Naci kwalliyata me rai da motsi na shiryawa mijina abincinsa mai dadi na gyara gidana ko ina yadauki kamshi babu abin danake jira sai shi kadai chan gefe naji wayata na ringing Sunan brother dina nagani na danna nasa akunnena shashshekar kuka naji Ana ta fadin ina lillahi wainna ilaihirrajuun Meke faruwa dani jinayi yana fadi allah yayiwa
mama da baba rasuwa yanzunnan hatsarin mota sukayi dif wayar ta katsi ga shi saura minti kadan mijina Ya shigo sati biyu baya gari Yace min yakusa zuwa gida nan da minti goma shabiyar zai shigo gida haka na daure na Dan dai daita fuskata kawai jinayi Ya rungumeni my babyn na daure narungumesa nima nai mishi oyoyo na kaishi yayi wanka na daukomai kayan da zaisa jallabiya muka huce wajan cin abinci yagama sai yake tambayata yanaga Bana murna kamar dazu daya jini awaya Nace mai ka koshi yanxu mai kake bukata Yace min ni Nace kasamu na biya mai bukatarsa natabbatar Ya
gamsu sannan muna Dan hira sai nake gaya mashi dazu dab dazaka shigo aka bugo min waya Mamana da babana sun rasu to nikuma naga ka kusan zuwa shiyasa na danne zuciyata na baka hakinka yanzu sai mu tafi ko razana yayi yasa kuka mai tsanani nima nasa kuka Yace indai aljanna na wajena yabani duniya da lahira in kece zakiya haka
No comments:
Write Please Share a Your Opinion.