Friday, 21 September 2018
![](https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEjVbPAo8q7oZWqnjT7HCdhph67FuOnz4HzuBz0fjpHGv66dNN9C-H0_XvUUvQRt75Y_L6QRsjO5zhhNz8TlLVLhL06Kt1dvRtvVWMKgJgyR9Xu-ENh18Efw_5FZ0xLKh4-dyWWVQhSIHcI/s640/FB_IMG_15375169620109157.jpg)
Abunda na sa gaba bayan daina fitowa a fim – Sadiya Gyale
Shahararriyar jarumar nan ta Kannywood wacce
aka dama da ita a lokutan baya, Sadiya
Muhammad Gyale ta yi tsokaci akan abunda ta
sa a gaba bayan barinta masana’antar ta shirya
fina-finai.
A cewar jarumar ta kama sana’a ne gadan-
gadan, inda ta ke saida kayayyaki daban-daban.
Sadiya tace tana saida kayan mata, na maza
dama kayan noma domin tafiyar da al’amuranta
na yau da kullun.
Dandalin Kannywood: Abunda na sa gaba bayan
daina fitowa a fim – Sadiya Gyale
Dandalin Kannywood: Abunda na sa gaba bayan
daina fitowa a fim – Sadiya Gyale
Jarumar ta bayyana hakan ne a wani hira da tayi
da jaridar Leadership Hausa.
KU KARANTA KUMA: Fadar shugaban kasa ta
kare Buhari akan amincewa da bayar da $1bn na
tsaro
Da aka tambayeta kan batun aure, kyakyawar
jarumar tace Insha Allah suna ta addu’a, Allah Ya
kawo miji nagari mafi alheri.
![](https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEgwd31p1HYgKdKLLBREDFpWXfcweGoeJlxteMtPHRU-ekWDclfvVxg3q7YA-U46pDCIH8h4Q_82UtV7b1w6x35copjPaBuqAKcuEQE9gUadF26-lgn_5RIXc2DQ1m_GAjYO06RqFkOhubs/s640/FB_IMG_15375157522791265.jpg)
Christiano Ronaldo Ya Fita Daga Filin Wasa Yana Kuka
Shahararen dan wasan
kwallon kafa na duniya Christiano Ronaldo ya
fice daga cikin filin wasa na Estadio Mestalla
yana zubda hawaye bayan da alkalin wasa ya
bashi jan kati a wasan Juventus da Valencia a
gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai na bana
wanda akayi a kasar Spain a lokacin wasan
rukuni na farko.
Alkalin wasan Felix Brych ya Sallami Ronaldo
ne, mintoci 29 da fara wasan a bayan da suka
game da Jeison Murillo mai tsaron bayan
Valencia har ta kai ga Cristiano ya kai masa
duka a yayin da suke gwagwarmayar daukar
kwallon.
Sai Murillo ya fadi kasa, hakan ya ja hankalin
alakalin wasa har inda ji ta bakin mataimakin
sa,
kafin ya koma filn wasai don nunawa
Ronaldo jan kati, ya fice daga wasan
Sai dai duk da rashin Cristiano a wasan
Juventus din ta doke Valencia daci 2-0
Sakamakon haka dan wasan ba zai buga wasan
da Juventus za ta yi Young Boys a ranar 2 ga
watan Oktoba ba a wasan rukunin na (H) na
biyu ke nan.
Sai dai kungiyar sa ta Juventus tace zata
daukaka kara a kan cewar bashi Jan Katin bai
dace ba.
Wednesday, 19 September 2018
![](https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEh1pGgrM48rGZ1cFY1BRpFMIPmP90KcEnH_fecr0kwgqzexs2xJdXpMbWtIXCIbABxCwVSEsvfcAROreL_TPYKgPV3TYilsYvpiUP2lsQQsA-9KY0TY5pDgqlNN8XFQrdwa-3UbjIj2YvY/s640/255BUNSET+255D.png)
Yadda zakuyi register Bashin 10,000 A layukan wayoyinku na federal government
Bayani Akan yadda zaku samu Bashin federal government na naira 10,000. Wannan dai bashine da federal government take basuwa ba dole bane saika biya Amma ga duk
wanda yabiya bashin 10,000 dinsa
zasu sake bashi damar samun wani bashin 40,000 har zuwa 1,000,000. Bugu da kari wannan bashin gaskiya ne domin duk wanda yayi register kafin sallar layya already yakarbi kudinsa. Domin samun naku saiku kubi wannan step din daya bayan daya.
![](https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEjzFzP07f8axxQWpUwly4zr5sR5-1bPaXAczavSRsLWdr-QSRlzeCK42uQOb010PW81hGZ8gCAIOxqANIR14esyIbP-FwOEaApGCJyE2-WXLs20rDYZ5JTPa84inRov8XruH4_pBMAN2BA/s640/FB_IMG_15372792698215823.jpg)
Lionel Messi ya dawo da karsashinsa na kwallo
Lionel Messi na Barcelona ya fara gasar
zakarun Turai a bana da cikakken karsashi, lura da kwallaye uku da ya zazzaga a wasan da suka lallasa PSV Eindhoven da ci 4-0 a
ranar Talata
Bayan jefa kwallon ta uku, abokan wasansa sun rufe shi saboda murna, yayin da magoya bayansa suka yi ta wake-waken kiran sunansa, in da kuma kocinsa, ya bayyana shi a matsayin
wani abu da ba a taba gani ba cikin tsawon
shekaru.
A karo na takwas kenan da Messi ke zura kwallaye uku-uku a wasannin zakarun Turai, in da ya zarce babban abokin hamayyarsa na Juventus Christiano Ronaldo , wanda ya zura
kwallaye uku-uku har sau bakwai a wasannin na
gasar zakarun Turai.
Ana iya tuna wayadda Messi ya gaza kai
tawagar kasarsa ta Argentina ga gaci a gasar cin kofin duniya a Rasha, yayin da Roma ta yi waje da su a gasar zakarun Turai a bara,
abin da bisa dukkan alamu ya bakanta ran gwarzon dan wasan, musamman idan aka yi la'akari da
jawabin da ya yi wa magoya bayansa a Camp
Nou.
Monday, 17 September 2018
![](https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEhWZ2rhR4xxvmZWubdRvvdzpQWtBP3pLeDNIvoUYlUsO2HGwODZPOq8ARPvJ1SWXRsL4hShDi97F8VvJ_gbfFJyKIKupCmabXIVj-nNClWZ3myN-rvzI3C4SwSdthjBo5QoPWcLAUzdJAU/s640/lionel-messi-barcelona-real-madrid_1a5beuyrhie1j1cp0fwynv2huu.jpg)
Dole Ne Real Madrid Ta Nemi Neymar, Cewar Messi
Kan wasan kungiyar kwallon kafa ta Barcelona,
Leonel Messi ya bayyana cewa abin bakin
cikine kan wasa Neymar yakoma Barcelona
ganin yadda kan wasan yabuga wasa a
kungiyar ta Barcelona kuma ya lashe kofuna da
dama tare dasu.
Neymar yakoma PSG daga Barcelona a watan
Agustan shekarar data gabata akan kuki fam
miliyan 200 wanda hakan yasa a yanzu kan
wasan yafi kowanne kan wasa tsada a duniya
kuma ya lashe kofin kasar Faransa.
Messi yace Neymar ya lashe manyan kofuna da
suka haka da gasar zakarun turai da gasar
Laliga da kuma ragowar kofuna saboda haka
har yanzu akwai Barcelona a zuciyarsa kuma
idan yakoma Real Madrid zai kara musu karfi.
“Tabbas nasar Real Madrid zasu nemi Neymar
sabida ya iya kwallo kuma duk wani abu da ake
bukata a wajen kan kwallo Neymar yanadashi
kuma irinsa Real Madrid take nema”
Messi yace yana bakin cikin ganin Real Madrid
ta kara karfi saboda bayason ganin su suna
lashe kofuna kuma idan har Neymar ya koma
kungiyar zasu cigaba da cin kofuna da kafa
tarihi kala-kala.
![](https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEgdh67YooQPVf8RzzmJsWpg3svZJbWiPwGB6IwVOsJHSdc0oYCC1crQHEMeuQs_6w5UulAk4cyq7ZEfJ57d5a_IBrBtqeTA0hYh-VCwsc6xRN2qf69Q7m1dBvRiN6LupLziRJ7PSSBa_dk/s640/14676545_1320795451272281_2574531765204942848_n.jpg)
Sarki Daya Ne Kacal A Kannywood Inji Adam Zango
Adam A Zango
ya bayyana cewa sarki kwaya daya tal ne
kawai a masana’antar Kanyywood da ke
shirya fina-finan Hausa.
Adam Zango ya bayyana hakan ne a
shafukansa na kafofin sadarwa na zamani,
inda ya nuna cewa har yanzu Ali Nuhu ne
sarki.
Daga baya kuma sai ya saka wani hoto, indayake zugunne a gaban Ali Nuhu, shi kuma Ali
yana zaune a kan kujera, sai ya rubuta cewa ‘tuba nake sarki’.
Wannan lamarin ya zo ne a daidai lokacin da wasu suke ganin akwai takun saka tsakanin
Adam Zango da Ali Nuhu, wanda har ake
tunanin yadda za a samar da zaman lafiya na dindindin a tsakaninsu.
![](https://lh3.googleusercontent.com/-GCwjUz5Wjpo/W5_VZlDCSbI/AAAAAAAAAbs/s640/_103455721_a857355c-ecc1-41d4-919c-0eacfce22064.jpg)
Kaciya ta sa an kwantar da mata 50 a asibiti
Wasu daga cikin matan ba su wuce shekaa hudu a duniya ba. An kama mata biyu 'yan kimanin shekara 60 da iyayen wasu matan da aka yi wa
kaciyar kan batun.
An haramta yi wa mata kaciya a Burkina Faso tun 1996, kuma wadanda aka samu laifin yin kaciyar ka iya shan daurin shekara uku a gudan
yari.
Ministar harkokin mata, Laurence Marshall Ilboudo, ta ce matan da aka yi wa kaciyar sun fi wadanda aka ba da labari yawa, sai dai ba a
gano wasun su ba
An yi wa matan kaciya ne tsakanin hudu zuwa shida ga watan Satumba a yankin Kaya, mai nisan kusan kilomita 100 daga babban birnin kasar, Ouagadougou, in ji ministar.
An kwantar da wasu daga cikin matan a asibitin lardi na Kaya Regional sannan aka kwantar da 38 daga cikin su a asibitin Chiphra Protestant da ke
Ouagadougou.
Wani likita mai suna Dr Dieudonne Ouedraogo ya ce wasu daga cikin matan sun samu manyan
raunuka.
![](https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEjpFV0FXpab_PFYEhkurXbUaWT0sfGNC24M5kKAn6A-SyqNbEYfH2r61blF4MtFG8NASnxVa5DwQm5LS4oFt6f3wlnq-CZsXgl4KklnVtAOEU-5oSX5gPRz_Lzc9eJXOCJ1ivZ5GfU1Xcs/s640/TELEMMGLPICT000134857582_trans_NvBQzQNjv4Bqek9vKm18v_rkIPH9w2GMNoGXySPv9M1Jbe0Fc3Bi1Fk.jpeg)
Mutum 1 Ya Rasu 40 Kuma Sun Jikkata Wajan Ruguguwar Shiga Kallon Kwallo
A kalla mutum daya aka
hallaka kuma kimanin 40 suka ji rauni a cikin
wata hayaniya wajan shiga kallon wasan
kwallon kafa a filin wasan dake Madagascar.
Wannan lamarin ya faru ne kafin a fara wasan
Madagascar da Senegal na neman tikitin shiga
kofin kasashen Afrika, 2019
Hakan ya faru ne sakamakon Dubban masu
sha'awar kallo suna kokarin shiga filin wasa ta
hanya daya tilo a ranar wasan wanda aka tashi
2-2
Biyu daga cikin wadanda ke fama da raunin
suna cikin mummunan yanayi a asibitin babban
birnin kasar Antananarivo. Mutane da yawa sun
yi ta hargitsi tun daga farkon safiya ranar
wasan don sanun shiga filin wasa a Stade
Municipal de Mahamasina.
Friday, 14 September 2018
![](https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEjXCwUkEl1YS0PUtn4c1Lqfy9w7zpJfDjq8qCR6G5xFTWzJ5Fxgv1ScQL1KT8cskH8nALPBUb389-w5XOn0-Mry_WzxKK4LK8-EcD1WVmL7P4cioK69XeLYf2ZEyd9udkaVv70i6_SLJIU/s640/Super-Eagles-1.jpg)
Hukumar NFF Ta Yiwa Golden Eaglets Alkawri Idan Suka Doke Ghana
Hukumar dake kula da
kwallon kafa ta tarayyar Najeriya NFF, ta
bukaci tawagar 'yan wasan Najeriya Golden
Eaglets, ta doke takwararta kasar Ghana a
wasan karshe na gasar cin kofin kasashen
Afrika ta CAF U17 2018 wadda akeyi a
Jamhuriyar Nijar inda tayi alkawarin karin kudi
ga 'yan wasan in har sun dauko kofin.
Kwamishinan fasaha na hukumar NFF Ahmed
Fresh Yusuf, ya ce kowanne dan wasan Eaglets
zai sami Kyautar dalar Amurka dubu $ 5,600
kwatancin Naira miliyan N2m) ko fiye da haka
idan har suka samu nasara a wasan ta ranar
asabar.
A ranar Laraba da ta gabata ne daddare 'yan
wasan Eaglets suka doke masu masaukin baki
kasar Niger da ci 2-1 a wasan kusa da na
karshe kuma an ba kowanne dan wasa kyautar
dala dubu $ 2,800.
Da yake jawabi akan wasan mataimakin mai
horas da kungiyar Nduka Ugbade wanda kuma
tsohon danwasan Najeriya ne a shekarun baya
ya ce tawagar ta 'yan kasa da shekara 17 za ta
yi kokari don tabbatar da cewa sun doke Ghana,
a wasan karshen.
"Abinda ke gabanmu yanzu shine mu fara gyara
wasu abubuwan da muka gani ba daidai ba a
cikin wasannin da mukayi baya. Ya kara da
cewar idan har 'yan wasan za su saurari bayani
da kuma aiwatar da umarnin da aka ba su, to
zamu doke Ghana a wasan karshe.
A ranar Asabar ne za'a buga wasan karshen da
karfe 7 na yamma, haka kuma a ranar ne za'a
fafata a wasan matsayi na uku a tsakanin masu
masaukin baki Nijar da Cote d'Ivoire da misalin
karfe 4pm, duk a filin wasa na Seyni Kountche
a Niamey jamhuriyar Nijar.
![](https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEj2mYMH0zjlL5_YFx9YistdT4EKY27nElEufsI7Eu8uVzNKh8N2rnTPG5RezHUmTBYa38zyvCfUcvZ0bxLkM03wL-pQJi8Z8jervalKy3jwqtuE-c8BrJtPgJaOqo3XMR6stiQ1fMEsYSU/s640/al-barnawi-boko-haram-696x456.png)
Mayakan Boko Haram sun kashe shugabansu
Majiyoyin da ke da cikakkiyar masaniya game da Boko Haram sun ce, wasu jiga-jigan
makusantansa ne suka kashe shi a ranar 21 ga
watan Agusta biyo bayan rashin gamsuwa da
salon jagorancinsa, musammam ganin yadda
yake da rauni idan aka kwatanta shi da
Abubakar Shekau.
A shekarar 2014 ne, Mamman Nur ya jagoranci
boren da mayakan suka yi wa shugabansu
Abubakar Shekau har aka samu tsagin
shugabancin Abu Mus’ab Al-Barnawy.
Koda dai wasu majiyoyin na cewa, Mamman Nur
ne hakikanin shugaban tsagin na Al-Barnawy,
kawai dai ya mika masa ragama ne saboda
darajar mahaifinsa, Mohammed Yusuf da aka
kashe a shekarar 2009.
sunan Al-Barnawy dai “Habib”, kuma mahaifinsa
ne ya assasa kungiyar ta Boko Haram.
Kwo yanzu, rundunar sojin Najeriya ba ta
tabbatar da mutuwar Nur ba wanda aka kashe
matarsa a wani samame da rundunar ta kai
maboyar kungiyar a yankin tafkin Chadi a cikin
watan Janairu.
Subscribe to:
Posts (Atom)