Lionel Messi na Barcelona ya fara gasar
zakarun Turai a bana da cikakken karsashi, lura da kwallaye uku da ya zazzaga a wasan da suka lallasa PSV Eindhoven da ci 4-0 a
ranar Talata
Bayan jefa kwallon ta uku, abokan wasansa sun rufe shi saboda murna, yayin da magoya bayansa suka yi ta wake-waken kiran sunansa, in da kuma kocinsa, ya bayyana shi a matsayin
wani abu da ba a taba gani ba cikin tsawon
shekaru.
A karo na takwas kenan da Messi ke zura kwallaye uku-uku a wasannin zakarun Turai, in da ya zarce babban abokin hamayyarsa na Juventus Christiano Ronaldo , wanda ya zura
kwallaye uku-uku har sau bakwai a wasannin na
gasar zakarun Turai.
Ana iya tuna wayadda Messi ya gaza kai
tawagar kasarsa ta Argentina ga gaci a gasar cin kofin duniya a Rasha, yayin da Roma ta yi waje da su a gasar zakarun Turai a bara,
abin da bisa dukkan alamu ya bakanta ran gwarzon dan wasan, musamman idan aka yi la'akari da
jawabin da ya yi wa magoya bayansa a Camp
Nou.
No comments:
Write Please Share a Your Opinion.