Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, Sanatocin sun gana ne a birnin Abuja don tattaunawa kan yadda za su tsige Saraki daga mukaminsa na
shugaban majalisa bayan sauya shekarsa daga
APC zuwa babbar jam'iyyar PDP mai adawa.
Ko da yake wasu rahotannin na cewa, Sanatocin
sun tafka zazzafar muhawara kan batun
tsigewar, in da wasu ke cewa, jam’iyyar ta APC
ba ta yi musu adalci kan wasu batutuwa.
Da ma tun bayan ficewar Saraki daga APC zuwa
PDP, Sanatocin APC suka lashi takobin tsige shi
da mukaminsa, in da suke cewa, dole ne
jam’iyya mai mulki ta rike kujerar shugaban
majalisa saboda rinjayenta a majalisar.
Wannan na zuwa ne a yayin da Majalisar
Tarayyar Kasar ke komawa bakin aiki a ranar
Talata bayan shafe fiye da watanni biyu na
hutu.
No comments:
Write Please Share a Your Opinion.