare
sai biri ya dauko sandaâ ya sa a kafadar shi ya lankwashe kafarsa Ya murtuke fuska ya zare ido ya
langabe kai jikin sanda, Dan fulani na ganin haka ya bushe da dariya ha ha
ha ha ha ya ce "Kwal uba Aradu kamar Baffa nah!!!"
By Dan Fulani
S!r A²
Angamu
Watarana wani Malami yana wa'azi yadda ake zama da mata sai yace ko wanne mai gida idan matarsa tayi girki idan yanaci yadinga cewa yayi dadi. Idan tayi kwalliya ya yaba. Dajin haka da Tanko yakoma gida da matar sa takawo abinci yafara ci sai yatuna da wa'azin Mallam. Sai yace kai amma abincinan yayi dadi. Yana fadin haka sai matar ta dauki murfin kwano ta kwada masa aka tace shekara ashirin muna tare baka taba cewa abincina yayi dadi ba sai da na karbo a makwobta
No comments:
Write Please Share a Your Opinion.