. hausanet hausanet





 

Friday, 15 February 2019

Yanzu-yanzu: Da yiwuwan a daga zaben gobe, INEC ta shiga ganawar gaggawa da masu ruwa da tsaki

Hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC tana cikin ganawar gaggawa da jami'an tsaro, masu lura da zabe da wasu masu ruwa da tsaki kan zaben da za'a gudanar. Game da wata majiya daga cikin ganawar, da yiwuwan abubuwa su canza bayan ganawar.

Ko sama ko kasa: An nemi kuri'un kananan hukumomi 2 an rasa a Neja

A yau, Juma'a ne Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta INEC a jihar Neja ta ce akwai

yiwuwar ba za a gudanar da zabukkan sanata a mazabun Neja ta Arewa da Neja ta Kudu ba a ranar Asabar saboda kuri'un zabe da aka tanadar domin mazabun sun bace. Bataren zabe na jihar, Farfesa Samuel Egwu ne ya bayyana hakan yayin da ya ke jawabi ga manema labarai a garin Minna.

Ko sama ko kasa: An nemi kuri'un kananan hukumomi 2 an rasa a Neja

A yau, Juma'a ne Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta INEC a jihar Neja ta ce akwai

yiwuwar ba za a gudanar da zabukkan sanata a mazabun Neja ta Arewa da Neja ta Kudu ba a ranar Asabar saboda kuri'un zabe da aka tanadar domin mazabun sun bace. Bataren zabe na jihar, Farfesa Samuel Egwu ne ya bayyana hakan yayin da ya ke jawabi ga manema labarai a garin Minna.

Thursday, 14 February 2019

Malamai In da zasu tsine min sau 10000, sai Allah ya karamin daukaka – Kwankwaso

Tsohon gwamnan jihar Kano, Engr Rabi’u Musa Kwankwaso, yayi karin haske akan maganarshi da yayi akan malamai da yace yakamata su dena amfani da mambarinsu domin zagi ko kushe su.

A ziyarar da wasu malamai suka kai masa a ranar Alhamis, Kwankwason yace kowa yayi zagi a kasuwa yasan da wanda yake, yace su malaman da yake magana akansu suma sunsan dasu yake.

Kwankwaso yace “Irin wadannan malamai ko zasu tsine min sau dubu sai Allah ya kara daukaka ni. Daya daga cikin abinda ya kawo wannnan muhawara shine rashin fadar sunaye ne, in anyi maganar masu shiga iri kaza, na ware da sauran banda ban fada ba. Kowa yasan a garin nan idan mukayi zagi a kasuwa munsan da wadanda muke.” a cewar Kwankwaso

A kwanakin nan dai Sanatan yayi maganar da ta ja hankalin mutanen jihar Kano dama kasa baki daya akan shigar malamai siyasa suna sukarsu. Lamarin da yaja malamai da yawa yi masa raddi na cewa ya taba sunnar Annabi (S.A.W) Saidai wasu na ganin malaman suna sukar Kwankwason ne saboda bambantar ra’ayi, saboda wasu na cewa kar a zabi duka yan takarkarun da yake goyon baya.

Muna nan daram a kan niyyar mu ta bawa Buhari kuri’u miliyan 19 – ‘One 2 Tell 10

Shugaban kungiyar “One 2 To 10” mai yiwa shugaba Buhari yakin neman zabe reshen jihar Katsina, Dakta Mannir El-Yakubu, y ace babu gudu, babu ja-da-baya a kan kudirin kungiyar na samar wa da shugaba Buhari kuri’u miliyan 19 a zaben shugaban

kasa na ranar Asabar. Da yake Magana a wurin taron yakin neman zaben shugaba Buhari a jihar Katsina, El-Yakubu, y ace kungiyar su za ta tabbatar da cewar shugaba Buhari ya samu kuri’a miliyan daya daga kowacce jiha daga jihohi 19 da ke fadin arewacin Najeriya.

Ya kara da cewa dandazon jama’ar da su ka halarci taron kamfen din Buhari a jihar Katsina shaida ce da ke nuna cewar mutanen jihar na tare dan su tare da bayyana cewar shugaban kasa

Buhari na da daraja a duk in da ya shiga a duniya. Kazalika, ya bayyana cewar shugaban kungiyar sun a kasa, Dakta Baffa Bichi, bait aba nuna gajiya wa ba a rangadin da kungiyar ta yi na dukkan mazabun da ke jihohin arewa 19 domin nema wa Buhari jama’a.

An kama samfurin takardun zabe buhu 7 a Jigawa


Rahotanni daga jihar Kano dake a shiyyar Arewa maso yammacin Najeriya na nuni ne da cewa jami'an 'yan sanda sun kama wasu takardun kada kuri'a na gwaji da ke kama da ta gaskiya ta hukumar INEC da aka nufi yin amfani da su a jihar Jigawa.


Labarin batun dai yana cigaba da janyo takaddama tsakanin mabiyan jam'iyyun PDP da na APC kan abinda ake shirin yi da takardun tun bayan da ya fallasa a kafafen sadarwar zamani.

Hotunan kafin aure na Rahama Sadau da Sadiq Sani Sadiq sun tayar da kura


Fitattun jaruman finafinan Hausa wato Sadik Sani Sadik da Rahma Sadau da alamun bayyanar soyayya a tartare da su biyo bayan hotunansu dake nuna alamun akwai soyayya mai tsananin karfi a tsakaninsu


Jarumi Sadik Sani ya baiyana cewa soyayya tana da dadi koda a ce kana da mata za ka iya karawa. Da alamu akwai yiyuwar aure a tsakanin jaruman

yan sanda sun kama Buhuna 17 makare da kuri'u da aka dangwalewa APC a

An kama Buhuna 17 makare da kuri'u da aka dangwalewa APC a

Kano Jami'an 'yan sanda sun kama buhuna 17 cike da takardun zabe da aka dan gwale a jihar Kano, 

rahotanni sun bayyana cewa an tafi da buhunan ofishin 'yansandan jihar dan gudanar da cikakken bincike. Jaridar Daily Nigerian ta bayyana cewa wata majiya daga jami'an tsaron ta tabbatar mata cewa jam'iyyar APC ce aka dangwalewa kuri'un.

Buhari da Atiku sun bayyana jihohin da za su rufe taron su na yakin zabe a yau Alhamis

Mu-hadu-a-2023: Buhari ne zai lashe zaben 2019 da gagarumin rinjaye - Hon Abdulmumini Jibrin

Damajalisar tarayyar nan mai wakiltar mazabar kananan hukumomin Bebeji da Kiru daga Kano da yanzu haka yake a matsayin korarre daga majalisar Alhaji Abdulmumin Jibrin ya bayyana cewa yanzu kam ta tabbata shugaba Buhari zai lashe zaben 2019 da gagarumin rinjaye. 


Dan majalisar da ya bayyana hakan a shafin sa na sada zumuntar Tuwita ya Kuma bayyana nasarorin da shugaban Kasar ya samu tare kuma da jam'iyyar adawa marar karfi a matsayin wasu dalilan da za su sa shugaban ya sake Lashe zaben cikin ruwan sanyi

Yariman Saudiyya Mai Jiran Gado ya hau rufin dakin Ka'aba (karanta)


Yariman Saudiyya Mai Jiran Gado ya hau rufin dakin Ka'aba

Yariman Saudiyya Mai Jiran Gado Muhammad bin Salman ya hau doron dakin Ka'aba a lokacin da ya ziyarci garin Makka Mai Girma. Rahotanni sun ce, Yariman ya ziyarci garin na Makka domin duba sabbin aiyukan da ake gudanarwa a Dakin Allah Mai Tsarki. Yariman da ya halarci wanke Dakin Ka'aba da aka saba yi tare da jami'an tsaro 600 dake kare shi ya fara sumbatar Hajarul Aswad inda daga nan kuma ya hau matattakalar tare da shiga cikin dakin Ka'aba.

Yarima bin Salman ya yi Sallah a cikin Ka'aba inda ya dauki wani tsumma tare da yin goge- goge, sannan kuma sai ya hau saman rufin Dakin Mai Tsarki wanda abu ne da ba a saba gani ba. Hawan Yariman saman Dakin Ka'aba ya janyo ka ce na ce a shafukan sada zumunta na yanar gizo. An samu tarihin cewar daga cikin Halifofin Daular Abbasiyya Abu Ja'afar Al-Mansur ya taba hawa rufin Dakin. A yanzu dai ma'aikata na hawa saman Dakin don tsaftace shi a lokacin da aka yi ruwan sama ko kuma za a sauya rigarsa. TRThausa.

Shin ko Rahama Sadau da Sadiq Sani Sadiq zasu yi aurene? Kalli hotunan dake nuna hakan

Wadannan hotunan taurarin fina-finan Hausane, Rahama Sadau da abokin aikinta, Sadik Sani Sadik da ke nuna alamar soyayya a tsakaninsu, wasu daga cikin abokan aikinsu sun saka wadannan hotunan a shafukansu na sada

zumunta inda suke musu fatan samun rayuwar aure me kyau. A farkon makonnanne Sadik ya saki wani sako ta shafinshi na Twitter dake cewa so ne kesa mutum ya kara aure koda kuwa yana zaune da iyalinshi lafiya, sakon ya dauki hankulan mutane

sosai. Saidai duk da haka ba za'a cire tsammanin cewa wadannan hotunan na yin wani sabon fim ne ba da ake son fara salonshi da haka dan ya samu karbuwa gurin jama'a ba kamar yanda a kwanakin baya ya faru tsakanin Maryam Booth da Sadik Zazzabi. Koma dai menene lokaci be bariba.

zabe:: Kalli wani mutum da ya koma da kwana rumfar zabe dan ya zama na farko da zai sakawa Buhari kuri'a

 Ya Tare A Rumfar Zabe Tun Kwana Uku Kafin

Zabe Domin Ya Zama Mutum Na Farko Da Ya Jefawa Buhari Kuri'a Abubakar Shatima, wani masoyin Buhari kenan wanda ya yi hijira daga garinsa na Jos izuwa wurin Zaɓe , tun a jiya 13/02/2019. domin zama farkon wanda ya zaɓi Buhari. Rariya.

kaya tattun hotuna rahama sadau tareda sadik sani sadik





Hausanet.ml