. Zai yi wahala a samu wanda zai maye gurbin Ronaldo - Juventus - hausanet hausanet





Tuesday, 9 October 2018

Home Zai yi wahala a samu wanda zai maye gurbin Ronaldo - Juventus

Subscribe Our Channel




Darakatan wasanni a Juventus Fabio Paratici,
yace zai yi wahala a iya samun wanda zai iya
maye gurbin zakakurin dan wasa kamar
Cristiano Ronaldo.



Paratici ya bayyana haka ne jim kadan bayan
karbar kyautar girmamawa ta mafi kwazon
daraktan wasanni a tsakanin takwarorinsa da ke
kungiyoyon gasar Seria A, a kasar Italiya.
Yayin da yake zantawa da manema labarai
dangane tasirin sauyin shekar Ronaldo zuwa



Juventus daga Real Madrid, Paratici, yace
kungiyar za ta cigaba da marawa Ronaldo baya
domin kare mutuncinsa, dangane da zargin
aikata fyade da wata mata ke yi masa.
Darakatan wasannin na Juventus, ya kuma



musanta rahotannin dake cewa, kungiyar na
shirin maido da tsohon dan wasanta Paul
Pogba, wanda a yanzu yake bugawa
Manchester United wasa, bayan sauyin sheka
zuwa kungiyar daga Juventus a shekarar
2016, kan kudi fam miliyan 89.