Mai horar da yan wasan Najeriya Gernot Rohr ya bayyana sunayen ‘yan wasan kasar 23 da zasu fafata a gasar cin kofin duniya da za’a
fara ranar 23 ga watan nan a Rasha.
Bayan karawar da kungiyar tayi da Ingila,
Rohr ya sauke ‘yan wasa biyu daga cikin 25 da ya tafi da su da suka hada da Ola Aina da Mikel
Agu. Wadanda suka samu shiga sun hada da masu
tsaron gida 3 da ‘yan tsaron baya 8 da ‘yan
tsakiyar fili 6 da ‘yan wasan gaba 6.
Sunayen masu tsaron gidan sun hada da
Ikechukwu Ezenwa da Daniel Akpeyi da Francis
Uzoho. Yan wasan baya sun hada da Wiliam Ekong da Leon Balogun da Kenneth Omeruo da
Bryan Idowu ad Chidozie Awaziem da Abdullahi
Shehu da Elderson Echiejile da Tyronne Ebuehi.
Yan wasan tsakiya sun hada da kaftin Mikel
John Obi da Ogenyi Onazi da John Ogu da
Wilfred Ndidi da Oghenekaro Etebo da Joel Obi.
Sai kuma yan wasan gaba da suka hada da
Odion Ighalo da Ahmed Musa da Victor Moses
da Alex Iwobi da Kelechi Ihenacho da Simeon
Nwankwo.
Najeriya zata kara da Croatia da Iceland da kuma Argentina a zagayen farko
No comments:
Write Please Share a Your Opinion.