SHIN HAR YANXU MUNADA MACE IRIN WANNAN?
Waya tayi ringing
(Matar ta dauka)
Matar: Hello Love.
Mijin: Yes Honey, ki shirya zamu fita yau.
Matar: Ina zamuje kuma ni 'yasu? bayan hakama ina busy yau.
Mijin: Ki bar duk abinda kikeyi ki shirya kawai yau rana ta musamman ce.
Matar: Alright Love.
Mijin: Sharp-sharp fa, nan da mintuna 30 ina xuwa.
Matar: Ok, bye.
Mijin: Cool (Sai ya kashe wayar)
...............
Cikin mintuna 30 ya iso gida kamar yadda yayi alqawari.
Mijin: Waye a gida??? (Kwan! Kwan! Kwan).
Matar: (Ta leqo ta windo), shigo honey a bude kofar take.
Mijin: Baby meye ke damunki ne? Bakifa shirya kanki ba har yanxu?
Matar: Tabbass, bazan shirya ba har sai ka fadamin ina zaka kaini.
Mijin: yau kwanan wata nawane?
Matar: 30th of January.
Mijin: Great! Today is my pay day, bayan hakama nasamu Karin albashi, don haka Ina son naje na kashe miki sosai. Toh Shikenan, yi sauri maza kije kiyi wanka Sharp-sharp.
Matar: No my love, babu inda zanje tare dakai.
Mijin: meye kike nufi ne kam haka?
Matar: My love, I know you love me, ammana hakan bazai zamto dalilin dalilin da zai sanya kana 6arnata kudi a kaina sosai ba.
Mijin: meye ke damunki ne kam haka? Kefa mata tace, masoyiyata ta farko, kuma Uwar yaya nah, don haka inada duk daman da zan kashe kudi a kanki.
Matar: My love, last time naje gida naga qaninka an koroshi a makaranta saboda ba'a biya kudin makaranta ba. Kuma sanin kanka ne da Kai kadai duk xuriyar suke gadara. Wannan gidan da mama ke ciki (surukarta) ya tsufa yana buqatar gyara sosai lura da yadda ya lalace.
Mijin: (ya nutsu sosai yana sauraronta)
Matar: Maimakon ka kashe kudi a kaina, kayi amfani da albashin naka mana wajen biyawa wadanda suka dogara da sai ka musu domin gudanar da rayuwarsu. A wajena inaga wadannan mitane sune na farko, dadin dadawa ma bawai ina qaunarka bane saboda abun hannunka, ina qaunarka ne a matsayin ka na nagartaccen namiji
Mijin: ammana bae..........
Matar: (tayi sauri ta katse shi) But bae nothing, yi sauri maza kaje ka biya kudin makarantar qaninkannan, ka kuma tallafawa wadanda keda wata buqatar muhimmiya matuqar albashin naka zai isa. Idan ansamu wani abu ya saura, inyaso sai kazo gida musan yaya zamuyi mu fasaltashi. Maigida nake gani tattare da kai bawai Bank Account ba.
Mijin (sai yafara qwalla): meye kuma zan roqa daga wajen Ubangiji? Ya wadatani da mata tagari mai abun mamaki. I Love you so so much my wife, you are one in a million. Wallahi naga nagartacciyar mace tattare dake, bawai wata slut ba ko slay queens na wannan zamanin namu.
Matar: I love you too my husband.
Mijin: taho gareni (ya bude hannuwan shi domin su rungumi juna) suka rungume juna.
Mijin ya zauna da matar domin bashi wassu shawarwari akan yadda zaiyi su kashe Wadannan kudaden akan masu buqata.
*Wannan shine ake kira nagartacciyar soyayya*.
Abin tambaya anan shine:
*SHIN ANA SAMUN IRIN WADANNAN MATAN DAYAWA A NIJERIYA KUWA?*
*Idan macece ke kike karanta wannan saqon, yaya kika auna kanki? Meye kika shirya domin zamewa nagartacciyar mace wacce mijinta zai na shawara da ita koda a critical condition yake*
Be wise yake mai karatu, Kiyi abinda yadace. Ki zamto mace mai nagarta da sanin yakamata.
Enter your comment...very nice
ReplyDelete