Spain ta sha kashin ne da kwallaye 3-2, in da Raheem Sterling ya zura kwallaye biyu a minti na 16 da kuma 38, yayin da Marcus Rashford ya jefa tasa kwallon a minti na 29. Ana minti na 58 ne, Paco Alcacer na Spain ya barke kwallo guda kafin daga bisani Sergio Ramos shi ma ya jefa guda a minti na 97. Raban da Ingila ta samu nasarar akan Spain tun
shekarar 1987,
lokacin da ta doke Spain da kwallaye 4-2. Ana kallon wannan nasarar a matsayin mafi kayatarwa da Ingila ta samu a karkashin kocinta, Gareth Southgate.
A karon farko kenan da Sterling ke ci wa
Ingila kwallo tun shekarar 2015 kimaninn
kwanaki 1102, a yayin wata karawa da
Estonia.
No comments:
Write Please Share a Your Opinion.