Ashe haka so yake na A lokacin da na
Fara kallon ta tana tafiya
cikin nutsuwa, burgewa, da takun Isa, Sanye take cikin doguwan rigan material, kalan brown da milk, saita yafa k'aramin mayafi akai, tana rik'e da wasu littafai a hannunta. Bata ankara ba sai dai taji abu ya dakar mata goshi harta kusa faɗuwa, kafin ta ɗago kanta kawai taji an kwashe da dariya, cikin kaunar
zuciya ta ɗago da kanta tana k'arema wurin kallo, gaba ɗaya cike wurin yake da ɗaliban jami'ar kuma kusan duka hankalinsu na akanta. Dariyarshi tafi shigar mata kunne, juyawa tayi ta watsa mishi harara. Dariya yayi irinta gogaggun en iskannan, "zo mana" ya kirata da hannu, yana zaune saman motah da en korenshi zagaye dashi, taso ace zata iya komawa ta sauke mishi duk masifan dake ranta, anma jin kanta da tak'ama bazai taɓa barinta ba, kuma shi bai kai ajin da zata tsaya gaban mutane tana maida magana dashi ba. Juyawanta kawai tayi taci gaba da tafiyanta,
Batasan sanda ya diro daga saman motan ba, sai dai kawai taji yana neman rik'o hannunta, cikin zafin nama ta juyo ta wankeshi da marin da yazo mishi a bazata, ɗaga kanshi yayi yana kallon mutanen da sukayi cincirindo suna kallonsu, sannan kowa ya fara k'ok'arin riƙe dariyanshi don
babu wanda baisan halin Abdallah ba. "Ni kika mara?" "an mareka ɗin, wannan shine gargaɗin dazan maka na ƙarshe akan shiga harkata da
kake "ke kinsan waye Abdallah, wallahi sai kinyi dana sanin marina da kikai"
Anma bakasan wacece Rabi'ah ba, kuma ina mai baka shawaran karka zaƙe akan saika sani ɗin" Nunata yayi da ɗan yasha, "zan ramane a
inda zaifi miki ciwo, kuma ki sani ban taɓa son abu na rasa ba, ko bakiso dole kiyi soyayya dani" Tofar da yawu tayi a k'asa, "Allah ya kiyayemun soyayya da ɗan shaye-shaye" ta juya ta barshi wurin a tsaye yana huci yama
kasa maida mata magana, ya watsa ma mutanen wurin kallo ba shiri kowa ya ɓace, ya shige motanshi ya jata a guje. Hankalinta kwance ta gama lecturenta suka fito tare da Aminiyarta Amrah, hannunta taja suka koma gefe, "Faɗamin Rabi'ah meye gaskiyar abinda naji wai kin mari Abdallah" "toh meye naga duk kin wani ruɗe kaman wani babban abune ya faru?" haba Rabi'ah, naga hankalinki kwance kaman bakisan halin Abdallah ba" "ni mamaki kike bani wallahi, siyasa ne kawai zai nunamun, anma kuɗi kam har ke kinsan Yayana yafi mahaifinshi sosae, don haka duk abunda zaiyi nima zan iya, ban taɓayin abunda nayi dana sani ba
"hakane fa, anma ni dai duk a tsorace nake "kinma warware," Tun daga bakin gate, ma'aikatan gidan ke
kawo mishi gaisuwa anma ko kallo basu isheshi ba, ganin motoci da yawa ya tabbatar mishi Daddyn nashi na a ciki, don haka kai tsaye falon Mai girma mataimakin Governor ya wuce, Zaune yake yana amsa waya, bodyguards
nashi zagaye dashi, yana ganin yanayin da Abdallah ya shigo dashi, ba tare da yaa gama ba ya katse wayan.
"Yadai Son?" cikin sham ƙamshi ya kalli bodyguards ɗin, sannan ya maida kallonshi kan Dad din nashi, alama ya musu da su fito, cikin bin Umarni duk suka fita. waye kuma ya taɓomin kai?" Saida ya ƙara ɓata fuska sannan ya faravmagana, "Haba Dad! Ni bansan me yasa baka damu da abinda nakeso ba, ba ruwanka dani sai harkan siyasarka kawai" akwai abinda ka taɓa nuna kanaso banyi maka bane?" "A'ah kawai dai wannan ne nake tunanin
bazan samu ba babushi, indai Kuɗi da Mulki na iyayin komai a duniya babu abinda zaka nema bazanyi maka ba"I know Dad, but uh should promise me" "promise" thank you Dad,
i love you
Sannan ya fara fara'a, jinsa yake wasai kaman yama riga da yaa rama abinda Rabi'ah ta mishi
No comments:
Write Please Share a Your Opinion.