Kungiyar kwallon Kafa ta Mancester City tana shirin kammala cinikin dan wasan gefe daga kulob din Leicester City, mai suna Riyad Mahrez, mai shekaru 27 da haihuwa akan kudi fam miliyan £75. Liverpool ta kara kaimi wajan sayen dan wasan
tsakiya kuma Kaftin a kungiyar Lyon, mai suna Nabil Fekir mai shekaru 24 a duniya bisa darajar kudi fam miliyan £60 wanda zasu fara
tattaunawa a satin da za a shiga kan
batun Manchester United, ta sa ido kan dan wasan tsakiya na kungiyar Aston Villa, mai suna Jack Grealish dan shekaru 22 a duniya, don ganin ta kawo shi kungiyarta. Napoli ta yi watsi da tayin kudi fam miliyan £39
wanda kungiyar Manchester City, ta yi akan dan wasan tsakiyarta mai suna Jorginho, inda ta bukaci a biya ta fam miliyan £52 kan dan wasan dan kasar Itali. Daraktan wasanni na kungiyar Kwallon Kafa ta AS Roma. ya ce babu wata kofa da zasu bayar
kan mai tsaron ragarsu mai suna Alisson mail shekaru 25, wanda ake alakant ashi da komawa kungiyar Liverpool. Dan wasan gaba na
Everton Wayne Rooney, ya fara tattaunawa da mahukuntan kungiyar Kwallon Kafa ta DC United, dake kasar Amurka kan batun komawarsa kulob din da taka leda a bana.
Manchester United, tana dab da kammala sayen dan wasan tsakiya na kungiyar Shakhtar Donestk, mai suna Fred, wanda ta ce tana da
karfin guiwar za'a kammala cinikin nan da sati mai zuwa. Manchester City, zata biya fam miliyan £60
wajan ganin ta cimma dogon burinta na sayen dan wasan gefe Leicester City, Riyad Mahrez, wanda tun a
watan janairu ta ke kokarin ganin ta kawo shi kulob din ta. Hausanet.ml
Enter your comment...
ReplyDelete