Labaran Safiyar Talata 20/11/2018CE - 12/03/1440AH. Cikakkun labaran
Jam'iyyar APC ta kafa kwamitocin sulhu domin hada kan 'ya'yan jam'iyyar gabanin babban zaben 2019.
Ofishin EFCC da ke Wuse 2 ya kama da wuta.
Shugaba Buhari ya bayyana cewar dakarun sojin Najeriya kadai ba za su iya kawo karshen kungiyar Boko Haram ba.
Jam'iyyu 38 sun marawa baya Atiku a matsayin dan takararsu na shugaban kasa.
Bangaren Atiku sun soki zuwan shugabannin tsaro wajen taron kamfen din Buhari.
EFCC ta gurfanar da Dan takarar gwamnan GPN a jihar Kano Idris Abdulkarim bisa zargin yin zamba.
Kotu ta haramta wa jaridar Daily Nigerian wallafa bidiyon Ganduje.
Kotu ta ki amince da bukatar Hukumar EFFC na mayar da Shari'ar Shekarau zuwa Abuja.
Shugaba Buhari ya bukaci 'yan Najeriya, musamman matasa, da su yi koyi da kyawawan halin Jonathan.
An kashe mutane, an kona gidaje da mota a wani biki a jihar Bauchi.
An dakatar da Akanta Janar na rikon kwarya a jihar Kebbi.
Mutane 12 sun mutu sakamakon ambaliyar ruwa a jihar Nha Trang ta kasar Vietnem wadda guguwar Toraji ta janyo.
Turkiyya ta fara kaddamar da hare-hara a yankin Afrin na Siriya.
A kasar Faransa an gudanar da zanga-zanga domin nuna adawar karin farashin man fetur.
No comments:
Write Please Share a Your Opinion.