Majiyoyin da ke da cikakkiyar masaniya game da Boko Haram sun ce, wasu jiga-jigan
makusantansa ne suka kashe shi a ranar 21 ga
watan Agusta biyo bayan rashin gamsuwa da
salon jagorancinsa, musammam ganin yadda
yake da rauni idan aka kwatanta shi da
Abubakar Shekau.
A shekarar 2014 ne, Mamman Nur ya jagoranci
boren da mayakan suka yi wa shugabansu
Abubakar Shekau har aka samu tsagin
shugabancin Abu Mus’ab Al-Barnawy.
Koda dai wasu majiyoyin na cewa, Mamman Nur
ne hakikanin shugaban tsagin na Al-Barnawy,
kawai dai ya mika masa ragama ne saboda
darajar mahaifinsa, Mohammed Yusuf da aka
kashe a shekarar 2009.
sunan Al-Barnawy dai “Habib”, kuma mahaifinsa
ne ya assasa kungiyar ta Boko Haram.
Kwo yanzu, rundunar sojin Najeriya ba ta
tabbatar da mutuwar Nur ba wanda aka kashe
matarsa a wani samame da rundunar ta kai
maboyar kungiyar a yankin tafkin Chadi a cikin
watan Janairu.
No comments:
Write Please Share a Your Opinion.