Adam A. Zango ya koma Bayan
Atiku
Tauraron fina-finan Hausa, Adam A. Zango wanda a da yana gaba-gaba wajan goyon bayan shugaban kasa, Muhammadu Buhari a masana'antar fina-finan Hausa ta Kannywood yanzu dai ya canja sheka zuwa PDP har ma ya hadu da Atiku ya kuma bayyana goyon bayanshi a gareshi. Adam A. Zango ya bayyana cewa, bai taba Tsammanin haka Atikun ke da haba-haba da mutane ba sai da ya hadu dashi. Ya kuma ce ita kanta APC din tana nufin Atikune. Masoyan Adamun da dama sun bayyana ra'ayoyinsu a shafukan sada zumunta wanda ta kaiga sai da ya rufe bayar da damar bayyana ra'ayoyi akan al'amuran shafinshi watau Comment na Instagram. Ga abinda wasu suka bayyana akan hakan


No comments:
Write Please Share a Your Opinion.