GA TARIHIN (EL CLÀSICO)
REAL MADRID VS BARCELONA KU BIYUNI
DOMIN JIN YADDA TARIHIN ZAI KAYA
El Clásico lakabi ne da ake yiwa wani
shahararren wasa a bangaren kwallon kafa, wannan wasa shine wasan da yafi kowanne wasa daukar hankalin masu sha'awar kwallon kafa a duniyar
Wannan wasa shine tsakanin shahararriyar kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid CF data fito
daga Madrid babban birnin kasar Spain. Da kuma babbar kungiyar FC Barcelona data fito daga Barcelona babban birnin Catalonia dake kasar Spain.
Wadannan kungiyoyi guda biyu sune suka fi kowace kungiya samun nasarori a bangaren kwallon kafa a kasar Spain baki daya.
El Clasico shine wasa mafi daukar hakalin mutane a duniya, domin mutane sama da 100 milliyan suna ganin shi daga kasashen daban- daban a fadin duniya, ciki har da kasarmu Nigeria.
El Clásico ya samo asalin sunansa ne a lokacin da Real Madrid ta samu gagarumar nasara akan Barcelona a wasan kusa da karshe na gasar
Spanish Cup.(11-1) a shekarar 1943.
Real Madrid da Barcelona sune suka fi kowace kungiya magoya baya a kasar Spain.
Real Madrid tana da kaso 32.8%. Sannan
Barcelona na da kaso 25.7%. Sai ta ukun su Valencia da kaso 5.3% Sai ta hudu Atlético Madrid da kaso 5. 3% Game da kidayar da akayi a Shekarun baya.
ADAWAR BARCELONA DA REAL MADRID
Tsananin gaba Ta Kara Kamari tsakanin
Barcelona da Real Madrid, tun bayan hijirar da Figo ya yi zuwa Madrid.
Sai kuma ya kasance takun wasan Barcelona ya sha bamban da na sauran kungiyoyin kwallo na duniya, inda su, su ka fi bayar da karfi wajen kwarewa kan iya ba-ni-in-ba-ka ta kurkusa. Yayin
da su kuma Madrid, gogaggu ne wajen iya zari- ruga da kuma cilla wa dan wasa kwallo ya tare a duk iyar nisan sa, sai kuma maida hari kan abokan adawa da hanzari, wato counter attack.
Kwarewar takun wasan kungiyoyin biyu ya sa masana kwallo, masu sharhi da manyan ‘yan jaridu na duniya su ka sa wa kowace haduwa za su yi, sunan wasan El-clasico, watau, wasan
gwanaye ko taurarin da duniya ke ji da su.
An sha yin kare-jini, biri-jini a baya, idan
kungiyoyin biyu sun hadu.
Tsakanin Real Madrid da Barcelona an hadu sau 176 a gasar La-liga.
Real Madrid ta samu nasara sau 72. Sannan Barcelona ta samu nasara sau 70, Sunyi kunnen doki sau 35 a tsakaninsu.
{{{A gasar Zaka rukarun turai Champion league Kuma An Hadu Sau 8}}}
Real Madrid ta samu nasara sau 3
Sannan Barcelona ta samu nasara 2
, Sunyi kunnen doki sau3 atsakaninsu.
{{{Copa del Rey An Buga Wasa 34}{}
Real Madrid Ta Samu NasaraSau 12
Barcelona Ta Samu Nasara Sau 15
Sunyi kunnen doki sau 7 atsakaninsother competitions*An Hadu Sau 20 ,
Real Madrid Ta Samu NasaraSau ,8
Barcelona Ta Samu Nasara Sau 6
Sunyi kunnen doki sau 6
Tsakanin Real Madrid da Barcelona Aduk Haduwa an hadu sau 238
Real Madrid ta samu nasara sau 95
Barcelona Ta Samu Nasara Sau 93
Sunyi kunnen doki sau 50*
Yan wasan da suka fi cin kwallaye a El Clásico sune
Rank Player Club Goal
1 Lionel Messi Barcelona 26
2 Alfredo Di Stefano Real Madrid 18
3 Cristiano Ronaldo Real Madrid 18
4 Raul Real Madrid 15
5 Cesar Rodriguez Barcelona 14
6 Francisco Gento Real Madrid 14
7 Ferenc Puskas Real Madrid 14
8 Santillana Real Madrid 12
9 Hugo Sanchez Real Madrid 10
10 Juanito Real Madrid 10
11 Josep Samitier Barcelona/ Real Madrid 10
12 Karim Benzema Real Madrid 9
El Clásico wasan daya wuce a Santiago Bernabeu, Real Madrid 2 - 2 Barcelona, Ranar 24/10/2018 El Clásico wasan da za'ayi na Gobe a Camp Nou Barcelona - Real Madrid. Time Karfe 4:15pm Ranar Lahadi 28 october 2018
GA TARIHIN YADDA SÅKÃMÅKÕÑ YA KASANCE YI SHĀRHÏ KO GYARA
KO KARIN BAYANI
No comments:
Write Please Share a Your Opinion.