. Mutum 1 Ya Rasu 40 Kuma Sun Jikkata Wajan Ruguguwar Shiga Kallon Kwallo - hausanet hausanet





Monday, 17 September 2018

Home Mutum 1 Ya Rasu 40 Kuma Sun Jikkata Wajan Ruguguwar Shiga Kallon Kwallo

Subscribe Our Channel




A kalla mutum daya aka
hallaka kuma kimanin 40 suka ji rauni a cikin
wata hayaniya wajan shiga kallon wasan
kwallon kafa a filin wasan dake Madagascar.
Wannan lamarin ya faru ne kafin a fara wasan
Madagascar da Senegal na neman tikitin shiga
kofin kasashen Afrika, 2019
Hakan ya faru ne sakamakon Dubban masu
sha'awar kallo suna kokarin shiga filin wasa ta
hanya daya tilo a ranar wasan wanda aka tashi
2-2
Biyu daga cikin wadanda ke fama da raunin
suna cikin mummunan yanayi a asibitin babban
birnin kasar Antananarivo. Mutane da yawa sun
yi ta hargitsi tun daga farkon safiya ranar
wasan don sanun shiga filin wasa a Stade
Municipal de Mahamasina.