. November 2018 - hausanet hausanet





Friday, 30 November 2018

Ko a cikin Aljanu Masoya Buhari sun fi yawa ---General bello muhammad bello



Tauraron fina-finan Hausa, Bello Muhammad Bello, General BMB na daya daga cikin jaruman dake goyon bayan shugaban kasa, Muhammadu
Buhari wanda har ya buga riguna da huluna na yakin neman zaben Buharin karkashin wata kungiya me suna VOBA daya bude yana

sayarwa Wani ya ce mai, zaben Buhari kam aikin addinine? Kaje ka zaba abun da kake so dan Allah haba! Mutum dai bai isa yace shi barai zaba Buhari bah sam Bello ya mayar mishi da amsar cewa, waya hana wani ra'ayinsa? Ba Atiku ba, idan kaga dama ka zabi aljani ma, ko a cikin aljannun masoya Buhari sun fi yawa

Sarauniyar kyau ta Rasha ta Musulunta

Sarauniyar kyau ta Rasha ta Musulunta, ta auri Sarkin Malaysia

Wata tsohuwar sarauniyar kyau ta Rasha ta zama sabuwar Sarauniyar Malaysiya bayan da ta musulunta ta kuma auri sarki kasar Muhammad
V na Kelantan Oksana Voevodina mai shekara 25 matashiya ce da mijin nata ya girme ta da shekara 24, wanda yake kan mulki tun shekarar 2016 An yi bikin Voevodina da sarkin ne a birnin Moscow a wani biki na kasaita ranar 22 ga watanNuwamba kamar yadda jaridar New York
Post ta ruwiato A wajen bikin dai ba sha barasa ba kuma ba a ci wani abinci da musulunci ya haramta ba. Kafin ta zama matar sarki amaryar ta ce: "A lokacin da nake makaranta ni mara ji ce. Ina son masu hatsabiban maza masu wasan zamiya da masu wasan keke da manyan baburan tsere wadanda suje shiga gasa Amma daga baya ta yi tsokaci cewa Ina ga namiji ne ya kamata ya zama shugaba a gidansa
kuma ya kamata samun sa ya fi na matar. Ba a san Voevodina sosai ba baya ga ficen da ta yi a zaben Saruaniyar kyau ta Rasha a shekarar
2015 Ba a bayyana yadda ma'auratan suka hadu ba sannan babu tabbas kan ko ta taba aure kafin wannan. Voevodina na da shekara 22 a lokacin da ta lashe gasar sarauniyar kyau ta Rasha.
Mahaifinta Andrey Gorbatenko babban likitan kashi ne a wani asibiti da ke kudancin Rasha Ta ce ta gano sirrin kyawunta ne a lokacin da take makaramtar gaba da sakandare. "Na fi kowa tsayi da siranta a ajinmu don haka sai na dinga damuwa. Amma shiga ta babbar makaranta ya sa na gane hakan abu ne mai kyau a gare ni." in ji ta. Voevodina dai ta zabi sunan Rihana a matsayin sabon sunanta na musulunci.


Tuesday, 27 November 2018

ZAFAFAN HOTUNAN NURA M INUWA TARE DA MATARSA DA YARSU FARRAH





Sababbin hotunan mawaki nura m inuwa tare da mai dakinsa wato matarsa da yarsa fahra Allah ya raya ya basu zaman lafiya amen

ZAFAFAN HOTUNAN NURA M INUWA TARE DA MATARSA DA YARSU FARRAH

Sunday, 25 November 2018

Soyayyar ----MARYAM YAHAYA da wani furodusa ta fito fili



Maryam yahaya tace Wata shakuwa da ake zargin tuni ta rikide takoma soyayya mai karfi ta shiga tsakanin daya daga cikin matasan jarumai mata a masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood dake tasowa, watau Maryam Yahaya
da wani mashiryin shirin fina-finai, Abubakar Bashir Maishadda. Masu bibiyar harkokin dake gudana a
masana'antar fina-finan ta Hausa dai musamman ma a bayan fage sun tabbatar mana da cewa a 'yan watannin nan wata alaka mai karfi da ake tunanin soyayyace ta shiga tsakanin mutanen biyu.

Kusan dukkan fina-finan da mashiryin fim din ke fitar wa akwai jarumar a ciki kuma ma takan taka muhimmiyar rawa a ciki. Haka zalika ma dai soyayyar tasu ta kara fito fili
karara ne a ranar 14 ga watan Satumba inda aka tsinkayi jarumar Maryam ta dora wasu hotuna a shafinta na dandalin zumuntar zamani na instagram ita da Furodusa Maishadda sanye da
zobuna iri daya wanda daga baya ta gogesu

Maryar Yahaya dai na daya daga cikin jarumai mata dake tashe yanzu a masana'antar Kannywood tun bayan wata muhimmiyar rawa da ta taka a cikin shirin fim din Mansoor.


Saurayina Baya Shirin Fim Kuma Ina Son Shi Matuka Hafsat Idris


A farfajiyar finafinan Hausa wato Kannywood mutane da yawa suna ganin ‘Yarwasa Hafsat Idris a matsayin sabuwar ‘yarwasa amma kuma ita jaruma ce domin tun da ta fito a wata fim mai suna Barauniya ta zama babbar Jaruma saboda hazakar da ta nuna a fim din

Gidan jarida ta yi hira da Hafsat Idris yayin da take daukar wata sabuwar fim mai suna Gimbiya Sailuba’ a garin Abuja. Da aka tambayeta akan daukakar da ta samu na faraddaya a harkar fim, Hafsat tace “Ikon Allah ne kawai da kuma himma da na sa akan sana’ar saboda ban taba irin wanan aikin ba amma tun da ta fara fitowa a fina- finan Hausa gaba na ke ta yi kuma ina wa Allah godiya da kuma kamfanin Maikwai Records da ta fara saka ni a fim. Ta kuma ce za ta so ta cigaba da aikin fina- finan Hausa duk da cewa aure ne ke gaban ta a yanzu haka

Kwarai da gaske ina da saurayin da na ke matukar so sai dai ba dan fim bane Bayan haka kuma Hafsat Idris ta bada bayani akan dangartakarta da Jarumai Nafeesa Abdullahi da Rahama Sadau da kuma a me zata fito a wasan ‘Gimbiya Sailuba Dangartakana da Rahama da Nafeesa ba ya wuce a wurin aiki

Idan aiki ya had mu zamuyi tare cikin fara’a da nishadi amma bayan haka babu wata alakar kawance da ke tsakani na da su. A cikin Fim din Gimbiya Sailuba kuma, Hafsat tace za ta fito ne a matsayin gimbiya san kowa kin wanda ya rasa.


Soyayyar ----MARYAM YAHAYA da wani furodusa ta fito fili

Maryam yahaya Wata shakuwa da ake zargin tuni ta rikide takoma soyayya mai karfi ta shiga tsakanin daya daga cikin matasan jarumai mata a masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood dake tasowa, watau Maryam Yahaya
da wani mashiryin shirin fina-finai, Abubakar Bashir Maishadda. Masu bibiyar harkokin dake gudana a
masana'antar fina-finan ta Hausa dai musamman ma a bayan fage sun tabbatar mana da cewa a 'yan watannin nan wata alaka mai karfi da ake tunanin soyayyace ta shiga tsakanin mutanen biyu.

Kusan dukkan fina-finan da mashiryin fim din ke fitar wa akwai jarumar a ciki kuma ma takan taka muhimmiyar rawa a ciki. Haka zalika ma dai soyayyar tasu ta kara fito fili
karara ne a ranar 14 ga watan Satumba inda aka tsinkayi jarumar Maryam ta dora wasu hotuna a shafinta na dandalin zumuntar zamani na instagram ita da Furodusa Maishadda sanye da
zobuna iri daya wanda daga baya ta gogesu

Maryar Yahaya dai na daya daga cikin jarumai mata dake tashe yanzu a masana'antar Kannywood tun bayan wata muhimmiyar rawa da ta taka a cikin shirin fim din Mansoor.

Zaka dade kana kallon hotunan nan na --- FATI WASHA baka kifta ido ba 


Zaka dade kana kallon hotunan
nan na Fati Washa baka kifta ido
ba saboda yanda ta yi kyau

Tauraruwar fina-finan Hausa, Fati Washa kenan a wadannan hotunan nata da ta haskaka, tasha kyau, tubarkallah

Thursday, 22 November 2018

Kalli wani iskanci da mai sana'a yake yiwa iyayen sa

MAI SANA OGA KAR KADAUKA

Kalli wasu kayatattun hotunan --- FATI WASHA

ZARAH NEW SONG AREWA24

Kalli Zafafan Hotunan ----AMINA AMAL

RAHAMA SADAU Ni Musulmace Kuma Nasan Iyakokin Addini Na RAHAMA SADAU




Idan baku manta ba abaya bayannan ne muka kawo muku wani labari inda fitacciyar jarumar film din hausa rahma sadau ta bayya na karara cewa korar da MOPPAN ta
mata alkairi ce agareta. jarumar tayi fira da mujallar guardian life inda jarumar tace ” Na san addini na

Nasan al’ada na Kuma nasan iyakokin da suka sa akai na. Kaga kamar bana jin dadin sa kananan kaya duk da yake bana ganin laifin bude gashi.” Jarumar tace itabata ganin laifin barin gashi a waje amma kuma tace tasan addinin ta kuma tasan dokokin daya dora mata. kome
zakuce game da wannan furucin


Tuesday, 20 November 2018

Labaran Safiyar Talata 20/11/2018CE - 12/03/1440AH. Cikakkun labaran


Labaran Safiyar Talata 20/11/2018CE - 12/03/1440AH. Cikakkun labaran

Jam'iyyar APC ta kafa kwamitocin sulhu domin hada kan 'ya'yan jam'iyyar gabanin babban zaben 2019.

Ofishin EFCC da ke Wuse 2 ya kama da wuta.

Shugaba Buhari ya bayyana cewar dakarun sojin Najeriya kadai ba za su iya kawo karshen kungiyar Boko Haram ba.

Jam'iyyu 38 sun marawa baya Atiku a matsayin dan takararsu na shugaban kasa.

Bangaren Atiku sun soki zuwan shugabannin tsaro wajen taron kamfen din Buhari.

EFCC ta gurfanar da Dan takarar gwamnan GPN a jihar Kano Idris Abdulkarim bisa zargin yin zamba.

Kotu ta haramta wa jaridar Daily Nigerian wallafa bidiyon Ganduje.

Kotu ta ki amince da bukatar Hukumar EFFC na mayar da Shari'ar Shekarau zuwa Abuja.

Shugaba Buhari ya bukaci 'yan Najeriya, musamman matasa, da su yi koyi da kyawawan halin Jonathan.

An kashe mutane, an kona gidaje da mota a wani biki a jihar Bauchi.

An dakatar da Akanta Janar na rikon kwarya a jihar Kebbi.

Mutane 12 sun mutu sakamakon ambaliyar ruwa a jihar Nha Trang ta kasar Vietnem wadda guguwar Toraji ta janyo.

Turkiyya ta fara kaddamar da hare-hara a yankin Afrin na Siriya.

A kasar Faransa an gudanar da zanga-zanga domin nuna adawar karin farashin man fetur.


IDAN KARASA MASOYI KAYI KUKA HAR HAWAYENKA SU KARE




IDAN KARASA MASOYI KAYI KUKA HAR HAWAYENKA SU KARE,masoyi shi yake kaunar masoyinsa, shiyake tausayinsa, shiyake kuladashi, shiya damu dadamuwarsa, shiyake samasa farinciki shiyake bashi kariya shiyake kare mutumcinsa shiyake martabashi shiyake xama abokin shawararsa shine me adana sirrinsa shine merufamasa asiri.masoyi ba lallai sai saurayi ko budurwa ba  iyaye suna ciki abokanai suna ciki makofta suna ciki yan.uwa suna ciki yannai ko kanne xaka iya daukar kowanne acikinsu  kayi kokari kagane masoyinka na gaskiya. Allah kahadamu da mai sonmu dagaskiya komai muninsa ko kyawonsa ameen. BY shafinmu www.hausanet.ml


Sunday, 18 November 2018

MATATA BATA DA NI'IMA, INA SHAN WAHALA DUK SANDA ZAN SADU DA ITA BAYAN BA BUDURWA BACE


MATATA BATA DA NI'IMA, INA SHAN WAHALA DUK SANDA ZAN SADU DA ITA BAYAN BA BUDURWA BACE

babbar magana ance da makasau bawa, domin dai duk matar dake da wannan matsakar lallai auranta yana cikin lilo domin ni'imar mace itace ke baiwa maigida nishadin kusantarta amma in dai jiki baki da ni'ima to kuwa idan ya dosoki da bukata ki tabbatar matsuwa ce, irin haka ne ke sanyawa kina ji kina
gani namiji ya dinga miki satar kwana, mai tsananin kaunar ki ne zai furta miki wanda yaga kuwa ba zai iya ba yayi ta kyara da hantararki karshe ma ki ga ya sake ki babu laifin tsaye babu na zaune.

YA KAMATA MA'AURATA INDA KUNA DA MATSALA SAI KU NEMA SHAWARA GA MASANA RASHIN NI'IMA

*_shike sanya mace duk sanda mijinta zai kusance ta sai ya sha wahala kafin mazakutarsa ta shiga farjinta ba wai matsuwa ba ce, a'a akwai masu irin wannan halittar ta matsuwar amman kuma ai da ni'ima ba a shan wahala duk sanda za'a kusance su, don haka yar'uwa da kin jiki kandas sai ki sani da akwai damuwa ga maigida.

Amman akwai wacce zaki ji tana cewa, ai ni idan ina tafiya ma ruwa har bi na
yake yi, to ki tambaye ta wane irin ne ruwan, don wasu fa ruwan karancin
wasu sindarai ne a jikinsu wanda fa ruwan karancin wasu sinadarai ne a jikinsu wanda bature ke kira da minerals kamar vitamin C , vitamin E , zine arginene, fotic acid, vitamin B1, 2 , 3 and B3 da dai sauransu ne, wasu kuma ruwa mai wari na ciwon sanyi gonorrhea- sai ace wai ni'ima akwai cikakken bayaninsu a shafin mata don haka ga macen dake da wannan matsalar ga abubuwan da zata dinga yi domin samun wadatuwar ni'ima a jikinta kamar haka.

                HADIN NI'IMA

aya
dabino
mazarkwaila
hakin daka madara ko nono mai kyau

YANDA AKE YI ZAKI

sami ayarki ki tsinceta tas sannan ki wanke ki shanya, idan ta bushe sai
ki zuba a turmi ki dakata lukwi, ki na dakawa kina tankadewa da rariya mai
laushi, sanya amarya kuka sai ki daka dabinonki da cukwi da mazar kwaila da
hakin daka lukwi ki hada da dakakkiyar ayarki guri guda, ki sami mazubi na
roba mai kyau mai murfi ki zuba, duk sanda zaki dinga sha sai kisa madara
peak ko kuma fresh milk danyen nono ko yoghurt me kyau, ba a bawa yaro
mai kiwa.

             HADIN NI'IMA 2

aya
Dabino
tafarnuwa
sugar da madara

YADDA AKEYI

zaki sami ayarki ki jika ta ta jiku sannan ki surfata, ki jika dabinon ki shi ma
ya jiku sosai sai a markada da dan blander ko kuma a markado a inji amman kice sai an gama nikan gero sannan za'a nika miki don kada a nika a kan kayan miya don kada yayi yaji, sai ki zuba garin tafarnuwa a kai sai ki hada
da madara ko nono idan da hali a saka a firji yayi sanyi ko kuma a sanya kankara a kai a sha ba a bawa yaro.

HADIN NI'IMA 3 

gwanda
kankana
abarba
_emon zaki
kankara
sugar

YANDA AKEYI

zaki sami gwandarki da kankanarki da abarba da ayaba ki yayyanka gwitsi
-gwitsi kamar kan kuda ' inji yara- sai ki bare bayan lemon zaki ki shima har
da wannan farar fatar ki cire kwallayen suma sauran ki ciccire kwallayen sai ki
hada su guri daya ki kara ruwan kadan kisa sukari kadan idan kina da firji kisa
a ciki idan kuma babu ki sak kankara akai ki ajiye shi narke sai ki tsiyaya
ruwan zaki ga ya zama mai kauri kitib ki dinga sha zaki iya hadawa da
yangudaddajin ma.

HADIN NI'IMA

dabino
madarar shanu
kanunfari gari
kirfa

YADDA AKEYI

za'a sami dabino a shanya shi ya bushe sai a cire kwallon a dakashi lukwi,
sannan a saka dakakkan garin janunfari a hada a kurfa guri daya sai a dinga
zuba cokali uku ana hadawa da madara shanu ana sha safe da yamma cokali
uku uku kullum tsahon sato guda.

           HADIN NI'IMA 5

garin idon zakara
garin tafarnuwa
ruwan khal
madarar shanu

YANDA AKEYI
a sami garin idon zakara da garin tafarnuwa hada rabin cokali a zuba a kofi a zuba ruwan khal karamin cokali a hada da madarar shanu cikin kofi a hada a sha, akwai saukar da ni'ima.

            HADIN NI'IMA 6

ruwan rake
Zuma
garin tafarnuwa
Garin kanunfari

YANDA AKE HADAWA

a sami rake a nikashi a blander ko kuma a saka cikin tirmi mai kyau a daka a
fitar da ruwan jiki, a zuba zuma mai kyau a kan ruwan raken a saka garin
tafarnuwa kadan a zuba garin kanunfari rabin cokali a hada a dinga sha akwai
saukar da ni'ima.

  RUWAN NI'IMA 7

Madarar shanu
ruwan khal
zuma
ruwan kankana

YANDA AKE HADAWA

a sami kankana a nikata ko a yankata gutsi-gutsi a zuba mata ruwa a barta ta
zagwanye a zuba a kofi a zuba ruwan khal da zuma a hada da madarar shanu a dinga sha shima yana da kyau.

HADIN TUKUDI NA GARI

garo
_kanunfari da citta da masoro_
hakin daka
sassaken kankana
dabino
mazarkwaila
sassaken baure

YANDA AKE YI

a sami gero a surfe shi a soya sam-sama sannan a dakashi ko kuma akai nika yayi laushi sai a zuba a tirmi a saka kanunfari garinsa da garin masoro da
garin sassaken kankana da garin dabino da dakakkiyar mazarkwaila da sassaken baure a hadasu a daka lukwi a shanya su a faranti ya bushe sai a dinga sha madara ko nono ko yogot.


MATATA BATA DA NI'IMA, INA SHAN WAHALA DUK SANDA ZAN SADU DA ITA BAYAN BA BUDURWA BACE

SHAWARA GA AMARYA GOBE A GIDAN MIJINTA 
               ☖ SIRRIN RIKE MIJI ☖

   AMARYA KI SANI; kamar yadda mutane suke Kai mamaci cikin kabari su tafi su barshi cikin kabarinsa haka iyaye suke Mai amarya su tafi su barta cikin dakin aurenta.
  Amarya ki natsu, gabanki ya daina faduwa saboda mijinki ba Mai cutarwa bane, farin ciki yazo miki dashi, Wanda yake maida budurwa ta koma uwa bayan lokacin kadan.

KADA KI FIRGITA DA YANA DA MATA KI ZAMA...
     ◦WAYAYYAR MACE GIDAN MIJINKI

wayayyun Mata kanana ko manya, kishi dasu yana da wahala. Idan mace ita ba wayya bace ko in ce idan bata dage ba, domin kwace Mata miji ba wuya zai yi ba, saboda wayayyar mace ba ta jij kunya ko girman kan yiwa mijinta duk Abu na farantawa saboda haka amarya ki zama wayayyar mace.
IDAN AKA SAMU WAYAYYAR YARINYA TUNI ZATA DANNE MANYA MATA A GURIN MIJI.
  haka ma babbar mace wayayya kishi da ita yana da wahala, Domin tana gyara jikinta tana kuma tattalin mijinta, abinda zai sawa abokiyar zamanta tunanin wai me wance takewa oga ne yake irin sannan rawar jikin ?
  Ko wata kasar zashi da ita yake tafiya, don Allah kema zama wayayya a gurin mijinki.

KALAMAN SOYAYYA NA MALLAKE MIJI CIKIN SAUKI.
                        
ANGONA, ZAMU JE KA KWANTA NA SHIRYA.
makwancina da Kai, babu abinda nake jira sai dai ka rike min hannayena mu tafi mu kwanta, kwanciya irin jaruman maza da matayensu..... I love you.....wane.

                        ②
ℳijina barka da shigowa, da fatan ka shigo lafiya.
        KE DA ℳIJINKI AMARYA

ki girmama shi.
ki bashi muhimmanci.
ki San damuwarsa da farin cikinsa.
ki sa shi dariya da nishadi.
ki yawaita maimaita masa Kalmar nan ta I LOVE YOU.
ki dinga yawan rumgume shi.
ki dinga kokarin kasancewa tare da shi matukar yana Gida.
ki dinga aika masa da kalaman sirrinku na ma'aurata ta hanyar sakon waya.ki tambaye shi gamsuwar sa bayan kun kamala saduwa.

                      DA ℳE ZAN GYARA

*MATATA BATA DA NI'IMA, INA SHAN WAHALA DUK SANDA ZAN SADU DA ITA BAYAN BA BUDURWA BACE*

babbar magana ance da makasau bawa, domin dai duk matar dake da wannan matsakar lallai auranta yana cikin lilo domin ni'imar mace itace ke baiwa maigida nishadin kusantarta amma in dai jiki baki da ni'ima to kuwa idan ya dosoki da bukata ki tabbatar matsuwa ce, irin haka ne ke sanyawa kina ji kina
gani namiji ya dinga miki satar kwana, mai tsananin kaunar ki ne zai furta miki wanda yaga kuwa ba zai iya ba yayi ta kyara da hantararki karshe ma ki ga ya sake ki babu laifin tsaye babu na zaune.


Thursday, 15 November 2018

Yadda Zaka Mayar Da Rancen Trader Moni Da Ka Karba




Yadda Zaka Mayar Da Rancen Trader Moni Da Ka Karba

Jama’a da dama suna tambaya akan shin ta yaya zasu mayar da kudin da suka ranta karkashin tsarin Trader Moni.

Yadda Rancen Trader Moni Yake
Da farko za’a baka N10,000 kai kuma zaka mayar da N10,250 cikin ko kafin watanni shida (6) ita kuma Gwamnati zata sake baka N15,000.
Bayan ka karb N15,000 zaka mayar da N15,375 cikin  ko kafin watanni shida (6) sai gwamnati ta sake baka N20,000.
Idan ka karbi N20,000 to zaka dawo da N21,000 cikin ko kafin watanni shida (6) gwamnati zata baka N50,000.
Idan ka karbi N50,000 zaka dawo da 52,500 cikin ko kafin watanni shida (6) gwamnati zata baka N100,000 ka mayar mata cikin watanni shida (6).

Tsarin Mayar Da Kudin Shine:
1. Wanda ya karbi N10,000 zai dinga biyan N430 a duk sati har tsawon watanni shida.
2. Wanda ya karbi N15,000 zai dinga biyan N640 a duk sati tsawon watanni shida,
3. Wanda ya karbi N20,000 zai dinga biyan N875 a duk sati tsawon watanni shida.
4. Wanda ya karbi N50,000 zai dinga biyan N2,187 a duk sati tsawon watanni shida.
Note: kana da damar mayar da kudin a yadda kake so ba sai a wannan tsarin ba, abinda ake bukata kawai ka mayar da kudin cikin lokaci.

Yadda Zaka Mayar Da Kudin Shine:
Zaka ziyarci daya daga cikin wadannan bankunan da zan jero a kasa sai kayi bayanin kazo biyan kudin Trade Moni, bankunan sune:
Eco Bank
Fidelity Bank
GT Bank
Heritage Bank
Ja’iz Bank
Stanbic Bank
Starling Bank
UBA Bank
Union Bank
Wema Bank

Ta Yaya Zaka Sake Neman Trader Moni Din?
Zaka sake nema kamar yadda ka nema a farko.

*540*265*12# xakaga ko saura nawa kagama biya  aman gaskia gwamnatice take biya



Friday, 9 November 2018

SAKONNIN SOYAYYA GUDA 10

SAKONNIN SOYAYYA GUDA 10+

NA ‘DAYA.
Ke kamar hasken wata ki ke mai hasken da ke haske idaniya, haka kuma kalamanki tamkar siga suke ma’abocin za’ki, tabbas kin yi kama da kanki hakan ya sanya na ji ina son ki.

NA BIYU.
A lokacin da kika ji kina son wani, to yi maza ki adana sunan shi a cikin d’aya daga cikin kogunan da ke a cikin zuciyarki, domin kuwa ita zuciya takan iya raunata a koda wane lokaci amma shi kogon zuciya ya kan kasance tare da ajiyar da aka yi a cikin shi har abada. Ina fatan zan kasance ni ne wanda za ki adana a ma6oya mafi sirrinta soyayya da masoyi? Ina son ki.

NA UKU.
Sauda yawan lokaci idanuwana sukan yi kishi da zuciyata!!! Kin kuwa san mene ne dalili? Saboda a koda yaushe kece abu mafi kusanci da zuciyartawa su kuma idanuwa kin kasance mai yin nesa da su. Ina son ki sosai da zuciya d’aya.

NA HU’DU.
Na kasance ma’abocin soyayya zuciyatama ta gaskata hakan, lokaci na shud’ewa soyayyar ki na k’aruwa a cikin zuciyata, a lokacin da ki ke cikin farin ciki kyakkyawar fuskar ki na bayyanar da murmushi mai taushi da tausasa zuciyar ma’abocin kallonta, kece wadda na ke so a cikin zuciyata babu wata da zata iya canja matsayin ki a wajena. Ina k’aunar ki.

NA BIYAR.
SO tamkar rayuwane, ba ko yaushe yake zamowa abu mai sauki ba haka kuma ba a koda yaushe yake wanzar da farin ciki ba, to amma mene ne zai sa matsawar muna raye da rai da lafiya za mu yanke alakar soyayya a tsakanin mu? Har zuwa yau babu kamar ki a cikin zuciyata domin kuwa jin muryar ki a kullum na rubanya adadin soyayyar da na ke yi miki a cikin ko wane dare ko safiya. karda ki rabu da ni dan Allah, domin hakan zai iya sanyawa na zamo mutum mai rauni a rayuwata.

NA SHIDA.
SO tamkar kurbar ruwan shayi yake mai tsananin zafi, a karon farko zaka kasance cikin shaukin begen shi wanda daga bisani kuma zai k’ona maka harshe na tsawan lokacin da zaka shafe kana yin jinyar shi.

NA BAKWAI.
Soyayyar da na ke yi miki tamkar tafiyace mai nisa da na fara yinta wadda bata da lokacin yankewa har abada. Na san burina zai cika matsawar ina tare da ke domin kuwa dukkanin burina yanzu bai wuce na samun ki a matsayin matata uwar ‘ya’yana ba. Ina son ki fiye da gwal ko kud’i.

NA TAKWAS.
Karda ki fadawa kowa kalaman sirrin bude soyayya da kawancen dake tsakanin mu, domin kuwa a dukkan lokacin da kika furta wadannan kalaman sirri ga wani wato “INA SON KA” hakan na nuni da cewa zai yi amfani da shi wajen bude mana akwatin soyayyar mu ta sirri wanda hakan zai bashi damar yi mana gagarumar sata har ya yi sanadiyar raba ni da ke har abada. Ina son ki.

NA TARA.
Na yi shiri tare da niyar turo miki da dikkanin soyayyata amma sai dai wanda zan turo da sakon nawa gare ki ta hannun shi ya bayyana hakan a matsayin wani babban abu da zai gagari bil’adama d’auka, amma karda ki damu zan zo nan bada dadewaba domin ki tabbatar da abun da na ke fad’a gaskiyane dama an ce zuwa da kai ya fi sak’o. Ki huta lafiya farin cikin zuciyata. Ina son ki.

NA GOMA.
Abba ne zaune a kan wata farar kujerar roba cikin wani lambu mai d’auke da korayen ciyayi da ni’ima mai dad’i, wajen da ya zamo masa wajen hutawar shi a dukkan lokacin da ya fita wajen aiki bayan ya yi aikin ya gaji nanne inda ya saba zuwa ya kirawo matar shi a waya domin jin halin da ta ke ciki tun bayan auren su wanda hakan ba karamin burge matar tashi yake yi ba sannan kuma yana k’ara soyayyar shi a cikin zuciyarta.

Yauma dai kamar kullum, ya fito da wayar ta shi daga aljihu ya shiga kiranta, kamar jira ta ke yi dama bugu d’aya ta d’aga, bayan sallama sai kuwa ya shiga cewa da ita

“Matata Uwar ‘ya’yana maganin kukana, Salimat a baya kafin mu yi aure na yi tinanin cewa bayan mun yi aure ba zan ke samun kulawa da tarairaya tare da kalaman soyayyar nan ta ki masu dad’i ba, na yi zaton komai zai canja kamar yadda na ke gani a wasu gidajen auren ashe mu ba haka abun ya ke ba saima abun da ya ci gaba ya kuma sauya sabon salo mai dad’i, Salimat ina son ki, koda aiki nake yi yadda zan dawo gida na tarar da ke kawai na ke yin tinani, kuma koda abinci zan ci ina ci ne ka