. SAKONA NA FARKO DANA KAIWA MASOYIYATA - hausanet hausanet





Saturday, 2 June 2018

Home SAKONA NA FARKO DANA KAIWA MASOYIYATA

Subscribe Our Channel


Labarin ya fara ne a lokacin da Ina tsaye a bakin titi ina hangen mutane suna ta wucewa, wasu a mota wasu a mashina! Wasu kuma a kasa! Yayin da wasu ke tafe a adaidaita sahu, kai harma na kan ga masu
wucewa a kekuna Idanuna suna ta bin su da kallo kowane ina ta hangen inda zanga masoyiya ta, duk motar datawuce sai nayi tunanin masoyiya ta tana ciki! Duk mashin din da ya zo wucewa sai na zaci an goyo ta a baya! Idanuna suna ta leka adaidaita sahu a kokarin neman masoyiyata

Ban ganta ba! Kamar yadda dafin so
da tsananin kauna suka tunzuro hasashe na nake zaton zan ganta, kamar yadda zuciyata take ta hadamin haka. A bakin titi na wuni. Ina sake tuno wasu kalamai da masoyiyata take fada min Idan so ya dade a jikin mutum shigewa yake zuciya! Yana mulkata ba tare da sanin hanyar saita kai ba Na yarda. Na fara tunanin ko na fara tare jama'a ne ina fada musu sako zuwa ga masoyiyata Wata budurwa na tare na fara mata magana Ki taimaka ki tsaya zan baki sako Ta tsaya tana min kallon tara kwabo
"Dube ka tsami da kai zaka tare ni,
kar ka kuskura ka sake kuskuren aikata haka a wurina mtssssswwbullshit" Tayi gaba na tsaya ina kallonta maimakon naji haushi sai nayi murmushi wani farin ciki naji a raina ina tunanin dan bata san yadda naji dadi a raina bane, saboda masoyiyata aka yi min
haka, na kara tare wani gabjejen kato
ya kalle ni yana jiran yaji sakona
Ka jira ubanka yazo ka bashi sakon"
Ya ce dani a fusace bayan yaji magannan        ta, sannan ya juya ya
wuce yana hararta, ya dauka zanji haushi? Tab! Bai san farin.  ciki naji a raina akan an zageni saboda masoyiyata ba Wani dan acaba yazo wucewa na sa masa hannu yana tsayawa nayi masa magana Abunda basu sani ba akan masoyiyata
Bani da zuciya Bana fushi Ni jimirau ne Bana raggwanci Wa zan ba sakona ya kaiwa masoyiyata domin samun zafafan labaran soyayya kawai ka kasance damu ako yaushe