. Hukumar NFF Ta Yiwa Golden Eaglets Alkawri Idan Suka Doke Ghana - hausanet hausanet





Friday, 14 September 2018

Home Hukumar NFF Ta Yiwa Golden Eaglets Alkawri Idan Suka Doke Ghana

Subscribe Our Channel




Hukumar dake kula da
kwallon kafa ta tarayyar Najeriya NFF, ta
bukaci tawagar 'yan wasan Najeriya Golden
Eaglets, ta doke takwararta kasar Ghana a
wasan karshe na gasar cin kofin kasashen
Afrika ta CAF U17 2018 wadda akeyi a
Jamhuriyar Nijar inda tayi alkawarin karin kudi
ga 'yan wasan in har sun dauko kofin.
Kwamishinan fasaha na hukumar NFF Ahmed
Fresh Yusuf, ya ce kowanne dan wasan Eaglets
zai sami Kyautar dalar Amurka dubu $ 5,600
kwatancin Naira miliyan N2m) ko fiye da haka
idan har suka samu nasara a wasan ta ranar
asabar.
A ranar Laraba da ta gabata ne daddare 'yan
wasan Eaglets suka doke masu masaukin baki
kasar Niger da ci 2-1 a wasan kusa da na
karshe kuma an ba kowanne dan wasa kyautar
dala dubu $ 2,800.

Da yake jawabi akan wasan mataimakin mai
horas da kungiyar Nduka Ugbade wanda kuma
tsohon danwasan Najeriya ne a shekarun baya
ya ce tawagar ta 'yan kasa da shekara 17 za ta
yi kokari don tabbatar da cewa sun doke Ghana,
a wasan karshen.
"Abinda ke gabanmu yanzu shine mu fara gyara
wasu abubuwan da muka gani ba daidai ba a
cikin wasannin da mukayi baya. Ya kara da
cewar idan har 'yan wasan za su saurari bayani
da kuma aiwatar da umarnin da aka ba su, to
zamu doke Ghana a wasan karshe.
A ranar Asabar ne za'a buga wasan karshen da
karfe 7 na yamma, haka kuma a ranar ne za'a
fafata a wasan matsayi na uku a tsakanin masu
masaukin baki Nijar da Cote d'Ivoire da misalin
karfe 4pm, duk a filin wasa na Seyni Kountche
a Niamey jamhuriyar Nijar.