. Wata matar aure: Sa'adatu Musa a jihar Nasarawa ta kai karar mijinta kotu - hausanet hausanet





Saturday, 27 October 2018

Home Wata matar aure: Sa'adatu Musa a jihar Nasarawa ta kai karar mijinta kotu

Subscribe Our Channel




Ita dai Matar ta yi ikirarin cewar mijin yana kwaracewa shimfidar ta har ta kai ga sau daya ya ke kusantar ta cikin watanni hudu Sa'adatu ta roki kotu ta raba aurensu da mijinta, Dembe domin ta ce ba za ta iya zama da mijin da         ba zai iya biya mata bukatunta na kwanciyar aure
ba Wata matan aure mai suna

Sa'adatu Musa ta.     shigar da kara Kotun Mararaba da ke       Jihar Nasarawa inda ta bukaci a raba
aurenta da mijinta, Dembe saboda kaurace wa shimfidar ta da ya ke yi. Sa'adatu ta yi korafin cewa mijinta baya bata hakkinta na kwanciyar aure inda ta ce sau daya kawai ya kwanta da ita cikin watanni hudu
Ta ce saboda irin wannan halin na ko
in kula da mijinta ke nuna wa game da hakkinta na aure, kwata-kwata ba ta samun gamsuwa da natsuwa cikin auren. Sa'adata ta fadawa kotu cewar da auri Dembe ne a shekarar 2015 amma har zuwa yau ba su
samu bai basu haihuwa ba ta roki kotu da raba aurensu inda ta kara da
cewar babu wani sauran soyaya
tsakaninsu. Ta ce babu yadda za su cigaba da zaman aure tare tunda baya iya biya mata hakkinta na
kwanciyar aure Sai dai mijinta Dembe ya musanta dukkan wannan zargin ta da ke masa. Alkalin kotun, Mr Ibrahim Shekarau ya dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 29 ga watan Oktoba domin bawa ma'auratan damar yin sulhu