Kurakurai :
1- A cikin kotu lokacin da alkali yace ya
janye shari’ar Mariya (Maryam Yahya)
akan cewar an yi mata afuwa kuma
kotu ta wanke ta, ya dace ace an ga
matsanancin farin ciki a fuskar
Abdullahi (Umar M Sharif) amma
fuskar sa a murtuke babu alamar
murna duk da irin son da aka nuna
yana yi mata.
2- Jarumin fim din Abdullahi ba shi da
abinda ake cewar “action” a turance
ma’ana kazar-kazar a aikace, sanyin sa
yayi yawa domin akwai abubuwan da
ya dace ya nuna zafin sa akan su
saboda son da yake yiwa Mariya amma
bai yiba.
3- An ga Kawu Bala ya fadi ‘kasa bayan
sun gama rigima da mahaifiyar Mariya,
shin mutuwa yayi ko suma? Sannan
kuma menene sanadin hakan? Domin
shine wanda bashi da gaskiya kuma
shine yaci zarafin ta balantana ace
sanadin abinda tayi masa ne yasa
zuciyar sa ta buga, shin hakki ne ya
kama shi ko me? Ya kamata a wayar da
kan me kallo
4- Wakokin fim din sun yi barkatai,
domin da yawa daga cikin su basu sami
muhalli ba kawai sako su aka yi
5- A kotu an ga su Yawale suna
hauragiya duk da tsari da doka irin ta
kotu amma ba’a ga an tsawatar musu
ba, ya dace a nuna musu cewar kotu fa
ba ‘kauye bace ballantana suyi abinda
suka ga dama a kyale su
6- Kauyen da suke ciki mai suna kukan
ka banza an nuna ‘kauye ne ‘kayau
amma wayewar mutanen garin da
lafuzan su sam babu ‘kauyanci a ciki,
hakan yafi kama da wadanda suke
cikin tsakiyar birni.
wannan gaskiya ne
ReplyDeleteToh Allah yatakaita gabah
ReplyDelete