Europa League
AEK Larnaca 1 - 1 Ludogorets Razgrad
FC Zuerich 3 - 2 Bayer Leverkusen
RasenBallsport Leipzig 2 - 0 Celtic
Salzburg 3 - 0 Rosenborg
FC Koebenhavn 0 - 1 Slavia Prague Zenit St.
Petersburg 2 - 1 Bordeaux
Anderlecht 2 - 2 Fenerbahce
Spartak Trnava 1 - 2 Dinamo Zagreb
Qarabag FK 0 - 1 Vorskla
Sporting CP 0 - 1 Arsenal
Milan 1 - 2 Real Betis
F91 Dudelange 0 - 2 Olympiacos
Rangers 0 - 0 Spartak Moscow
Villarreal 5 - 0 Rapid Wien
*
*
Eintracht Frankfurt 2 - 0 Apollon
Marseille 1 - 3 Lazio
*
*
Besiktas 2 - 4 Genk
Sarpsborg 08 1 - 1 Malmoe FF
*
*
Sevilla 6 - 0 Akhisarspor
Standard Liege 2 - 1 FC Krasnodar
Jablonec 1 - 1 FC Astana
Rennes 1 - 2 Dynamo Kyiv
Chelsea 3 - 1 BATE Borisov
Thessaloniki FC 0 - 2 Vidi FC
Duk Da Ba Messi Da Ronaldo Wasan “Clasico”
Zai Kayatar
Wasan da yafi kowanne girma da daukar hankali
a gasar La Liga shine wasa tsakanin kungiyar
Barcelona da Real Madrid, a shekarun baya ‘yan
wasan kungiyoyin biyu sun zama fuskar wasan
na Clasico a duniya, inda kowanne daga cikinsu
yake nuna irin tashi bajintar.
A wannan shekarar wasan zai dauki sabon salo,
saboda babu Ronaldo na kungiyar Real Madrid,
sannan babu Messi na kungiyar Barcelona,
Ronaldo ya bar Madrid zuwa Juventus ta kasar
Italiya, shi kuma Messi ya samu rauni inda zai yi
jinya ta kimanin makonni uku zuwa hudu.
Duk da haka, manazarta sun ganin wasan zai
kayatar kamar yadda aka saba, saboda ‘yan
wasan kungiyoyin biyu zasu nuna bajintar su
yadda ya dace, ko da babu zakarun guda biyu,
sannan suma magoya bayan kungiyoyin biyu a
shirye suke su nuna wa duniya yadda
kungiyoyinsu biyu zasu kaya, musamman a
shafukkan sada zumunta.
Dukka kungiyoyin biyu suna fuskantar kalubale a
wannan kakar wasan ta 2018 zuwa 2019, sannan
dadin dadawa, rashin zakarun ‘yan wasan
kungiyar biyu zai iya baiwa wasan fata fuska ta
daban, wato sabanin wacce aka saba sanin
wasan na ‘Clasico’ da shi.
Masu kungiyar kwallon kafa ta Manchester sun
gargadi kociyan kungiyar bisa halayensa marasa
kyau dayake nunawa a cikin fili.
Hukumar kula da kwallon kafa ta kasar Ingila FA
dai tana tuhumar Mourinho ne dai laifin karya
doke bayan da kungiyarsa tasamu nasara akan
kungiyar kwallon kafa ta Newcastle daci 3-2 a
farkon wanna watan.
*
*
*
*
*
Har ila yau Mourinho yana cikin hatsaniyar da
akayi a filin wasa na Stamford Bridge a wasan da
kingiyar ta buga 2-2 da kungiyar kwallon kafa ta
Chelsea a satin daya gabata bayan da Chelsea ta
farke kwallonta ta biyu.
*
*
*
*
*
Tuni dai rahotanni suka bayyana cewa iyalan
Glazer sun bayyana rashin jin dadinsu bisa
halayen Mourinho dayake nunawa wanda yake
ragewa kungiyar daraja a idon duniya kuma suka
gargadeshi da rage faruwar hakan anan gaba.
*
*
*
*
*
Har ila yau masu kungiyar kungiyar sun gargadi
Mourinho akan kada yaci gaba da cacar baki da
tsohon dan wasan kungiyar, Paul Scholes wanda
yake yawan sukar Mourinho da salon yadda
kungiyar take buga wasa.
*
*
*
*
*
*
A cewar masu kungiyar, cece kuce da manyan
kuma tsofaffin ‘yan wasan kungiyar irinsu Paul
Scholes zai iya jawowa kan magoya bayan
kungiyar ya rabu saboda har yanzu sunada
magoya baya a kungiyar
Muhammad Salah Ya Kafa Tarihi A Liverpool *
*
*
*
Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta
Liverpool Muhammad Salah ya karya tarihin zura
kwallo 50 a raga a kungiyar bayan ya zura
kwallaye biyu a wasan da kungiyar ta buga na
gasar zakarun turai.
*
*
*
*
Duk da rashin fara kokari a farkon kakar
wasannin ta bana, dan wasan gaba na kungiyar
kwallon kafa ta Liverpool Mohammed Salah
yanzu haka za’a iya cewa ya gano bakin zaren.
*
*
*
*
Salah dai ya gamu da matsalar rashin kokari a
kakar wasannin bana ,wanda har wasu na cewa
tabbas ba zai iya abin da yayi a bara ba na cin
kwallaye masu yawan gaske shi kadai.
*
*
*
*
Amma sai dai duba da yadda ya zura kwallo
guda a wasan su da ya gabata na gasar Firimiya
da kuma la’akari da kwallaye biyun da ya zura a
ranar Laraba a gasar zakarun nahiyar Turai, ana
iya cewa ya gano sirrin saboda haka za’a cigaba
da suya daga nan har zuwa tsakiyar kakar
wasanni ta bana don a tabbar zai sake cimma
irin nasarar da yayi bara.
*
*
*
*
“Na yi farin ciki da wannan mataki na zura
kwallaye dana taka a kungiyar mai girma kamar
Liverpool kuma ina fatan zan dora daga inda na
tsaya domin ganin mun samu abinda mukeso a
wannan kakar.
*
*
*
*
A kakar wasansa ta farko dai Salah ya zura
kwallaye 44 cikin wasanni 56 sai dai a wannan
kakar kawo yanzu ya zura kwallaye shida ne
cikin wasanni 13 daya bugawa kungiyar
MUNA CIKIN MAWUYACIN HALI MARAR KYAU
AMMA ZA MUYI IYA IYAWARMU DOMIN KARE
MARTABAR
MADRID INJI CASEMIRO*
*
*
*
*
*
Dan wasan tsakiyar kungiyar kwallon kafa ta Real
Madrid, Casemiro, ya bayyana cewa kungiyar
tana cikin wani hali mara kyau duk da cewa sun
samu nasara a wasan da suka buga a gasar cin
kofin zakarun turai daci 2-1 akan kungiyar
Biktoria Plzen.
*
*
*
*
Kungiyar wadda itace take rike da kambun gasar
dai ta buga wasanni shida a baya inda bata samu
nasara a wasanni hudu ba halin dayasa kungiyar
cikin rudani sakamakon rashin samun nasarori.
*
*
*
*
A wasa na gaba da kungiyar zata buga shine
wasan da zata kai ziyara gidan kungiyar kwallon
kafa ta Barcelona, wasan da za’a fafata shi a
ranar Lahadi kuma ana ganin idan har kungiyar
tayi rashin nasara kociyan kungiyar zai iya rasa
aikinsa.
*
*
*
*
“Magana ta gaskiya bama cikin yanayi mai kyau,
yakamata mu gayawa kanmu gaskiya amma
kuma dole sai mun girmama ‘yan wasan
kungiyarmu da mai koyarwa sannan kuma mu
sake dagewa” in ji Casemiro Yaci gaba da cewa
a kwallon kafa komai yana iya faruwa rashin
nasara ko kuma nasara kawai dai abinda
yakamata suyi shine su yarda da kansu kuma su
yarda komai zai iya yiwuwa a wasa.
*
*
*
*
Real Madrid dai a yanzu maki hudu ne tsakaninta
da Barcelona wadda take a mataki na daya kafin
buga wasan hamayyar na sati mai zuwa kuma
kungiyar zatayi iya yenta domin ganin tabawa
Barcelona mamaki har gida
*
*
*
Mai koyar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa
ta Kano Pillars, Ibrahim Musa ya bayyana cewa
‘yan wasan kungiyar sun koyi darasi daga abinda
yafaru a wasan kungiyar na karshe da kungiyar
kwallon kafa ta Enugu Rangers a ranar Laraba
*
*
*
*
Kungiyar kwallon kafan ta Rangers ta zamo
zakara ne bayan da aka tashi wasa 3 da 3 inda
Kano Pillars ne suka fara jefa kwallayensu guda
uku kafin atafi hutun rabin lokaci ta hannun ‘yan
wasa Rabiu Ali Pele da Ibrahim Alhasan da
Nwagua Inda daga bisani Enugu Rangers ta farke
wadanan kwallaye bayan andawo daga hutun
rabin lokaci.
*
*
*
*
A bugun daga kai sai mai tsaron gida ne Rangers
din ta sami nasara daci 4 da 2 kuma wannan
shine karo na 6 da kungiyar kwallon kafan ta
Enugu Rangers ta lashe wannan gasa bayan da
kungiyar ta lashe a shekarun 1974 da 1975 da
1976 da 1981 da 1983 da kuma 2018 dinnan da
muke ciki.
*
*
*
*
A yanzu haka ta tabbata kungiyar kwallon kafa
ta Enugu Rangers ce zata wakilci Najeriya a
gasar Confederation cup ta nahiyar Afrika da
za’a fafata ta gaba
*
*
*
*
“Tabbas munyi abin kunya tabbas saboda munyi
sake kuma abinda bai kamata ba kenan amma
kuma munyi koyi darasi daga wasan kuma nan
gaba dole sai mun kiyaye da irin wannan
sakacin” in ji kociyan kungiyar ta Kano Pillar
*
*
*
*
Kano Pillars dai bata taba lashe gasar cin kofin
kalubale ta Aito Cup ba a tarihi kuma wannan ne
karo na farko da kungiyar tasamu nasarar zuwa
wasan karshen
‘Manchester United Ba Za Su Iya Cin Komai Ba’
A Wannan Kaka Inji Tsohon
Dan wasanta Phil Nebille
*
*
*
Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta
Manchester United, Phil Nebille ya bayyana cewa
kungiyar kwallon kafa ta Manchester United
bazata iya cin kowanne kofi ba a wannan kakar
duba da irin kwallon da kungiyar take bugawa.
*
*
*
*
Tsohon dan wasan yace yakamata kungiyar ta
manta da maganar lashe kowacce irin gasa ta
mayar da hankali akan neman tikitin zuwa gasar
hakan yana nufin ta koma neman zama cikin ‘yan
hudun faro na gasar.
*
*
*
*
Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United dai
tasha kashi a hannun kungiyar kwallon kafa ta
Jubentus hakan ya nuna cewa har yanzu
kungiyar bata kama kafar manyan kungiyoyi ba a
duniya.
*
*
*
*
“Yakamata su fara mantawa da lashe gasar cin
kofin zakarun turai ko gasar firimiya domin
karfinsu bai kaiba kawo yanzu indai kungiyar
Jubentus zataso tayi musu irin wannan dukan a
gida’ in ji Phil Nebille
*
*
*
*
Ya ci gaba da cewa “Yanzu abinda yakamata
Mourinho da ‘yan wasan kungiyar suyi shine su
dage wajen ganin sun kammala gasar firimiya a
matsayi na uku ko na hudu shine kawai abinda
zasu iya su fita kunya”
*
*
*
*
*
Manchester United dai zata buga wasa na gaba
da kungiyar kwallon kafa ta Eberton a gasar
firimiya a ranar Asabar kuma bayan ta buga 2-2
da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea a satin daya
gabata.
ZAMU SHA WAHALA A WASANNMU DA REALMADRID INJI COACH DIN BARCELONA BALBERDE*
*
*
*
*
Mai koyar da kungiyar kwallon kafa ta Barcelona,
Enestor Balberde, ya bayyana cewa tabbas akwai
wasa mai wahala a gabansu a wannan satin
yayinda suke shirin karbar bakuncin kungiyar
kwallon kafa ta Real Madrid a ranar Lahadi.
*
*
*
*
Barcelona dai tasamu nasara akan kungiyar
kwallon kafa ta Inter Millan daci 2-0 a gasar
zakarun turai yayinda itama kungiyar kwallon
kafa ta Real Madrid ta samu nasara akan
kungiyar Biktoria Plzen kafin karawar tasu a filin
wasa na Nou Camp.
*
*
*
*
Sai dai mai koyar da ‘yan wasan kungiyar kwallon
kafa ta Real Madrid aikinsa yana cikin hatsari
bayan da kungiyar ba ta samun nasara a
hannunsa matakin dayasa ake ganin idan sukayi
rashin nasara a hannun Barcelona zai iya rasa
aikinsa.
*
*
*
*
“Real Madrid zasufi Inter Millan hatsari a
gabanmu domin zasu fito kwansu da
kwarkwatarsu domin gani sun samu nasara
batare da la’akari da halin da suke ciki ban a
rashin samun nasara”
*
*
*
*
in ji kociyan na Barcelona Ya ci gaba da cewa
“Mun nuna cewa zamu iya buga wasa babu
Messi duk da cewa babban dan wasane a
wajenmu amma mutane sun zuba ido suna jiran
suga yadda zamuyi da Inter Millan yanzu kuma
zasu jira wasanmu da Real Madrid”
*
*
*
*
Messi dai bazai buga wasan ba bayan yaji ciwo a
satin daya gabata a wasan da kungiyar tasamu
nasara akan kungiyar kwallon kafa ta Sebilla daci
4-2 a satin daya gabata sai dai dan wasa Rafinha
yam aye gurbinsa kuma har ya zura kwallo a
ragar Inter Millan din
*
*
*
RÊÅL MADRID TA FARA ZAWARCIN ANTONIO
CONTE GADANGADAN DOMIN JIRA TAKE TAGA
KUSKURE KADAN TA SALLAMI KOCIYANTA *
*
*
*
*
Rahotanni daga kasar Sipaniya sun bayyana cewa
kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta fara
tattaunawa da tsohon kociyan kungiyar kwallon
kafa ta Chelsea, Antonio Conte, domin ya maye
gurbin kociyan kungiyar Julian Lopetegui.
*
*
*
*
Tun bayan daya fara koyar da ‘yan wasan
kungiyar dai kungiyar tafara buga wasanni batare
da samun nasara ba yayinda kungiyar tafara
shan kashi a hannun kungiyar kwallon kafa ta
Atletico Madrid daci 4-2 a gasar cin kofin Super
Cup.
*
*
*
*
Kawo yanzu dai kungiyar ta buga wasanni shida
inda bata samu nasara a cikin guda hudu ba
hakan yasa aka fara rade radin cewa kungiyar
zata iya korar kociyan dan asalin kasar Sipaniya.
*
*
*
*Ana tunanin idan kungiyar kwallon kafa ta Real
Madrid tayi rashin nasara a hannun abokiyar
hamayyarta ta Barcelona a wasan da zasu fafata
a ranar Lahadi abune mai wahala kungiyar taci
gaba da zama da mai koyarwar.
Tuni dai aka bayyana cewa shugaban gudanarwar
kungiyar, Florentino Perez, ya tattauna da
wakilan mai koyarwa Antonio Conte domin ganin
sun shirya idan har ta tabbata kungiyar zata
dauki sabon kociya.
Kawo yanzu dai Conte yana rikici da kungiyar
kwallon kafa ta Chelsea bayan da kungiyar ta
koreshi kuma bata biyashi wasu daga cikin
hakkokinsa ba inda a kwanakin baya aka bayyana
cewa tsohin kociyan Jubentus din zai kai
kungiyar Kotu
Nasiha itace kashin-bayan addini, domin addinin
gaba dayan shi nasiha ne, kuma nasiha tana
kasancewa ne ga Allah, da manzonsa, da
shuwagabannin musulmi, da gama-garinsu.
Dukkan sanda mutum yayi nasiha game da
wadannan abubuwa, ta addini ya cika, kuma duk
wanda yayi sakaci wajaen nasiha ga wani cikin
wadannan abubuwa, to haqiqa addininsa ya samu
tawaya gwargwadon sakacinsa.
Don haka wajibi ne musulmi ya lura da amana
wajen nasihar da ze gabatar, da bayanin gaskiya
ba tare da yin kara ba ga kowaye, domin shi
yana cikin kariyar Allah.
Ya Allah Kasa Mu Dace Sannan Allah Ya Karbi
ibadun Mu Badan Halin Mu Ba
INA YUWA KUWA BARKA DA JUMA'AT
KAREEEEE
No comments:
Write Please Share a Your Opinion.